chapter 24

45 3 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
  *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_Jiddah S Mapi_

*Chapter 24*

             ~Mamakin turancin daya fito daga bakinta yayi, da wasa yace "inna kece da turanci?"
hannu ta ɗaga mishi fuska ba yabo ba fallasa tace "banson wasa a wannan lokacin"
ganin yayi ta sauya kama daga inna zuwa hajiya, daga yanayin magananta zakaji kamar ta gaji da boko tayi zurfi a karatu, tsit yayi da bakinshi.
daga shi har noor ba wanda yayi magana har flight nasu yayi landing, lokacin da mutane suka fara fita noor ta zaro nikab a cikin jakanta tasa, cusa kai tayi cikin mutane tana neman hanyan da zata samu ta tsere ba tareda ta haɗu da anwar ba, tayi nasaran fita ba tareda kowa ya ganta ba, har bakin airport ɗin taje tana shirin fita taji an riko hannunta, a tsorace ta tsaya ba tareda ta juyo ba, dajin rikon tasan Anwar ne, murya na rawa tace "ka sakeni"
murmushin gefen baki yayi bai saketa ba, ya matso kusa da ita, ta baya ya rungumeta, shinshina wuyanta ya fara yana lumshe ido, ji tayi yana shafa karan hancinshi a wuyanta, da sauri tasa hannu ta baya ta tureshi, ko gezau baiyi ba, hannunshi yasa ya matse cikinta saida tayi kara, mutane sai kallonsu suke suna murmushi, sun zaci soyayya yake nuna mata a idon duniya, a baɗini ita kaɗai tasan azaban rikon da yayi mata, a hankali yace "kina ganin zaki iya tseremin ne?"
girgiza kai tayi, ya daɗa matseta ta runtse ido tana cizan baki dan ba karamin azababben riko yayi mata ba, "ina zakije? wa kika sani a Borno?"
jijjiga kai tayi "babu"
sakinta yayi ya riko hannunta, kallon cikin idonshi tayi, yayi murmushi yace "muje ko?"
a hankali ta fara takawa tana biye dashi, a gefen inna ya ajeta kafin ya ɗau waya yace "mun iso"
shiru inna tayi tana kallonshi yaki yadda su haɗa ido, noor ta zauna kamar akan kaya, hannunta har rawa yake, murza yatsunta take tana kallon kasa, jameel ya lura da halin da take ciki, ga anwar yayi attacking nata da ido, cikin ƴan mintuna taji karan jiniya da hayaniya a kofan airport, buɗe musu akayi suka shiga, convoe na manyan manyan tsala tsalan motoci aka haɗa musu, parking sukayi a cikin airport ɗin kafin suka fito, wasu excort ne masu bakaken kaya, majiya karfi suka fito, jan carpet suka fito dashi aka shimfiɗa daga wajen motan da yafi ko wanne tsada har zuwa inda su inna suke, noor bata kara shiga tashin hankali ba saida taga dogarai rike da manyan bulala, wasu kuma suna hura algaita, anwar ya mikawa inna hannu, a hankali ta mike suka fara jerawa suna tafiya akan red carpet ɗin, noor tana baya ta taƙure jikinta tana tafiya kamar wacce aka zarewa laka, jameel ya rungume jakan dake hannunshi yana kallon kowa ɗaya bayan ɗaya, abin tsoro ya fara bashi, lokacin da suke tafiya gaba ɗaya mutanen wajen suka russuna kasa suna gaisuwa, koda yazo bakin mota wani dogari ya aje hannunshi a kasa alaman anwar ya taka ya wuce, kin takawa yayi kawai ya tsallaka aka buɗe mishi kofan motan da yake sheƙi kamar bayan kwai
"sarki yana maraba da zuwan yarima, an gaida yarima Allah yaja nisan kwana, kaga yarima me jiran gado gabanka sarauta bayanka sarauta, gidanku kun gaji kuɗi kun gaji sarauta, fulani tana gaisuwa"
inna ma ta shiga motan, noor ta makale a bayan wani excort tana leken cikin motan, anwar da yake zaune a ciki ya cire hulan uniform ɗin ya ɗaura akan kafarshi, ya kalleta daga sama har kasa, ganin jikinta yana rawa ya lumshe ido kamar ba zaiyi magana ba, leɓenshi taga yana motsi, kallon tsoro take mishi, a hankali yace "shigo"
maƙe kafaɗa tayi "nikam zan koma garinmu"
wani tsawa da aka daka mata saida hanjin cikinta ya murɗa, wani dogari rike da bulala yace "kinyi karya ƴar talakawa, ke wace da yarima yana magana kina magana?"
a tsorace ta shiga motan ta zauna gefenshi tana karkarwa har hakoranta suna haɗuwa da juna suna bada sautin kat-kat, inna ta kalleta ta ɗauke kai, tausayin noor ta fara ji tunda ta shigo hannun anwar, jameel ya zauna cikin motan da ko a mafarki bai taɓa tunanin zai tsaya a inda yake bama balle ya shiga, kallon anwar yayi abin mamaki yaga ko dariya daya saba mishi yau baiyi ba, hasalima kallo ɗaya yake mishi ya watsar dan bayason tambaya.

