chapter 13

44 1 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
    *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_jiddah S Mapi_

*Chapter 13*

*Last free pages daga wannan mun gama free pages*

              ~ji kake tass, karan fashewan kwalban turaren, a tsorace ta shigo ɗakin ta kalli sani driver tace "wa aka sace?"
a tsorace yace "amarya"
hannu ta ɗaga zata kai mishi mari Abba ya rike hannun, kofa ya sannan cikin dauriya yace "mutane suna nan dayawa kada kiyi kowa yasan abinda yake faruwa, mu kwantar da hankali akwai manyan baki wanda suke nan, calm down musan yadda za'ayi"
jikinta har ɓari yake cikin tsoro tace "karsu illatamin yarinya"
hannu yasa a bakinta ya rufe, "ba abinda zasuyi mata"
waya ya ɗaga ya kira layin noor, kira biyu ta ɗaga yace "sameni a ɗakina"
tashi tayi daga zaunen da take tasa hijabi akan makeup ɗin da yake kwance a fuskanta, ɗakin Abba taje ganinsu cikin tashin hankali sai taji ba daɗi, to amma tana yin haka ne domin gyara rayuwan haneefa na gaba, durkusawa tayi "Abba gani"
share zufa yayi kana yace "inaso kimin wani alfarma"
jijiga kai tayi, yace "kisa kaya irin na amare kije wajen lunching a matsayin haneefa"
a tsorace ta ɗago tace "matsayin haneefa kuma Abba..."
hannu ya ɗaga mata "banason ta bambayoyi kiyi abinda nace kawai"
tashi tayi ta fita, tasan dai itace tace a ɗauke haneefa amma bata taɓa zaton su Abba zasuce tasa kayan amarya taje wajen lunching ba, a zatonta zasu haɗu ne duka su fara neman inda haneefa take, da haka dai har tasa kayan da haneefan ta cire wanda ya matukar yimata kyau, momy ce ta shigo da farin mayafi irin wanda amare suke sawa a kansu su rufe fuska, takalmi dogo fari itama momy tasa mata, ta fesa mata turare, hannunta ta riko suka fito tare, fuska a rufe babu me ganinta, abba yasa a canja mota aka yiwa wani daban ado, da kanshi ya buɗe mata marfin motan ta shiga,
anwar sai kiran numbern haneefa yake baya tafiya, ya fara gajiya domin sun kusa 1hour basu zo ba, gashi baida number ɗin noor, koda yana dashi ma ba zai kirata ba, jameel ya lura da yana cikin damuwa ya matso yace "yi hakuri zasu so ai, kasan shirin amare"
"jameel mutane da suna jiranmu acan"
karan tsayuwar mota sukaji, jameel yace "to gasu nan"
saida su inna dasu kannen jameel suka shiga mota, kafin ya fito ya shiga motan da amarya take, gabanta ne ya faɗi jin ƙamshin turarenshi ya buga mata hanci, cikin nutsuwa ya zauna, duk motocin suka jeru a layi suka fara tafiya, saida suka ɗau hanya, kirjinta sai bugawa yake, kallon lallenta yayi yaga sai murza hannu take ga kanta a rufe, hannu yasa ya riko hannunta baiyi magana ba sai murza ƴan yatsunta yake, jikin noor ne ya fara rawa ji take kaman ta janye hannu, amma tana tsoron kada ya gane, kallon karamin yatsanta yayi, jan lalle da bakin yayi mishi kyau sosai, a hankali ya kai yatsan cikin bakinshi, ba zato taji ya fara tsotsan karamin yatsanta, runtse ido tayi kaman tayi ihu ta daure tana zazzare ido a cikin mayafin, saida ya tsotsa sosai kafin ya cire, matso da bakinshi yayi saitin kunnenta yace "kinyi kyau, lallenki yayi kyau"
giɗa kai tayi, yace "yau ba shagwaɓa ne? ko kunyata kike ji?"
jijiga kai tayi, yasa hannu zai ɗaga mayafin a tsorace tasa hannu ta rike hannunshi, murmushi yayi "yau kin zama me tsoro fuskanki kawai zan gani kaɗan, nayi missing naki sosai"
kin magana tayi, ji take kaman ta tsala ihu, wai yau itace da wannan me raken suna zaune waje ɗaya? dolene ta koya mishi hankali ta nuna mishi asalin bambancin dake tsakaninshi da haneefa, banza talaka mara galihu, ace motocin biki ma saina gidansu zai taho a ciki, kato dashi baida ko mota guda"
sun kusa isa hall ɗin taji yasa hannu ya janyota jikinshi, a kunne ya raɗa mata "ko kimin magana ko nayi kissing naki"
hannu tasa ta fara tureshi, yaki sakinta har driver yayi parking, matsowa yayi kusa da ita sosai har tana jiyo sautin numfashinshi, hannunta ya kamo wanda take tureshi dashi, saida ta daina motsi tsaban rikon da yayi mata, kasa da murya yayi a kunnenta ya raɗa "yanzu fa ke matata ce, ba budurwa ta ba, muyi kiss, na jima inason hakan amma na ɓoye saboda haramci, yanzu an ɗaura mana aure please ki bari inyi"
fizge kanta ta fara jin kalaman da yake mata, wani irin tashin hankali ta shiga kamar tayi magana ya gane bada haneefa yake tare ba, kara matsowa yayi "inyi?"
girgiza kai tayi kana ta fashe da kuka, jin sautin kuka yasa hannu a bayanta yana taping kaɗan, "sorry shikenan na fasa, banda kuka"
sauke ajiyan zuciya tayi ya riko hannunta suka fito tare, a hankali suke takawa ana musu liki, hannunshi a cikin nata tana ji yana murzawa har suka isa inda aka tanada domin zaman ango da amarya, a tare suka zauna, su Abba da manyan bakinshi aka fara gudanar da shagalin biki, hankalin momy baya kanta kamar yadda Abba ma dauriya kawai yakeyi, Allah Allah yake a gama kira commissioner ya sanar mishi abinda yake faruwa, yanzu baison tada hankalin jama'a ne, kiran ango akayi da amarya su shigo fili, bayan sun shiga noor taso tayi rawa sai kuma ta tuna haneefa bata iya rawa sosai ba, matsowa yayi ya rike ƙugunta a hankali yace "ba kince zakimin rawa ba ranan aurenmu?"
girgiza kai tayi, yace "to meyasa bakiyi?"
kai ta kuma girgizawa tana janye hannunshi daga waist nata, matsowa yayi kusa da ita sosai yace "ba zan sakeki ba sai kinyi rawa"
mutane suka fara tafi, jameel yazo yana watsa musu kuɗi, abin ya birge mutane, mc yace su koma su zauna, komawa sukayi abba yana kallon mami, faruk ne ya shigo hankali a tashe, Abba ya mishi alama "an ganta?"
kamar zaiyi kuka ya girgiza kai, tashin hankali su Abba suke ciki babu wanda yake da nutsuwa cikin su uku harda sani driver, haka dai suka daure ake gudanar da lunching, saida aka kusan tashi aka fara raba abinci da drinks masu tsada, bayan kowa yaci ya koshi za'a tashi mc ya ɗau mic yace yana da muhimmiyar sanarwa, ai kuwa kowa ya bada hankalinshi, ya fara jawabi kamar haka.

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now