chapter 9

40 4 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
    *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_jiddah S Mapi_

*Chapter 9*

              ~Anwar yana farin ciki ya isa gida, raken daya dawo dashi ya rabarwa yara domin baisan inda zai zauna ya cigaba da siyarwa ba, inna tana ganinshi ya shigo da kus-kus ya aje, fuskanshi da alaman damuwa ga kuma farin ciki a gefe ɗaya, kallonta yayi yazo ya zauna a gabanta ya karɓi abin gyaran farcen da take aiki dashi, ya kamo yatsanta ya fara yanke mata farcen, kallonshi tayi taga yana murmushi, sai itama taji daɗi har cikin ranta, tace "meyake saka murmushi?"
"inna insha Allah zan samu kuɗin aikin Abban jameel"
"aina zaka samu?"
"gidan wani mutum ne zanje nayi bayin flower na rinƙa kula da shuƙe-shuƙen gidan"
jikinta yayi sanyi ta kalleshi na tsawon sakonni kana tace "kana ganin zaka iya aiki a karkashin wani?"
"inna ni waye da bazan iya ba? ai ko bazan iya ba zan koya saboda munada buƙatan kuɗin"
"to nidai addu'ata Allah ya tsareka a duk inda kake"
"Ameen inna"
bayan ya gama yanke mata farcen ya haɗa mata ruwan wanka ta shiga banɗaki shikuma ya shiga ɗakinshi, murna da farin ciki yakeji koba komai zai daina ganin jameel nashi yana kuka.