saida suka shiga kafin sauran suma suka shiga, fita sukayi daga airport motocin da suke bin bayan masu sunfi talatin, gasu manya manya ciki babu karamin mota, noor sai rarraba ido take har yanzu ta kasa zama me kyau a motan, drivern da yake jansu ma kaɗai tasan yafi ubanta kuɗi, domin wani tsadadden shadda ne a jikinshi da wani sarka wanda tasan idan an siyar zai siyi motocin gidansu, anwar daya lumshe ido ya ɗaga kanshi sama kamar me bacci, tunani kawai yakeyi, ido ɗaya ya buɗe yana kallonta, ganin yadda take murza yatsunta yayi dariya wanda a iya leɓen bakinshi ya tsaya, hannunshi ya ɗaura akan nata, a hankali ya surfa yatsunshi cikin nata, murza ƴan yatsunta ya fara idonshi a lumshe, da sauri ta fara janye hannun, riko yayi mata sosai ta yadda ba zata iya janyewa ba, muryanta yana rawa tace "kayi...kayi..hakuri"
murmushin gefen baki ya mata wanda yake kara mishi kyau idan yayi, cikin murya me cike da izza yace "sorry for what? murza miki nakeyi kuma naga kamar kinaso"
wasu zafafan hawaye ne suka cika mata ido tace "dan Allah kace su saukeni zanje hotel na kwana"
girgiza kai yayi cikin sanyin murya yace "no kin saba zuwa hotel nan garin ba'aso mata suna zuwa, ko bakiso muje gida musha soyayya?"
da wani shu'umin murya yayi magana yana kashe mata ido, "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un allahumma ajjirni fi musibati wa akhlifli khairan minha"
addu'an da take maimaitawa a ranta kenan wanda batasan ma ya fito fili ba, daga nesa ta hango unguwar da suke shirin shiga, wani irin silent area ne wanda aka ƙawata da kayan ado masu kyau, ko wani gida a wajen idan ka gani zaka iya rantsuwa da ruwan gold aka kera, bata gama sarewa ba saida suka isa inda taga manyan dakaru tsaye a kofa an shimfiɗa carpet an rubuta welcome back yarima da manyan harufa an zagaya ko wanne harafi da flower me tsadan gaske, get na gidan ta kalla wanda yasa saida taji idonta yana ɗaukewa dan wani walƙi take gani, gida ne wanda ko a kasar turai bata taɓa ganin irinshi ba, buɗe musu marfin mota akayi shi ya fara fita, sai ita data fito tana nokewa tana rarraba ido, inna data fito durkusawa kasa sukayi "an gaida maman sarki Allah yaja nisan kwana sarki yana miki maraba"
jijjiga kai tayi, da gudu wani yazo da alkyabba a hannunshi ya sawa inna, aka aje mata takalmin sarauta cire na kafanta tayi tasa wanda suka aje mata, Anwar kuma yana daga tsaye sukazo da wani tsadadden alkyabba da hulanshi, sa mishi akayi ya karɓi hulan da kanshi yasa, takalmin sarauta yasa a kafarshi, nan ya fito kamar sarkin makka, kwarjini yayi sosai ga wani kyau da uniform da kuma kayan sarauta sukayi mishi, takawa ya fara ana busa sarewa ana mishi kirari me ratsa jiki, jameel yana daga gefe a hankali ya zame ya sauka daga kan carpet ɗin, anwar ya kalleshi yayi mishi alama da ya hau, girgiza kai yayi cikin girmamawa yace "bazan iya ba yarima"
