chapter 25

46 6 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
  *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_Jiddah S Mapi_

*Chapter 25*

             ~Meerah ce ta fita zuwa inda bayi suke karɓan abinci ta karɓo plate ɗaya ta dawo ɗakin, noor tana zaune idonta yana kan slin har yanzu sai hawaye da suke zirara kamar ba zasu tsaya ba, zama tayi a gefenta ta riko hannunta cikin son tausasa mata zuciya tace "ki daure kici abinci kada ulcer ta kamaki"
idanunta a kafe tace "idan ulcer ya kama ni me zaiyi?"
cikin sanyin murya Meera tace "zai kashe ki"
murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tace "to dan Allah ki barshi ya kamani, inaso na mutu"
da mamaki tace "haba noor kefa musulma ce ki yadda da ƙaddara mana Alkhairi ko sharri, wannan jarabawan da kike ciki na shiga wanda ya ninka naki goma, da zakiji tarihina da ba zakiyi kuka akan naki kaddaran ba, dan Allah ki daure kici"
kinci tayi sai kuka take ta rasa me zuciyarta yake raya mata, gashi kuru-kuru tana kallon haneefa kuma ace mata ba haneefa bace?
da kyar Meera ta samu taci abincin kaɗan tasha ruwa, kwanciya tayi tana tunani har bacci ya ɗauke ta domin ta gaji sosai, meera fita tayi daga ɗakin ganin ta samu bacci, noor tana cikin bacci taji an watsa mata ruwan sanyi kamar kankara, firgigit ta tashi tana murza ido, ganin wata mata katuwa da kiɓa sosai tayi a kanta tana murmushin mugunta, sanyin ruwan taji har cikin kashinta, bakinta yana rawa tace "me na miki?"
kara watsa mata ruwan tayi, a fusace ta mike zata kai mata mari, ji tayi an rike hannunta da karfi kamar za'a karya, matar babu alaman dariya a tare da ita tace "ke? ni zaki mara? Lalle zakiyi rayuwan kunci a gidannan lalle zaki gane ke karamar kwaro ce"
karɓan uniform tayi daga hannun wata wacce take gefe ta tsaya cikin girmamawa, mika mata tayi "kisa yanzu ki fito aiki zakuyi"
karɓa tayi domin ta matuƙar tsorata, matar ta juya ta fita, noor ta warware kayan, riga da zani ne blue black, na zani da farin riga, sai ɗan kwali irin zanin, kallon jikinta tayi kana ta kalli kayan, wani irin kuka ne yazo mata, faɗawa tayi kan gadon ta fara kuka, saida tayi me isanta kafin ta mike tasa kayan a gajiye, ba karamin kyau kayan yayi mata ba, musamman ɗankwalin domin ya haskata sosai, gashinta ta kame waje ɗaya ta cusa cikin ɗankwalin, a tsorace ta fito daga ɗakin tana kallon cikin gidan, wani slipas ta gani an aje mata a bakin kofa, sawa tayi a kafarta ya mata yawa amma haka ta lallaɓa tasa, daga nesa ta hango masu irin uniform nata ciki harda meera suna durkushe ana musu jawabi, kafanta har yana harɗewa ta isa inda suke, durkusawa tayi taga matar data watsa mata ruwa itace take jawabin, "saura zasuyi wanki saura kuma zasuyi girki, ku rabu kashi biyu"
giɗa sukayi su duka suka mike, sun rabu kashi biyu noor tana cikin masu girki, godiya ta yiwa Allah dan batason wanki, ai kuwa aka bata babban tukunya ta wanke, ta girka, matar tace "girki me daɗi zakuyi domin kanin yarima yana hanya, zaizo yaga yayanshi"
tafiya aka fara dasu zasuje inda zasu fara girkin,  kallon cikin gidan take har yanzu bata yadda cewar a duniya take ba, bayan gida aka kaisu da manyan itace akace ta hura wuta, kiciniyar haɗa bakin itace ta fara, bata iya ba da kyar ta haɗa, bayan ta hura wutan hayaki ya fara damun idonta harda hawaye, saura suna yanka kayan miya saura suna kula da wuta.

