chapter 19

72 4 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
  *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_Jiddah S Mapi_

*Chapter 19*

_Mun kara yawan free pages, ya zama book 1 shine free book2 kuma paid ne, hajiya ki biya kuɗinki ki karanta littafin hakki na daga farko har karshe, yanzu fa muka fara domin akwai cakwakiya, Naira 300 ne kacal, wanda suka shirya biya kafin mu gama book 1 sumin magana kai tsaye 08144818849_

             ~Kamar kullum yauma noor tana ɗaki tayi crossing leg tana shan icecream, hannunta rike da waya tana chatting a group ita dasu  anee, wani material me laushin gaske ne a jikinta baki da ratsin ja, ba karamin kyau tayi ba fuskanta sai glowing yake, wayan ta matso dashi daidai kan small pink lips nata, cikin nutsuwa sa yanga da iya magana ta fara voice tana basu labarin marin data yiwa wata malama a school yau, tana cikin yin voice taji an turo kofa, a hankali ta ɗago manyan idanunta ta kalleshi, kallo ɗaya ta mishi kana ta watsar taci gaba da voice nata, a jikin kofan ya jingina ya zuba mata ido yana kallonta, kamar akwai abinda yake nazari a tare da ita, lips nashi na kasa yasa cikin baki yana tsotsa a hankali, gaba ɗaya hankalinshi a tashe yake tunda Abba ya kirashi yau a waya, sexy eye's nashi ya lumshe a hankali ya kuma buɗewa kamar me jin bacci, ido huɗu sukayi da sauri ta sauke kai kasa, gabanta ne ya faɗi ganin wani kwarjini da yanayi na musamman a cikin idanunshi, ganin bata katse voice ɗin ba yace "ki kashe zamuyi magana"
harara ta watsa mishi, da gayya ta kuma kawo wani labarin tana cigaba da basu tana dariya, ganin ba zata katse ba yace "Abba yana nemanmu da gaggawa"
wayan sake hannunta ne ya suɓuce ya faɗi kasa jin abinda ya faɗa, da mamaki ya kalleta itama kallonshi take tana kokarin ɓoye tsoron da take ciki, cikin voice nashi me daɗin sauraro yace "meyasa kika tsorata kamar baki da gaskiya?"
dakewa tayi tace "kaine kayi kama da marasa gaskiya not me"
murmushin gefen baki yayi kana yace "Abba yace muje a tare"
bata kulashi ba ta dau wayan ta shige bedroom, rufe kofan tayi ta goya hannayenta duka biyu a baya ta fara safa da marwa a cikin ɗakin, "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Allah yasa Abba bai gano komai ba"

zufa ne ya fara ƙeto mata yana jika kyakkyawan fuskanta, a hankali tasa hannu ta share tana cigaba da zagaye ɗakin a mugun tsorace, saida taji yace "ki shirya ki fito" kafin ta daure ta tura kofan toilet ta shiga, cire kayan jikinta tayi kana ta kunna ruwan sanyi ta zauna tana jin yadda yake ratsa jikinta, runtse ido tayi tana tuna abinda ta yiwa ƴar uwarta abar kaunarta haneefa, da sauri ta tashi ta ɗaura towel, gaban madubi taje ta zubawa kanta ido tana kallon cikin idonta ta cikin madubin, gashin kanta da yake a jike ta maida baya, ta cikin madubi taga haneefa tana mata magana, ja baya tayi da sauri, murmushi take mata tana cewa "kije ki gayawa Abba abinda kikamin"
runtse ido tayi da sauri ta juya zata fita taji an tura kofan cikin wani irin murya me tsoratarwa tace "kin kashe ni, ba zan barki ko zauna da anwar nawa ba, ba zan taɓa barinki ba noor"
ihu tayi ta koma baya ta jingina da bangon toilet ɗin, tanajin sanyin tyles yana ratsa ta sosai, jikinta ne ya fara ɓari.

