chapter 17

23 5 0
                                    

*HAƘƘI NA*

By
_jiddah S Mapi_

17.

                ~Tana shiga tana kallon mutane sai kallonta ake tayi fuska ta fara neman inda number 14 yake, a tsorace take amma tayi ta maza tana addu'a, saida ta rinƙa zagaya a wajen kafin ta haɗu da room 14, cikin tsoro tayi knocking, text ya shigo tana dubawa taga yace _ki shigo a buɗe yake_
shiga tayi bakinta da sallama, tana rarraba ido har ta isa tsakar ɗakin, komai a kimtse kan gadon an shimfiɗa fararen bedsheet ga kuma kamshi da yake ɗakin, kalle kalle ta fara bataga kowa ba, a hankali tace "gani nazo"
kana jin muryanta kasan a tsorace take, tayi kusan 1hour a wajen tana kiranshi yana rejecting, sakone ya shigo tana dubawa yace _duba kan gado na aje miki flower dama shi nakeso na baki_
idonta ne ya sauka akan wani red flower guda ɗaya a tsakiyan gadon, idonta ne ya cika da hawaye a hankali ta karasa bakin gadon tasa hannu ta ɗau flower, a jikin flower an rubuta i love you da manyan harufa, zama tayi a bakin gadon ta fashe da kuka me tsuma zuciya, kiranshi tayi a waya yaki ɗagawa saida ta tura mishi sako _akan wannan ka fito dani zuwa hotel?_
emoji na dariya ya tura mata, tace _where did you get my new number?_
saida ya ɓata lokaci kafin yace _a wajen me motan da kika taimaka mishi ya kira yayarshi tana hospital_
wani sabon kuka ta fashe dashi, saida tayi me isanta kafin ta mike, jikinta very weak, fita tayi daga ɗakin taga har 9 da rabi yayi, da kyar ta samu taxi ya yadda zai shiga da ita lungun gidansu anwar, gyangyaɗi ta fara a cikin taxin tana jin wani irin bacci yana ɗaukanta domin ta gaji, yana ajeta ta fito ta bashi kuɗinshi ta nufi gida tana rufe ido, buɗe kofan tayi ta shiga tana layi kamar wacce tasha wani abin, inna ta kasa bacci sai lekawa take ko zata dawo, hankalinta yaki kwanciya bataso wani abin ya sami noor domin za'a iya zargin anwar, ganin ta shigo tace "kin dawo?"
cikin muryan bacci tace "eh"
wucewa tayi ciki, inna ta bubbuga anwar wanda yayi kamar yana bacci tace "tashi ta dawo jeka rufe kofan gidan"
tashi yayi ya rufe kofan ya nufi ɗakin inna, da sauri tace "ka manta ba anan zaka kwana ba"
girgiza kai yayi "inna anan zan kwana"
"banason musu kaje ɗakin matarka"
da sauri yace "matata? matar da take zuwa hotel itace matar aure?"
inna ta lura ranshi a matuƙar ɓace tace "kayi hakuri ka bita a hankali har ku rabu kaji?"
giɗa kai yayi kana ya mata saida safe ya tafi, da sallama ya shiga ta cire hijabin ta wurgar a gefenta, wando ne iya gwiwa a jikinta sai vest mara hannu pink, ta baza gashinta ta turo karamin bakinta tana bacci cikin nutsuwa, ji yayi kamar ansa mishi barkono a kirji, wannan kyaun ɗan maciji take dashi, a fuska da jiki kyakkyawa ce ajin karshe amma dafinta ba karamin dafi bani, harma yafi na maciji illa, toilet ya shiga yayi alwala yazo ya shimfiɗa sallaya ya tada salla, har karfe biyun dare yana salla bai runtsa ba, yana dab da sallama yaji ta fara kuka "haneefa a bani ruwa, unty haneefa ki bani ruwa inajin ishi"
kuka takeyi tana cewa abata ruwa, sallamewa yayi, addu'a ya fara hannunshi sama yana rokan Allah yajikan haneefa da waɗanda suka rigamu gidan gaskiya, bayan ya shafe addu'a ya kalleta yaga harda hawaye, a hankali ya mike ya ninke sallayan, wajen frij yaje ya ɗauko goran ruwa yazo gabanta, gefen gadon ya fara bugawa alaman ta tashi, sai jujjuya kai take tana cewa "ruwa"
ganin ba zata tashi ba ya zauna a gefenta ya ɗago kanta kana ya ɗaura mata goran a bakinta, sha ta fara, tayi kusan rabin goran swan water kafin ta ɗauke kai, kwantar da ita yayi, yana shirin rufe goran yaga ta buɗe ido, murtuƙe fuska yayi, ta karɓe goran ta buɗe, a fuska ta tsiyaya mishi ruwan tana kallon cikin idonta, lumshe ido yayi yanajin saukan ruwan a fuskanshi, saida ta karar duka kafin ta wurga goran kasa, fararen kafafunta tasa ta sauko dasu, tashi tayi daga kan gadon tana kallon jikinta, tsaki taja cikin raini da tsiwa wanda ya riga ya zama jikin jikinta tace "dole nayi wanka wannan kazamin jikin naka ya taɓa ni matsiyaci talaka mara galihu"
shiga toilet tayi saida tayi wanka ta ɗaura towel ta fito tana gyara gashinta, tashi yayi ya cire rigan jikinshi yasa jallabiya blow me laushi, pillow ya ɗauka ya shimfiɗa a kasa ya kwanta, wayanshi ya buɗe yana kallon hotonshi da haneefa wanda suke zaune itace tayi musu hoton sunyi kyau sosai a ciki, wayan ya ɗaga yasa a kirjinshi yana missing nata sosai, kara kallon hoton yayi a hankali ya kai wayan bakinshi ya yiwa hoton kiss yanaji kamar itace a gabanshi, wasu irin zafafan hawaye suka cika mishi ido, saida ta gama shafe shafenta kana ta mike tasa rigan bacci me laushi ta faɗa gado tareda kashe wuta, lumshe ido tayi da niyyan yin bacci, haneefa ta gani cikin farin kaya tana tareda yara suna wasa, sunanta ta kira koda ta juyo sai taga ta haɗa rai tana kallonta, matsowa ta fara ta rike wuyanta tace "ki faɗi ke kika kasheni"
da karfi ta fara ihu "zan faɗa wallahi zan faɗa, kiyi hakuri zan faɗa"
anwar daya fara bacci yaji muryanta tana ihu, tashi yayi ya zaci mafarki yake, haska wayanshi yayi kana ya kunna wutan ɗakin, sai birgima take tana cewa "zan faɗa!!! zan faɗa!!!"
jin yasa hannu yana tashinta tayi sauri ta rike hannun, janyoshi tayi zuwa kan gadon da karfi ta rikeshi tana shiga jikinshi kamar zata tsaga ta shiga har cikin kashi da fatan dake jikinshi, janyeta ya fara, jikinta yana ɓari sai zufa takeyi ta kara rikeshi sosai tana cusa kanta a kirjinshi, ganin yadda ta tsorata yasa ya kyaleta, jinta a jikin mutum tsoron ya ragu taji dama dama, saida ta nutsu sosai kafin ya fara zameta daga jikinshi, da kyar ya cireta yasa mata pillow ta rungume kafin ya sauka daga kan gadon, kwanciya yayi yana tunanin kalman da take maimaitawa na zan faɗa, to me zata faɗa? da wannan tunanin yayi bacci.

Abba yana kan bincike har yanzu akan mutuwan haneefa,

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now