washe gari da asuba Jameel yayi musu sallama a firgice, anwar da yake rike da brush ya ɗago yana kallonshi cikin firgici, tsoronshi kada ace abba ya mutu, da sauri ya saki brush ɗin yaje wajen jameel yace "meya faru?"
jameel yace "Abba zai mutu"
baisan lokacin daya suri jallabiya ya ɗaura akan gajeren wandon dake jikinshi ba, a tare suka fita anwar ya tada mashin, yana jin inna tana cewa su tsaya zata bisu baibi ta kanta ba, direct gidansu sukaje anwar yana shiga yace "kira taxi"
wacce take tsaye da alama kanwar jameel ce ta fita da gudu ta kira taxi, ɗaga Abba sukayi suka sashi a motan, nan suka shiga tafi da umma da anwar da jameel, city hospital suka nufa emergency aka karɓesu, bayan sun shigar sashi ɗakin anwar da jameel sun gagara zama sai safa da marwa suke, kusan 1hour doctor ya fito ya musu alama dasu sameshi, har rige-rige suke wajen bin bayan doctor, bayan sun shiga ya basu wuri suka zauna yace "wannan yana cikin tsananin ciwo, ruwa ne ya taru a kirjinshi dole sai munyi aiki.kamar yadda muka gaya muku a baya, kuma kuɗin  aiki miliyan uku ne, kamar yadda kuka sani, ba zamu taɓa shi ba sai kun kawo rabin kuɗin wato miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar"
kwafa jameel yayi kanshi ya dafe yana jin maganan kamar saukan aradu, anwar yace "ba komai ku fara aikin zamu kokarta"
jameel ya ɗago jajayen idanunshi yace "zamu kokarta ta yaya? aina zamu samu miliyan uku? kawai mu ɗauke shi mu koma gida na cire rai da rayuwarshi, muje kawai"
hannunshi anwar ya riko suka fita waje, yana sharan hawaye yace "ka samu umma ka kwantar mata da hankali zan nemo"
hannunshi ya rike "kada kasa kanka a wani hali saboda rashin lafiyan mahaifina"
cire hannunshi yayi kana yace "saina dawo"
tafiya yayi ya hau mashin nashi, unguwan da Abba ya mishi kwantance can yaje, tun a hanya ya fara ganin rantsatsun gidajen da suke layin, a bakin wani kofa yayi musu sallama kana yayi tambaya suka nuna mishi har gidan Abba, godiya yayi ya wuce har bakin maƙeƙen get ɗin ya tsaya yana karewa gidan kallo, sai a time ɗin ya tuna bai ɗauko takaddan da Abba ya bashi ba saboda ruɗewa, gashi ya koma gida sunyi nisa, gwada sa'a yayi yaje wajen masu gadi wanda suke tsaye sun tsare kofan suna kallon duk masu shige da fice na layin, gaishesu yayi suka amsa cikin ɗaure fuska, a hankali yace "Alhaji yana nan?"
"wake nemanshi?"
kallon wanda yayi tambayan yayi babu alaman wasa a tare dashi, yace "shi yace nazo"
"ina shaida?"
"na manta a gida"
da hannu suka mishi alama da ya koma, kin tafiya yayi yana rokansu su barshi ya shiga, suna cikin jayayya faruk yayi hon, buɗe mishi kofan akayi ya fito da motanshi, har zai wuce sai kuma ya tsaya ya sauke glass yana kallon anwar wanda yayi jugum ya tsaya ya rasa abinyi, buɗe motan yayi ya fito, hannu ya mika mishi suka gaisa yace "wa kake nema?"
bayani ya mishi faruk yace "kaine bakon Abba?"
kai ya jijjiga yace "eh"
"to bismilla mu shiga daga ciki dama Abba jiranka yake tin da safe sai kuma baka zoba"
murmushi kawai yayi baice komai ba har suka shiga cikin babban gidan da yake kama da aljannan duniya, bin ko ina yake da kallo har suka isa bakin babban falo, kallonshi yayi yace "bari nayi mishi magana first"
jijjiga kai yayi, faruk ya shiga ciki, Abba yana ɗakinsu noor yana duba jikin haneefa wacce ake shirin ɗaura mata ruwa, sallama yayi kana yace "abba bakonka is here"
kallonshi abba yayi "Are you sure?"
giɗa kai yayi, Abba yayi murmushi yace "okay bari a gama ɗaurawa haneefa ruwan sai inje bismilla shigo dashi main palour"
"okay Abba"
fita yayi noor tana zaune a gefe tayi tagumi, da wasa da wasa haneefa tana nema ta ɗaurawa kanta ciwo akan wannan me raken, saida aka ɗaura mata ruwa kana Abba ya fito, time ɗin Faruk ya shigo da anwar yana zaune a gefenshi suna hira, shi anwar baya magana sai eh da a,a kawai yake faɗa, hankalinshi akan Abban jameel da yake cikin wani hali a hospital, Abba ne ya fito yana murmushi yana kallon anwar, zama yayi akan kujera anwar ya sauka kasa ya zauna yana gaida Abba, amsawa yayi cikin sakin fuska yace "sannu anwar har na cire rai da zuwanka"
hannu yasa ya sosa kai yace "a gafarceni Alhaji"
Abba ya giɗa kai kana yace "ba komai"
noor ce ta fito tana kallon takaddan da aka rubuta maganin haneefa akai, wando jins blue ne a jikinta da top fari, kayan ya kamata sosai, Abba ya ɗaga kai yace "noory? kawowa bakonmu ruwa da lemo"
ba tareda ta sauko ba ta juya ta koma tareda cewa "toh Abba"
ɗabi'an Abba ne idan yana falo babu me aikin da suke shigowa, taje kitchen ta ɗau plate kana ta dawo ta ɗaura ruwa da lemo ta koma ɗaki, haneefa ta samu bacci, after dress baƙi ta ɗaura a saman kayanta ta fito, ɗaukan plate ɗin tayi ta sauko kasa, time ɗin Abba ya ɗau cheque yana yiwa Anwar sign, a hankali take takawa har ta isa gabansu, Abba ya ɗago yace "yawwa noor"
jin sunan da Abba ya kira yasa anwar ɗago kai dan yaji sunan a bakin haneefa, ido huɗu sukayi, plate na hannunta ne ya faɗi kasa, ji kake tass ya fashe harda karamin glass cup da yake kai, baya tayi tana kallonshi a tsorace, meya kawoshi gidanmu?
Abba ya tsaya da sign ɗin ya kalleta yace "me haka?"
durkusawa kasa tayi tana tsince glass ɗin daya fashe, "tuntuɓe nayi Abba"
"sannu"
ya kasa ɗauke idonshi akanta, nan gidansu ne kenan? zufa yaji ya fara ƙeto mishi, ta yaya zai iya aiki a gidansu?
kallon Abba yayi wanda yake miƙa mishi cheque, Ido ya zubawa cheque ɗin yanada buƙata amma ba zai iya zama anan gidan tareda wannan yarinyar ba, Abba yace "karɓa mana anwar"
a hankali yasa hannu ya karɓa, noor kuma ta juya ta koma cikin ɗakinsu, ruwan da bata kawo ba kenan, hannu tasa ta dafe goshinta wanda zufa ya fara ketowa, a fili tace "ya biyota har gida kenan?"
kanta ta ɗan buga da hannunta "me ya gayawa Abba? karfa zancen auren haneefa yayi mishi"
kwafa tayi kana tace "da ko sai inda karfina ya kare wajen raba auren nasu"
kasa tsayuwa tayi saida ta zaune a gefen haneefa wacce take ɗaure da drip a hannu tana bacci, hannu tasa ta shafa kanta sannan a hankali tace "ba zan bari rayuwarki ta lalace ba"

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now