chapter 11

46 2 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
    *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_jiddah S Mapi_

*Chapter 11*

              ~Bayan kwana biyu Abba ya kira anwar a waya yace "ina airport kazo ka ɗaukeni"
bin wayan anwar yayi da kallo bayan Abba ya kashe, ga driver Amma meyasa yace ni zanje na ɗaukoshi?
dama yana wajen flower wanda suka jara kyau suna kamshi yana bayinsu, haneefa ce ta bashi maganin da zaisa musu su kara kyau dan ta lura kamar ansa musu chemical ɗin da zai kashesu ne, ya ajiye pipe yaje ya shirya cikin kananan kaya ya samu sani driver yace "bani makullin mota Alhaji yace naje na ɗaukoshi"
bashi makullin yayi yace "Allah ya tsare"
karɓa yayi yaje compound ya shiga motan da yaga ana yawan fita da Abba a ciki, fita yayi a unguwan yana karewa ko ina kallo, da haka har ya isa babban airport, fitowa yayi daga motan yana neman Abba, can ya hangoshi hannunshi rike da babban bakin jaka, manyan kaya ne a jikinshi, da sauri ya karasa yace "sannu da dawowa Alhaji"
abba ya mika mishi hannu suka gaisa yace "ya gidan ya zaman bakunta koda shike ai yanzu ka saba ko?"
giɗa kai yayi yana karɓan jakan dake hannunshi suka karasa ya buɗe mishi kofan mota cikin girmamawa, Abba ya shiga shima ya zagaya ya shigo, sai sannu yake yiwa Abba, Abba ya saki jiki dashi yana janshi da hira har suka isa gida, sai a sannan Abba yace "aina ka koyi mota?"
"motan abokina nasir a wurinshi na koya"
"madalla gashi ka kware sosai"
fita sukayi bayan yayi parking, ya fito ya buɗe mishi marfin motan shikuma ya ɗau katon bakin jakan ya rataya a bayanshi suka jera suna tafiya, jin sallaman Abba yasa momy ɗagowa da sauri, kallonshi tayi tana zaro ido alaman ya mata surprise ta mike da ɗan gudunta taje ta faɗa jikinshi, riketa yayi yana dariya anwar ya tsaya a baya yanajin nauyin ganinsu a haka, noor da haneefa suka shigo a tare da uniform na school a jikinsu da gudu noor taje ta rungume Abba tana dariya tace "Abba yaushe ka dawo?"
shafa kanta yayi "yanzu saukana"
haneefa kuma kallon anwar wanda ya kawar da kai daga kallonsu Momy tayi, da alama hakan sabon abune a wajenshi, ta kashe mishi ido tareda turo ɗan karamin bakinta sannan tayi mishi kiss, da sauri ya ɗauke kai dan baison Abba ya gansu, dariya tayi taje wajen Abba tace "Abba ka dawo? Ina tsarabata?"
"to haneefa ƴar son tsaraba sai anjima zan baki"
rungumeshi tayi tace "to Abba"
kallon anwar wanda yake tsaye yayi kafin ya cire makulli a aljihu ya mika mishi "gashi ajemin jakan a ɗakina"
karɓa yayi ya wuce inda yasan ɗakin Abban yake, buɗewa yayi ya aje jakan kana ya fito ya maidawa Abba makullin yace "gashi na aje"
"yawwa anwar na gode ko?"
giɗa kai yayi sannan ya fita, momy ta bishi da kallo tana murmushi nutsuwan yaron ya birgeta, shiyasa takejin daɗin abotan da suke da faruk, gashi sun shaƙu kamar dama sun san juna, har faruk ya san su jameel da inna, kullum sai anwar ya bashi labarinsu.

Faruk ma yazo suka gaisa da Abba yayi mishi ya hanya yana wani sunnar da kai, Abba yace "meya faru naga sai sunnar da kai kake?"
shiru yayi, kana yace "ba komai Abba"
momy ta kalli Abba sannan tace "jeka faruk"
tashi yayi ya tafi ta kalli Abba tace "me yasa yake wani jin kunya?"
murmushin gefen baki Abba yayi "ba komai wani voice kawai ya turamin shine yake jin kunya"
"muji voice ɗin"
"keda wa?"
marairaicewa tayi "nida kai mana"
hancinta yaja yace "ni ai naji kuma na goge"
ta san baiso taji ne kawai, sharewa tayi domin bata takura mishi akan komai.

haneefa tana murna domin tunda abba ya dawo ta san zai tsaida maganan aurenta da anwar, noor ta kula da haka, ta kudiri aniyan saiya bar gidan kafin haneefa ta ɗago maganan aure tsakaninsu, itafa ko jikokinta ba zasu auri talaka ba balle yayarta wacce suke ciki ɗaya.

cikin dare Abba ya gyarawa jakan wajen zama domin kuɗi ne na mutane da gwala-gwalai a cike da jakan haka yasa yake bawa jakan tsaro sosai, ko momy batasan abinda yake ciki ba, har suka kwanta bacci Momy a gefenshi yana kallon jakan, can cikin dare ya tashi zaisha ruwa bai kula da inda jakan yake ba saida yasha ruwa sosai kana ya koma zai kwanta, baya ya koma yana shirin faɗuwa ganin babu jakan a inda ya aje, numfashi ya fara yi da karfi yana kiran sunan momy "sadiya!! sadiya?"
a hankali ta buɗe ido tace "meya faru?"
"ina jakata?"
tashi tayi ta murza ido tana kallonshi "jaka kuma?"
girgiza kai kawai yayi domin ya rasa bakin magana, da sauri ta sauko daga kan gadon ta rikeshi ganin yana dafe kirjinshi, cikin tashin hankali ta taimaka mishi ya kwanta kan gado yana so yayi magana ya kasa, dudduba ɗakin ta fara babu jaka, hankalinta ya tashi, gashi Abba ya fara numfashi sama-sama, buɗe kofan ɗakin tayi tana kiran "faruk?"
yah faruk dake bacci yaji sautin muryan momy tana kwala mishi kira, da sauri ya kalli agogo yaga karfe 2, baisan lokacin daya sauko ya fita ba, ganinta a rikice yaje ya riketa yana tambayan meya faru?
da kyar tace "Abbanku yana numfashi sama-sama"
har suna rige-rige wajen shiga ɗakin, Abba ya gani kwance akan gado yaje da gudu yana ɗagoshi yace "abba what happen to you?"
girgiza kai Abba yayi da kyar ya furta kalman "jakata"
"ina jakan naka?"
"ban gani ba umar"
dubawa faruk ya fara baiga komai ba, tare da momy sukayi niyan fita Abba yace "kada ku ɗaga hankalin kowa da daren nan kuma kada abar kowa ya fita har zuwa safiya, faruk kaje ka tsaya a kofa kada kayi bacci"
jijiga kai yayi ya fita da sauri yana duba cikin gidan, baiga komai ba, zama yayi a mazaunin me gadi yana kallon ko ina na cikin gidan, momy kuma ta bawa Abba tablet nahsi yasha ya kwanta, tagumi tayi "Allah ka rufa mana asiri dukiyan mutane ba namu ba"
ta san dana Abba ne ba zai damu har haka ba.

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now