Anwar da shogowanshi kenan yaji ihu, yayi shiri cikin manyan kaya yadi ne me taushi sai ƙamshin turare yake, tura kofan yayi yaji a kulle, da sauri yaje ya buɗe drower ya ciro spare key yazo ya buɗe, shiga yayi yaga bata bedroom kallon kofan toilet yayi da alama tana ciki, wani ihun ta kuma yi, da gudu ya karasa wajen ya tura kofan ya shiga, zuwa lokacin jikinta yana ɓari sosai ta zame kasa ta zauna ta taƙure waje ɗaya, kallonta yayi na tsawon 3mins yana mamakin abinda yasa ta tsorata, a hankali ya karasa inda take ya mika mata hannu, da sauri tasa hannu a nashi ta mike, ba zato yaji ta faɗa jikinshi ta kankameshi, cikin kuka tace "ka fita dani, ka fita dani please"
riketa yayi yana janyeta daga jikinshi, ba karamin riko tayi mishi ba, ganin haka yasa anwar ya fara janta zuwa waje, saida ya isa bakin gado da ita ya fara janyeta, wani kyakkyawan riko ta kuma yimishi, izuwa yanzu gangan jikinshi da ruhinshi sun fara amsa rikon da tayi mishi, kirjinta ta manna da nashi, a tsorace tace "Please don't go"
tattaro nutsuwa yayi da kyar yace "ba zan fita ba, sakeni kisa kaya abba na jiranmu"
sakinshi tayi kanta kasa tace "dan Allah kada ka fita"
zama yayi a bakin gadon, ganin haka ta juya taje gaban mirror ta fara shafa mai, a gaggauce take yin komai, koda ta gama ta gyara gashinta ta kame waje ɗaya da ribbon, wajen wardrobe taje tana duba kayan da zata sa, idonta ya sauka akan wani dogon riga purple wanda yasha stone work, cirowa tayi ta buɗe zip ɗin, pant tasa da bra irin me faɗin nan, duk purple ne, sauke towel ɗin tayi kasa tana shirin sa rigan, daidai lokacin Anwar ya ɗago kai daga danna wayanshi da yake "subhanallah"
shine kalman daya fito daga bakinshi ba tareda ya shirya ba, ganin bayanta da yake a waje gaba ɗaya daga ita sai pant da bra, zai ɗauke Ido ta juyo fuska a shagwaɓe domin zip ɗin ya fashe, kasa ɗauke ido yayi daga kanta musamman kirjinta da yake a cike fam, gashi fari sol kamar baturiya, har yanzu da tsoro a tare da ita ta shagwaɓe fuska tace "zip ɗin ya ɓaci"
baiji me take faɗi ba domin hankalinshi duka ya maida kan kirjinta, ganin bai mata magana ba sai kallonta yake, tsaki taja kaɗan tayi zaton ko shareta yayi kawai dan itama tana mishi shiru idan yana mata magana, ɗauke kai yayi ganin ta juya tana sa rigan, saida tasa kafin tazo gabanshi ta tsaya tareda juya baya tace "ka janyemin zip din ɗin"
a hankali yasa hannu yana jan zip ɗin, idonshi ya zuba akan gadon bayanta wanda yake sheƙi, Allah yayi halitta anan, ganin zip ɗin ba zai janyu ba da alama ya ɓaci, ji tayi kafafuwanta sun gaji da tsayuwa dama a durkushe take, yana shirin ce mata ta canja kaya tasa wani yaji ta zauna akan cinyarshi, kallonta yayi mamaki ya kasa ɗauke wa akan fuskanshi, wannan yarinyar ta ɗauka kowa ne zata rinƙa zama akanshi?
"ka janye min bazan canja kaya ba shi zansa fa"
baiyi magana ba ya fara kokarin jan zip din, a hankali ya kai bakinshi bayanta, saukewa yayi akan zip din ya janye sama "shikenan"
tashi tayi ɗau mayafi kawai tasa akanta, agogon hannunshi ya kalla yace "ɗankwali fa?"