murmushi kawai yayi yaci gaba da tafiya, noor jakan data rataya ta rike gam kamar zasu kwace mata, kafafunta suna rawa ta fara binsu tana kallon kasan carpet, koda suka isa bakin get remote aka danna nan take get ɗin ya buɗe da kanshi, da sallama a bakinshi ya shiga, gara tashin hankalin data shiga lokacin data ganshi da uniform da wannan tashin hankalin data gani yana jiranta a cikin gidan, wasu mata ne sunsa uniform baki da fari, duk sun kewaye inda zai wuce da alama bayi ne, daga can ciki kuma taga wasu larabawa suna tsaye da alkyabba a jikinsu, ƴammata ne guda biyu ko wacce ta kasa ɓoye farin ciki akan fuskanta, yana shigowa sukazo da gudu suka rungumeshi, kuka suka fara, ya rikesu duka biyu yace "banda kuka"
"you're welcome yayanmu"
da mamaki ta kallesu jin sunyi magana da turanci da kuma hausa, da fari ta zata larabawa ne sai yanzu taga kama a tare dasu da anwar ɗin, jikinsu kamar ka taɓa jini ya fito, sakinshi sukayi sukaje wajen inna wacce take tsaye tana sharan kwalla, rungumeta sukayi "munyi missing naki hajiya babba"
shafa kansu tayi, wata yarinya ce kyakkyawa ta fito daga ɗaki, batafi shekara 7 ba, tayi kyau sosai cikin wani pink na ƴar kanti wanda kasan yake a buɗe, gashinta aka kame gida biyu aka sa mata kyakkyawan ribbon pink guda biyu, ganin anwar ta fara gudu tana son isowa wajenshi, tana zuwa ya ɗaga ta sama yana juyi da ita, dariya takeyi tana murna sosai, saida ya gama juyi da ita ya rungumeta tsam a jikinshi idonshi yana cika da hawaye, ɓoye hawayen yayi yace "i miss you so much my little princess"
hannunta tasa a gashinshi tace "daddy Ina kaje ka barni anan?"
girgiza kai yayi "ba gashi na dawo ba"
giɗa kai tayi tace "where is my mom? kace zaka dawomin da ita ina take?"
idonta ne ya sauka akan noor wacce ta rakuɓe a gefe tana murza hannun jakanta, jikinta yayi sanyi sosai, sauka tayi daga jikinshi taje wajen noor da gudu, noor dake tsaye taji an faɗa jikinta, ganin yarinyar tana mata murmushi yasa ta ɗaga ta, kallon anwar tayi "she's my mom?"
girgiza kai yayi "no"
Inna tayi mishi wani kallo wanda yasa ya ɗauke kai, yarinyar dake hannun noor tace "kece mom nawa?"
noor ta kalli inna wacce take giɗa mata kai alaman tace eh, giɗa kai tayi, da murna yarinyar ta rungumeta tace "yeah nima zan yiwa su nihal gwalo ince musu momy na is back"
sharan hawaye kawai anwar yakeyi, leɓenshi na kasa a cikin bakinshi yana ciza da karfi yanajin zafi a ranshi.

HAƘƘI NAUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum