chapter 18

38 5 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
  *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_Jiddah S Mapi_

*Chapter 18*

              ~kallon bayanta tayi bataga kowa ba, abinda yake bata tsoro kenen, yana ganin duk wani motsi nata amma ita bata ganinshi, tana fita ta shiga mota da sauri ta dafe kirji, jakanta ta buɗe ta ciro goran ruwa tasha kana ta kalli driver wanda yake bacci tace "sani!!! sani!!!"
a firgice ya tashi yana laluman kofa, cikin gigin bacci yace "ban faɗa ba"
da mamaki tace "meka faɗa?"
murza ido yayi ganin noor ce zaune yace "hajiya kin fito?"
wani uwar harara ta watsa mishi, ganin zai tada mota tace "dakata"
buɗewa tayi ta fita, ta buɗe mishi tace "fita ka koma baya, ba zan tsaya ka kasheni a banza ba, idan munje gida na sauka kaja kanka damuwanka ne"
fita yayi ya koma baya, tasa tissue ta goge mazaunin driver kana ta zauna ta kulle motan, driven ta fara tana tuna abinda ya faru yanzu, haka kawai saiya kirata ita bata ganinshi shi kuma ya gama kare mata kallo?
kallon agogo tayi taga karfe 1 saura, tsaki taja ta hango wani me gashin nama, tsayawa tayi ta siya dayawa domin yunwa takeji, dawowa tayi taci gaba da tuƙi har ta isa gida, ɗaukan jakanta da ledan tayi kana ta wurga mishi tissue tace "dawo ka koma gida koda wasa naji wannan zancen a bakin wani daga ranan you are no longer driver"
giɗa kai yayi duk da baisan me tace ba amma yaji driver a ciki yasan aikinshi take nufi.

juyawa tayi ta shiga gida shi kuma ya tada motan ya tafi, koda ta buɗe kofan taji a buɗe shiga kawai tayi ba tareda ta rufe ba, inna da take ɗaki tana jiran shigowanta taji karan kofa, fitowa tayi ta wuce ta gefenta taje ta rufe kofan da bolt, dan batason anwar ya yanke baccin da yakeyi, ɗaki ta shiga ta ganshi kwance a kasa ya ɗaura kanshi a pillow sannan ya rungume ɗayan pillow yana bacci, tsallakashi tayi ta wuce kan gado,ajiye ledan tayi ta cire mayafin dake kanta, buɗe ledan tayi ta fara cin naman, saida ta koshi nak kafin tasha ruwa, tashi tayi ta kai sauran frij, kayan jikinta ta cire ta shiga toilet tayi wanka saboda ta gaji, da towel ta fito tana kallonshi yana cigaba da bacci, rigan bacci mara nauyi tasa riga da wando kana ta fesa turare ta shafa night cream nata kana ta haye gadon ta kwanta, kanta ta ɗaura akan Pillow tana tuna wannan mutumin data kasa tuna fuskanshi, hasalima bata kalleshi ba a lokacin da yazo wajenta balle ta gane kamanninshi,  "kashe wutan"
taji yayi magana da sauri ta leka tana kallonshi a zuciyanta ta fara magana "dama ba bacci yake ba?"
kin kashe wutan tayi, ya kuma cewa "kashe wutan nace"
bata kashe ba saima gyara kwanciya da tayi, tashi yayi jallabiya ne a jikinshi me taushi pitch color, takawa ya fara cikin nutsuwa da rashin son hayaniya, hawa gadon yayi da sauri ta mike tana rufe jikinta da duvet, matsowa ya fara ta fara yin baya saida ta kai karshen gadon kana ta fara zare ido tana kallonshi, matsowa yayi dab ita kamar jikinsu zai taɓa juna yasa hannu akan switch ɗin ya kashe wutan, sauka yayi daga gadon da sauri ta sauke ajiyan zuciya, komawa yayi ya kwanta a inda ya tashi, rungume pillown yayi yana tuna haneefa da itace suke tare da yanzu yana cikin farin ciki mara misaltuwa sai gashi Allah ya ɗauke ta, wasu zafafan hawaye ne suka fara bin kyakkyawan kumatunshi, ta zaci zai taɓa ta kamar yadda taje wani katon ya gama latsa ta a hotel ne har take ja da baya?
raɗaɗi yakeji a cikin zuciyarshi, noor itama kwanciya tayi, shiru tayi a cikin bargon bacci ya kasa ɗaukanta, tunanin haneefa ne ya cika mata zuciya data sani da bari tayi kawai ta auri wannan anwar ɗin, gashi yanzu itace a gidanshi matsayin mata, har tsoron rufe ido take tayi bacci haneefa kawai take gani, wasu zafafan hawaye suna wanke mata fuska da haka har tayi bacci.

washe gari ta shirya cikin uniform na school tayi kyau sosai, jakanta na teddy ta goya a baya kana ta ɗau ruwan sanyi ta rike a hannunta, takalmin kafanta snicker ne, kallon abincin kofan ɗakinta tayi, tsaki taja "wannan matan ba zata daina kawo min abinci ba ko? me zanyi da wannan kazamin girkin?"
kallon plate ɗin tayi ta kuma jan tsaki, zata wuce wayarta ta faɗi akan plate ɗin, durkusawa tayi kasa ta ɗaga tana kallo, hamdala tayi be fashe ba sai ɗan tsagewa da yayi kaɗan, buɗewa tayi taga shinkafa ne da wake da manja, ga kuma yaji a gefe, haɗiye miyau tayi ganin yaji a gefe, ji tayi kamar taci, janyo plate ɗin tayi ta ɗibi yaji dayawa ta zuba a gabanta ta fara ci, ji tayi ya mata daɗi batasan lokacin da taci dayawa ba, saida ta cinye tas kafin ta kalli plate ɗin, tashi tayi zata tafi taji muryanshi a bayanta yana cewa "abincin kazaman kikaci?"
huci ta fara ta rasa amsan da zata bashi, yana gyara ɗaurin agogon hannunshi ya kara maimaita mata "abincin kazama kikaci?"
inna da take bayi ta fito da sauri ta nunashi da yatsa "kai anwar yaushe ka koyi banzan hali? nan ba gidansu bane? dan taci abinci kake wannan maganan ba matarka bace? kuma ai ƴata ce"
shiru yayi inna ta gama mishi faɗa, noor dake tsaye taji daɗin faɗan da tayi mishi, juyowa tayi ta yiwa inna murmushi tace "na gode"
"ba komai ƴata"
fita tayi bayan ta aika mishi wani mugun harara, saida inna taga kanta ya ɓace kafin tace "ba haka ake gyara mutum ba, janyota jiki zakayi ba wai bakar magana ba"
fita yayi ranshi ya ɓaci da faɗan inna, hawa mashin nashi yayi fuuu yabar layin, wuceta yayi jakanta a goye a bayanta tasa hannu ta rike igiyan ta gaba tana tafiya kamar wata karamar yarinya, ji yayi kaman ya bigeta ko zai huta da bakin cikin da yakeji idan ya ganta.

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now