"ban iya ɗaurawa ba unty haneefa ke ɗauramin"
jikinshi ne yayi sanyi jin ta kira sunan haneefa, mutuwan haneefa ya matukar taɓa ta, jaka ta ɗauko yaje wajen wardrobe ya ciro ɗankwalin, hannunta ya riko tana kallonshi baki a buɗe yaje gaban mirror da ita, zaunar da ita yayi akan stool ya tsaya a bayanta, ware ɗankwalin yayi yasa hannu ya zame mayafin data sa, ɗaura mata ya fara, tana kallonshi ta cikin madubi,  yadda ya bada himma kamar wanda ya kware a wajen ɗauri, matso da fuskanshi yayi zuwa nata Duk cikin yanayin ɗaurin ne, lumshe ido tayi jin sajenshi yana shafan gefen fuskarta, bata buɗe ido ba saida taji ya cire hannunshi daga kanta, a hankali ta fara buɗe ido, wani irin murmushi ne ya suɓuce mata wanda ya bayyana fararen kyawawan hakoranta, saida dimple nata ya motsa, ganin wani irin ɗauri da yayi mata, ba karamin kyau tayi ba, kamar wani me aiki a shagon saloon haka yayi ɗaurin, kallonta yake shima ta cikin madubin, ɗaurin ya mata kyau sosai, ɗagowa tayi ta kalleshi ya lumshe ido, haneefa ta gani a bayanshi ta rungumeshi tana shafa fuskanta a nashi, buɗe ido tayi ta kalli noor da wani irin idanu masu tsoratarwa tace "anwar nawa ne ba zan taɓa bari ki zauna kusa dashi ba"
a tsorace ta mike ta tureshi ta bar ɗakin, kallon agogon yayi kana yaja kofan shima ya fita, tana tsaye a kofa ta naɗe hannu a kirji tana tunani, fitowa yayi yana rufe kofan, kallo ɗaya ya mata ya watsar, saida ya gama rufewa yayi gaba, bin bayanshi tayi tana kallonshi, ɗakin inna ya shiga yace "inna saimun dawo"
da murmushi a fuskarta ta fito ta kalli noor wacce tayi kyau sosai tace "noor zaku fita?"
giɗa kai tayi tana ciro glass daga jakanta, inna tace "ku dawo lafiya"
giɗa kai tayi, sa glass ɗin tayi kana ta ciro cingum ta jefa a bakinta, yayi gaba ta kalli inna da mamakin inna taji tace "inna nayi kyau?"
giɗa kai tayi "kinyi kyau amma ki cire cingum ɗin ko ƴata?"
tufar da cingum ɗin tayi kana taci gaba da tafiya, murmushi inna tayi, ta lura akwai tsantsan yaranta a tareda noor, koda ta fita taga yana zaune akan mashin nashi, zaro ido tayi "ba dai anan zasu gida ba?"
ganin ta fito ya kunna mashin ɗin, tsayawa tayi a inda take, yayi mata alama tazo, make kafaɗa tayi kamar zatayi kuka, agogo ya nuna mata alaman lokaci yana tafiya, wayanta taji yana ruri ganin numbern abba ne yasa taje da sauri ta hau mashin ɗin, bata amsa ba dan tasan zatasha faɗa, jan mashin din yayi a tsorace ta rikeshi gam ji take kamar zata faɗi, tafiya yake a nutse jin yadda ta rikeshi ya gane tsoro take sosai, hakan yasa baya tafiya da gudu, saida suka hau kwalta ya fara gudu, matsowa tayi sosai ta rungumeshi da iya karfinta, addu'a takeyi a ranta, kallon yatsunta da suka fito ta cikinshi yayi, cikin rashin magana sosai yace "ki saki jiki kada ki faɗi"
ai jin yace zata faɗi yasa ta kara rikeshi kamar zata shiga jikinshi, da kyar suka isa gida, a bakin kofa ta sauka tana hamdala, sa space nata tayi getman ya buɗe mata kofa, shiga tayi tana taku ɗai ɗai.

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now