Anwar yana zaune a wani ƙayataccen palour wanda akayi ado da kayan sarauta kamar da gold aka yisu, kafafunshi ya ɗaura kan wani tsadadden centre table, jikinshi sanye da riga da wando na shan iska, ac tare da fanka duk suna hura fatar jikinshi, gefe guda bowl ne cike da kayan fruits, sannan wani tsadadden drink wanda aka tsiyaya rabi a cikin glass cup dake gefe, a hankali yake sipping yana bawa little noor itama a baki tana sha, baki ta buɗe zatayi magana yace "not now sai zuwa anjima yanzu am so tired"
baki ta turo irin na yaranta tace "dady I want to ask you question faa"
girgiza kai yayi yana mika mata cup na hannunshi, karɓa tayi tasha kana tayi shiru tana kallonshi, so take ta tambayeshi meyasa mom nata take zaune a cikin masu aikin gidan? amma yaki bata dama tayi mishi tambayan, mami ce ta fito hannunta rike da katon takadda da biro, sanye take da wani tsadadden yadi wanda yake sheƙi anyi ɗinkin buba, ta fito kamar balarabiya, wuyanta da hannunta sarkan gold ne kana gani ka san ba kananan gold bane, zama tayi a gefen anwar tace "noor jeki samu su unty feenah zamuyi magana da dadynki"
maƙe kafaɗa tayi "mami ba zanje ko ina ba, meyasa momy na take zaune a wajensu unty meerah?"
girgiza kai tayi anwar daya tsani yaji tace momynta ya kalleta ranshi a ɓace yace "wa ya gaya miki itace mom naki? your mom is d..."
hannu mami tasa a bai alaman yayi shiru, ɗauke kai yayi yana cizan leɓe, ranshi kamar wuta, daurewa yakeyi yana maida hawaye badan haka ba babu abinda zai hanashi kuka a wannan lokacin, mami tace "oya tashi kije wajensu unty feenah"
tashi tayi da gudu ta wuce ciki, mami ta kalleshi taga bayama kallonta ya ɗauke kai, gyaran murya tayi kana tace "your brother is coming today"
juyowa yayi da mamaki yace "Allah?"
giɗa kai tayi nan ya fara dariya yace "mami da gaske zai zo?"
"na taɓa maka karya?"
girgiza kai yayi fuskanshi ya kasa ɓoye farin cikin da yake ciki, a take ya saki jiki da mami, ta kalleshi tace "anwar ga wannan takaddan kayi sign"
karɓa yayi yana kallo, ganin sunan Abdullahi Makama ɓaro-ɓaro a jikin ya mika mata a take farin cikin fuskarshi ya kau, sauka kasa tayi tazo kusa da kafanshi tana shirin rike kafarshi ta rokeshi ya rike hannunta "what are you doing Mami?"
idonta cike da hawaye tace "he's your father bai kamata kana haka ba"
girgiza kai yayi "mami kibar wannan maganan banaso ana famemin ciwon daya jima bai tashi ba, dan Allah ki bari"
da sauri ta tashi ganin Khairat ta shigo ɗakin, da mamaki ta kalli mami wacce take ɓoye hawayen daya zubo mata sannan ta taɓe baki ta karaso wajen anwar, zama tayi a hannun kujeran da yake, hannayenta biyu tasa ta dafa kafaɗarshi, riga da wando ne a jikinta irin me laushi da tsantsi ɗin nan, sai gashinta da tayi parking nashi babu ɗankwali ta fito, cike da kissa tace "ya anwar kanajin yunwa?"
hannunshi yasa ya cire nata daga shoulder ɗinshi kana yace "no"
kokarin tashi yake tasa hannu ta maidashi inda yake, fuskanta ta matso dashi ta haɗa da nashi, murya kasa-kasa tace "i miss you so much"
