chapter 6

54 3 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
    *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_jiddah S Mapi_

*Chapter 6*

              ~da asuba haneefa ce ta fara tashi, miƙa tayi tana salati bayan ta kunna wutan ɗakin, idonta ne ya sauka akan kayan dake kasa rigan noor da wando dasu jaka, kallon noor tayi wacce take bacci sosai gashinta ya kwance ya barbazu akan pillow, gabanta ne ya faɗi ta fara tunanin ina taje da wannan kayan? sauka tayi daga gadon ta kwashe kayan ta kai washing machine, takalmin ta maida a ma'ajiyan takalma, alwala taje tayi kana tazo ta tada salla, saida ta idar ta fara tashin noor tareda kiran sunanta "noor tashi kiyi salla"
turo karamin bakinta tayi sannan ta buɗe ido ɗaya ta kalleta, komawa tayi ta kara jan duvet ɗin baccinta taci gaba dayi, haneefa ta kara tashinta cikin bacci tace "am off banayi"
shiru tayi "to kodai date nata ya canja?"
girgiza kai kawai tayi sannan ta juya ta fita daga ɗakin, kitchen taje ta fara taya mai girki aiki, saida suka haɗa breakfask sannan taje ɗakin Momy ta gaisheta, Momy tace "noor kam tana aikin nata na bacci ko?"
"eh momy bacci take"
"tayi salla ne?"
"a,a tana off"
"okay"
tashi Momy tayi suka sauko tareda haneefan, yau weekend kowa yana gida harda Abba dasu ya faruk, Abba ne ya fito daga ɗakinshi hannunshi rike da jaka yasa haneefa ta kira mishi driver ya bashi sako zuwa bank, zama yayi akan kujeran dining yana tambaya ina noor?
haneefa tace "bacci take"
faruk ya fito daga ɗaki yana kallon makullin dake hannunshi, gani yayi kamar gefen key holder ɗin ya karye, waje ya fita zuwa wajen compound ya duba motanshi, waro ido yayi ganin yadda gaban glass ya fashe ga taya yayi faci komai na motan ya ɓaci, da karfi ya kira me gadi, yana zuwa ya durkusa, "waya fita da motata?"
me gadi ya kalli motan, sai yanzu yaga abinda ya faru, hannu yasa ya dafe kirji kana yace "yallaɓai wallahi ban sani ba"
"baka sani ba? kamar yaya? waye a bakin get?"
"wallahi bansan wanda ya fita da motan ba, ni dai na san jiya da wuri nayi bacci amma banga kowa ya fita da mota ba"
yana magana jikinshi yana rawa, ran faruk ya ɓaci sosai, da karfi ya fara kiran duk ma'aikatan gidan, suka taru a gabanshi yana tsaye yana karkaɗa makullin, kana ganinshi kasan ranshi ya ɓaci, yana son motan sosai har cikin ranshi, sannan Abba bai daɗe da siya mishi ba, 2weeks kacal motan yayi, tambayansu ya fara waya taɓa mishi mota? kowa yace bai sani ba, girgiza kai yayi "kuje shikenan"
komawa ciki yayi ranshi yana tafasa ya fara kwalawa Noor da haneefa kira.
tana zaune akan sallaya sai yanzu taga dama ta tashi tayi salla, jin ya faruk yana kwala mata kira taji kamar ta tsula fitsari a wando, a take idonta ya fara raina fata, ta san yau ta kaɗe har ganyenta.

jin kiran yaki tsayawa Momy da take zuba abinci wa Abba ta kalleshi tace "meya faru kake kiransu haka?"
"momy tambayansu zanyi"
"okay"

hijabin dake jikinta har kasa purple ne daga sama an ɗaure da igiya baki, tafiya ta fara jikinta yana rawa, zuba mata ido yayi yadda take taka stair kamar zata faɗi, kanta a kasa har ta karaso gabanshi ta durkusa, haneefa ma tazo ta durkusa, yana daga tsaye yace "waya shiga motata jiya?"
shiru ba wanda ya amsa, tsawa ya daka musu "i said who use my car?"
jikin noor ya fara ɓari tayi rau rau da idanu, bakinta yana rawa tace "n.."
haneefa tace "nice"
kallonta noor tayi da mamaki yadda ta amsa itace tayi wannan laifin, faruk ya kalleta sosai yace "are you sure?"
girgiza kai tayi "eh jiya ne aka kirani a waya ƙawata tayi accident itada driver ɗinsu kuma dare yayi shiyasa na shiga kawai naje wajen"
yana huci yace "ina taje?"
"tayi tafiya ne shine dare ya kamata"
"wace kawar taki?"
"Elham"
wayanshi ya ciro daga aljihu yace "bani number ɗin gidansu"
numbern Elham ɗin ta bashi ya karɓa sannan ya kalleta, looking serious yace "idan na kira naji saɓanin abinda kika gayamin kinsan me zai biyo baya"
jijjiga kai tayi, ya danna call, kira ɗaya Elham ta ɗaga tace "ya faruk good morning"
"morning ya jikin naki?"
a hankali tace "da sauki"
"bakiji ciwo ba kam?"
"eh kafata ce ta ɗan gurje amma haneefa tazo sun kaini hospital a daren an wanke"
"okay Allah ya Kara sauki"
"ameen na gode sosai ya faruk"
katse wayan yayi, "daga yau idan abu ya faru kada ki kara kuskuren tafiya ke kaɗai, bakya tsoron hanya ne?"
"am sorry"
Abba yana jinsu har ya gama faɗan suka dawo wajen cin abinci"

HAƘƘI NADove le storie prendono vita. Scoprilo ora