chapter 12

38 5 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
    *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_jiddah S Mapi_

*Chapter 12*

              ~Ta sameta a ɗaki ta kwanta rub da ciki tanajin ranta kamar wuta, a hankali ta tura kofan ta shigo, towel karami ta ɗauka first ta fara tsane gashinta wanda ya jiƙe da ruwa, cire kayan jikinta tayi kana tasa riga da wando buɗaɗɗe, kallon noor tayi tana cigaba da tsane gashin tace "a koda yaushe idan kika shiga tsakaninmu sai Allah kara kusantani dashi, meyasa ba zakisa a ranki wannan haɗin Allah bane, kuma babu wanda ya isa yaja da ikonshi?"
kwafa tayi tana kallonta ta cikin madubi ko motsawa batayi ba, ta san ba bacci take ba, tace "you have to respect him sabida zai zama mijin yayarki, and shi ɗin abokin yayanmu ne, noor kada negative behavior ɗinki ya haifar mana da matsala watarana, you know I love you but your love can't stop me from loving my love"
"you can't love him sama dani"
kallonta tayi tana daga kwancen tayi maganan, murmushin takaici tayi kana tace "there's different between love and love, akwai so na jini wanda ɗan uwa yake yiwa ɗan uwa, akwai kuma so me shauƙi wanda masoyi yake yiwa masoyi, Yah faruk is my brother zan iya hugging nashi ko sau ɗari ne a rana ɗaya banji komai ba, shima haka, but Anwar is my love da nayi hugging nashi zanji shauƙi, zanji kamar na shiga jikinshi ko zuciyanshi na huta, noor ki gane mana, ki gane irin soyayyan da Allah ya ɗauramin na anwar, nima da zan iya cireshi a raina dana cire ko dan na zauna lafiya dake, but i can't, ko wani rana jinshi nake yana kara shiga raina, a duk lokacin daya kalleni ji nake kamar kada ya daina kallona, noor inason Anwar please ki dawo normal ki daina nuna mishi halin da babu kyau"
"ba komai zan daina"
murmushin jin daɗi tayi "that's my sis I love you"
murya ƙasa tace "love you too"

washe gari Abba yace suje da faruk ya nuna mishi komai na company, yayi godiya yace "Abba ina neman alfarma"
Abba yace "ina jinka me kake so?"
"zan koma wajen inna ta saboda ita kaɗai take zaune"
giɗa kai Abba yayi "ba komai ka gama aikinka ai amma ka bari sai gobe ko yau kakeson tafi?"
"a,a zan bari sai gobe"
"amma zaka rinƙa zuwa kana dubamu ai ko?"
"eh Abba"
tareda ya faruk suka tafi company aka nuna mishi komai ya kuma fahimta dama business ya karanta hakan bai bashi wahalan ganewa ba, office nashi me kyau aka bashi makulli ya kalla tareda godewa Allah wanda ya kawoshi wannan matsayin ba tareda yasha wani baƙar wahala ba, duk da yasha wahala a rayuwa to gashi Allah ya dubeshi.

tun a ranan ya fara aiki kuma Alhmdllh ya gane komai, koda zai koma gida Abba ya turo driver a ɗaukeshi baiji daɗi ba domin yafiso ya tafi da mashin nashi wanda ya saba da hawanshi, koda ya koma gida Abba yace ya aikin?
godiya yayi yacewa Abba bayason driver yana zuwa ɗaukanshi zai tafi da kanshi, ganin yafi sakewa da tuƙa mashin Abba ya amince da kudirinshi, koda dare sukasha waya da haneefa kaman gari ba zai waye ba, har bacci ya fara ɗaukanta yace "haneefa?"
kin amsa mishi tayi ya kuma cewa "haneefa"
muryanshi kasa, ganin bata amsa ba ya kalli wayan yayi murmushi da may be tayi bacci ne, yace "saida safe"
a hankali tace "uhummm"
"bakiyi bacci ba?"
murya a shagwaɓe tace "um um sai kayi bacci zanyi nima"
"meyasa?"
"no sai kinyi kafin nayi dai"
"a,a nikam ba zan iya bacci ba idan banji sautin numfashinka a kunnena ba"
lumshe ido yayi haneefa tana sashi cikin wani hali shiyasa yake gujewa yin waya da ita musamman da dare, ganin yayi shiru tace "to kayi"
muryan da take magana dashi shi yafi komai ɗaga mishi hankali, ji yayi kamar ya kashi wayan sai kuma yace "kiyi bacci na fara jin bacci kinsan gobe zakije makaranta ko?"
kamar zatayi kuka tace "to kamin yadda zanyi nayi baccin dan na kasa yi"
ya rasa me zai mata a hankali yace "rufe idonki"
rufe ido tayi, kasa yayi da murya a hankali ya fara furta mata kalman "i love You"
da haka har yaji ta fara numfashi a hankali, murmushi yayi tayi bacci, har zai kashe wayan sai kuma yace bari ya bari tayi nisa, noor jin tayi bacci ta ɗago kai tana kallon wayan da yake haske, sunanshi ta gani ɓaro ɓaro an rubuta Anwar Darling da alaman love a gaban sunan, hannu ta ɗaga zata maka wayan da kasa taji an riko hannunta, haneefa ce cikin bacci tace "ka kara cewa i love you"
a hankali ta kara wayan a kunnenta, ji tayi yace "i love you so much, kiyi bacci karki makara gobe, ba naji muryanki kamar kinyi bacci ba?"
giɗa kai tayi domin noor tasa wayan a speaker, girgiza kai tayi "ina sonka"
"ina sonki, ina sonki, ina sonki"
da haka har ta koma baccin"
jin tayi shiru yace "good night"
bin wayan Noor tayi da kallo bayan ya kashe, aje wayan tayi tasa hannu akan pillow ta danne a fuskanta nan ta tsala wani irin ihu kaman ta haukace, da kyar tayi bacci ranan ji take kaman taje ɗakinshi tasa mishi pillow har sai ya mutu kafin ta fito.

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now