hannu yasa ya ɗan ture face nata daga nashi, gefe ya kalla ya ɗau wayanshi yace "I have alot to do"
tashi yayi zai tafi da sauri ta mike ta shari gabanshi, kallon sama da kasa yayi mata kana ya raɓa gefe zai wuce, hannu tasa ta riko hannunshi, ta baya ta rungumeshi cikin sanyin murya tace "abinda za kayi ya fini muhimmanci?"
tureta yayi ya wuce ya barta a wajen, mami tana ganin ya tafi ta mike zata tafi itama, muryan khairat taji tana cewa "duk wulakancin da yakemin bakya magana saide ki mike ki tafi, ko bakya so saiya aureni"
murmushi mami tayi "khairat kenan ni ban hanashi aurenki ba gaki gashi"
wucewa tayi ta barta tsaye a wajen tana cika tana batsewa, anwar ɗakin jameel yaje, aje wayanshi yayi akan gado yana kallon yadda jameel ya shirya kayanshi jira kawai yake lokaci yayi ya tafi, kallonshi yayi yaga yana bacci, "jameel? jameel?"
buɗe ido yayi ganin anwar ne a gefenshi ya tashi da sauri ya sauka kasa, cikin girmamawa yace "na'am?"
dariya anwar yayi sosai kana ya mika mishi hannu yace "tashi dan Allah"
girgiza kai jameel yayi yace "bazan iya ba, Anwar meyasa baka nuna min matsayinka da ɗaukakan da Allah ya baka ba?"
"matsayi ɗaukaka duk anan duniya ne jameel dan Allah ka tashi, kaji abokina?"
tashi yayi ya ɗan rusuna yaki yadda ya tsaya daidai da dashi, murmushi anwar yayi shine abinda bayaso yafison samun aboki wanda zasu zauna kamar ƴan uwa, gefenshi ya nunawa jameel bayan ya zauna yace "zauna muna da magana"
zama a kasa jameel yayi, shima ya sauko daga gadon ya zauna a kasa, kallonshi jameel yayi yana mamakin sauƙin kai irin nashi, murmushi yayi wanda yake karawa fuskanshi kyau da kwarjini, cikin sanyin murya da rashin son magana da hayaniya yace "jameel naga ka shirya kayan ka kanada niyan tafiya gobe ko?"
giɗa kai yayi
"meyasa kake son tafiya?"
"saboda kai ba sa'an abota dani bane"
"hmm niba mutum bane?"
"kai mutum ne amma Allah ya maka baiwa ya baka kyaun hali da dukiya"
"to inaso kayi amfani da kyawun hali na ka zauna kusa dani so nake ka samu umma da Abba kace kaine ka siya musu gida anan kanaso ku dawo nan da zama"
waya ya buɗe ya nuna mishi hoton wani kerarren gida yace "ga gidan dana siya muku a ciki zaku zauna"
hawaye ne ya cika idon jameel girgiza kai ya fara, zaiyi magana anwar yace "banason musu, auren fatima ma anan gidan nakeso kuyi"
kuka ya fashe dashi baisan lokacin daya rungume anwar ba, cikin kuka yace "hakika wani abokin yafi ɗan uwa, kai ɗan uwana ne ba aboki ba"
saida yayi kuka sosai anwar bai hanashi ba, bayan ya gama kukan anwar yace "yau kanina zai zo zanso ka haɗu da mutumin da nafi kauna duk duniya, a rayuwa banason abinda zai taɓamin shi, ina sonshi sosai, idan mutum yanaso yaga raina ya ɓaci to ya ɓata ranshi, idan kanaso ka ganni cikin farin ciki to ka faranta mishi"
jameel yace "dama kana da kani?"
giɗa kai yayi "kwarai kuwa kanina abin alfahari na"
"to Allah ya kawoshi lafiya zanso ganinshi nima"
hira suka fara harda zancen nas wanda yake karatunshi acan egypt.

HAƘƘI NAWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu