chapter 10

42 3 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
    *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_jiddah S Mapi_

*Chapter 10*

              ~Tana gama mishi rashin mutuncin ta juya ta tafi, momy dasu Abba harda su haneefa da yah faruk suna falo da alama shawara suke, taji momy tace "shirya muje Shoprite"
kallon haneefa tayi wacce take murmushi tace "bana jin daɗi momy kuje kawai"
"to Allah ya baki lafiya jeki kwanta ki huta ko?"
giɗa kai tayi, ɗaki taje ta faɗa gado tana jin kanta yana ciwo, kamar da wasa tayi karya da rashin lafiya gashi yanzu tana jin kanta yana ciwo da gaske, haneefa ce ta turo kofa ta shigo, kallonta tayi "sannu sis"
giɗa kai kawai tayi, haneefa ta shiga toilet tayi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin leshi blue black ɗinkin riga da skirt, ta yafa mayafi fari da farin takalmi, tayi kyau sosai, wayanta ta canja cover zuwa fari ta kalli noor tace "me zan siya miki?"
"babu"
ta janyo blanket ta rufa har kanta dan batason surutu, zuwa tayi ta yaye blanket ɗin tayi mata peck a goshi, rufe ido noor tayi har ta maida mata blanket ɗin ta juya ta tafi, tare da momy wacce tasha atamfa ɗinkin buba da mayafi babba, tayi kyau sosai, ya faruk shi zai kaisu domin Abba zaiyi tafiya, tare suka fita suna tambayan ya jikin noor, da sauki ta amsa, suka fita a tare driver ya fito musu da mota suka shiga faruk ya karɓi key, tafiya sukayi, Abba da yake ciki ya tashi yaje ya duba noor tareda yimata ya jiki? tace lafiya Abba da sauki, sallama yayi mata da niyan sai bayan kwana uku zai dawo, kamar tayi kuka haka takeji domin batason Abba yayi nesa da ita, saida ya shirya yazo ya bata kuɗi dayawa yace ta aje musu itada Haneefa na zuwa school, godiya tayi ya fita saida ta bishi a baya ta rakashi har wajen mota tana ɗaga mishi hannu, ɗaki ta koma bayan ya tafi ta kwanta tana kallon saman ɗakin.

zazzaɓi ta rinƙa ji yana damunta har ta samu tayi bacci da kyar, sai kusan karfe 3 na yamma ta tashi tana murza ido, da mamaki taga su momy basu dawo ba, waya ta ɗaga zata kira haneefa sai kuma ta aje tasan sun ratse wani wajen ne, a hankali ta sauka daga gadon tana jin jikinta weak, cire kayan jikinta tayi kana ta zaro babban towel pink ta ɗaura a kirji, ribbon ɗin dake kanta ta cire nan take gashinta suka barbazo har gadon bayanta, tanada niyan wanke kanta idan tayi wanka, shiga toilet tayi tana murza ido, a hankali ta karasa inda zata zauna domin rage cikinta da takeji ya mata nauyi sakamakon shawarma da tayita ɗurawa cikinta jiya, ta buɗe kenan zata zauna ta hango wani katon snake ya zuro kai yana kallonta, wani irin tsalle tayi ta kwala ihu "snake!!! snake!!! help please help"
shine abinda take iya furtawa gashi ta rufe kofan ta gagara buɗewa.

tsayawa yayi daga ɗaukan takaddan da Abba ya bashi sako ya ɗauka yaba isa ya kai musu a hanya, shi kaɗai Abba ya yadda dashi har yake shiga ɗakinshi, ihu yakeji daga ɗakin, ɗaukan takaddan yayi ya mikawa isa, zai fita yaji ana buga kofan ana cewa "help"
dawowa yayi yana bin inda yakejin ihun da kallo, daurewa yayi ya fara takawa izuwa ɗakin da yaji ihun yana fitowa, noor harta gaji da tsalle kamar zata sume haka take zare ido tana ihu, addu'a yayi a ranshi kafin ya murɗa handle na ɗakin ya shiga, kallon ɗakin yayi yadda yake a kimtse a gyare yasan wannan shine ɗakinsu haneefa, bubbuga kofan toilet take muryanta har ya fara dishewa tace "maciji ku taimaka"
da gudu ya karasa wajen ya fara buga kofan, ganin ba zai buɗu ba ya fara bugawa da karfin gaske, jin ana buga kofan taji ranta ya fara sanyi, muryanta yana rawa tace "please a buɗeni makulli akan gado"
da gudu yaje kan gadon ya fara duba makullin, cikin Sa'a ya samu, ya dawo ya buɗe kofan toilet ɗin kana ya shiga yana kallonta, da wani irin karfi ta rungumeshi, janye jikinshi ya fara ta ƙankameshi sosai dan ta mugun tsorata, ganin taki sakinshi yace "sakeni na duba"
kin sakinshi tayi tana sauke ajiyan zuciya tace "no please karka tafi, zai kasheni"
runtse ido yayi jin yadda take ƙankameshi kamar zata shiga jikinshi, da kyar ya cireta daga jikinshi yaje bakin toilet ɗin yana dubawa, ganin macijin yasa yaje ya ɗau sanda yazo yana fito dashi, ta rakuɓe gefe ta kankame jikinta manyan idanunta a waje, kashe macijin yayi kana yasa akan sandan ya zai fita dashi, komawa bayanshi tayi ta rikeshi tana ihu, "ya subhanallah" ya furta a kasan makoshi jin yadda ta kuma rikeshi tama manta towel ne a jikinta wanda ya fara zamewa har saman kirjinta ya bayyana, kin sakinshi tayi har ya fitar da macijin, hannu yasa yana niyan cireta daga jikinshi yaji bata motsi, juyo da ita yayi yana kallonta, ta lumshe ido alaman ta suma, ɗagata yayi sama ya kaita ɗakin akan gado ya kwantar da ita kana yaje ya ɗibo ruwa yazo yana yayyafa mata a fuska, bata buɗe ido ba sai ajiyan zuciya data sauke me nauyin gaske, kara sa mata ruwan yayi a fuska nan ta buɗe ido tana ganinshi tasa hannu akan riganshi ta rikeshi sosai tana janyoshi jikinta a tsorace tace "ya cijeni maciji"
turo kofan haneefa tayi hannunta rike da fan ice wanda tasan noor tana matuƙar so, tayi mata surprise domin taga tana fushi da ita shiyasa ta siya mata har guda biyu a shoprite, fuska ɗauke da murmushi tace "noory have your favorite ice..."
kasa karasa maganan tayi lokacin da taga noor tana janyo anwar jikinta, roban icecream ɗin ya faɗi kasa da sauri taja da baya tana zaro ido, anwar jin karan faɗuwan abu ya kara ture noor yana kallon inda yaji karan, ganin haneefa tana kallonsu ya janye jiki da kyar ya sauka yana kallonta, nufota ya fara ta fara ja da baya tana mishi kallon tuhuma, noor ta mike taje wajen haneefa da gudu ta rungumeta tana ihu tace "snake"
hannu haneefa tasa ta zameta daga jikinta kana ta juya zata fita anwar yace "haneefa?"
bata juyo ba bakuma ta amsa ba, jikinta har rawa yake domin bataji daɗin yanayin data gansu ba, noor ta koma gado ta janyo pillow da kyar ta runtse ido bacci ya ɗauketa, juyawa yayi ya fita daga ɗakin jikinshi a sanyaye, yayi sa'a ba kowa a falo ya dudduba ko zaiga haneefa bai ganta ba, fita yayi ya wuce dakinshi, zama yayi a bakin gado ya dafe kanshi, me haneefa tayi zato? yaga rashin jin daɗi kuru-kuru a fuskanta, da ya sani da bai shiga ɗakin bama, to ai rai yaje ceto da baije ba baisan yadda noor ɗin zatayi da wannan katon macijin ba, karamin wayan da haneefa ta bashi shi yayi kara ya ɗaga yana kallon me kiran, jameel ne, "Hello"
"ga inna"
bawa inna wayan yayi suka gaisa yana tambayanta ya gida, kuka ta fashe mishi fashi ita dole sai tazo taga inda yake, da kyar ya lallasheta har tayi shiru yace gobe zai zo, ta amsa da to kana sukayi sallama, jameel yana karɓa yace "meyasa ka haɗani da inna kasan kuka baya mata wuya"
dariya jameel yayi "to ba gashi ta daina kukan ba kuma kun gaisa?"
hira sukayi yana tambayan ya jikin Abba, jameel ya amsa da sauki Abba har ya fara fita yanzu, daɗi sosai anwar yaji jin ance har Abba ya fara fita.

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now