Chapter 20

74 4 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
  *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_Jiddah S Mapi_

*Chapter 20*

             ~Shiru yau ta wuni a gidan anwar kuma sun fita da faruk sai kusan mangrib suka dawo, alwala sukayi sannan suka idar da salla a masallacin Abba dake kofar gida, bayan sun idar suka shigo ciki anwar zama yayi a kan kujeran dake bakin kofa gefen sani suka cigaba da hira, faruk bayan ya shiga ya kuma fitowa yana yiwa anwar magana, a tare suka shiga ciki, dama shi jira kawai yake noor ta shirya ta fito su tafi, saide yana jin nauyin kiranta, shiga ciki sukayi momy tace "haka zaku tafi bakuci abinci ba?"
"momy ki bari kawai zamuje restaurant"
girgiza kai tayi "ka zauna dai tunda time yaja"
ba dan yaso ba ya zauna a gefen Faruk kan kujeran dining, cikin tafiya kamar sarauniya haka take taka stair ɗin tana kallon wayan hannunta, da haka har ta karaso inda suke, riga da wando tasa domin atamfan ya dameta da zafi, kallonta yayi a ranshi yace "ba zata iya zama da kayan arziki ba dama"
momy ce tayi serving nasu da coconut rice wanda yaji kayan lambu, itama noor zubawa tayi akan plate, shiru tayi tana juya cokalin a kan plate din, gaba ɗaya ta kasa nutsuwa wannan camera da suke magana akai takeson gani, a hankali yake cin abincin ganin bataci ko sau ɗaya ba ya ɗago yana kallonta, tayi nisa cikin tunani, kallon kafarta yayi wanda yake kusa da nashi, a hankali yasa yatsunshi akan nata, shafawa yayi ta ɗago tana kallonshi, ɗaga mata gira ɗaya yayi alaman meyake damunta?
girgiza kai kawai tayi ta ɗibo abincin a spoon ta kai bakinta, kallon yadda take taunawa cikin nutsuwa yake, saida yaga ta maida hankali tana ci kafin shima yaci gaba da ci, bai wani ci sosai ba yace "Alhamdulillah"
faruk da yake kallonsu ta kasan ido yace "ba dai ka koshi ba?"
giɗa kai yayi "na koshi"
itama goge baki tayi da tissue tace "momy am okay"
tashi tayi ta gyara mayafin jikinta ta ɗau jakanta tace "let's go"
sallama ya yiwa faruk da momy, envilope ɗin faruk ya bashi yace "ka kula sosai"
jijjiga kai yayi, tunda ta ɗaura manyan idonta akan envilope ɗin bata ɗauke ba, tunani take ta yadda zata ɓatar da wannan shaidan, daidai bakin kofar fita tasa yatsunta a nashi, yana mamakin yadda take canjawa kamar hawainiya, bata rike hannunshi duka ba amma yatsunta yana cikin nashi, a hankali take murza babban yatsanta akan nashi, faruk yana kallon su yaji sanyi a ranshi, saide yaji wani zafi kaɗan domin yaso haneefa ce take tare da anwar, time da zasu hau mashin ya mika mata yace "rikemin"
da sauri ta karba, koda ya hau mashin ɗin itama ta hau, yayi mamakin yadda bata tsorata sosai ba yanzu domin bata rikeshi ba, buɗe envilope ɗin tayi tana kallon abin ciki, da mamaki taga wani (card reader) gidan memory, tanada tabbacin a ciki cameran yake, da sauri ta mayar, bayan sun isa gida ta sauka ta shiga ciki, inna tana ɗakinta, wucewa tayi zuwa room nata, ta cire mayafin nan ta fara safa da marwa tana tunanin ta inda zata ɓullowa lamarin, murmushin gefen baki tayi kana ta wuce toilet tayi wanka, shafa mai mai kamshi da turare mai kamshi tayi, wani wando gajere wanda ya tsaya a cinyanta tasa, santala santalan kafafunta a waje sai sheƙi suke kamar ta shafa musu massage oil, top baki tasa wanda yake da tsagu a hannun, farin fatanta ya fito sosai kamar ka sace ka gudu, parking gashinta tayi da bakin ribbon, zama tayi a bakin gadon wayanta a hannunta tana jujjuyawa.

ɓangaren anwar saida ya aje mashin ɗin a mazaunin shi, ya shiga ciki domin duba inna, tana bacci, murmushi yayi ya shiga cikin ɗakin ya canja kaya zuwa wani jallabiya blue black me kyau, turare ya fesa kana ya ɗau envilope ɗin ya wuce ɗakin da yake kwana, da sallama a bakinshi ya shiga ganin bata falo yasashi ɗauko laptop nashi ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin, kafanshi ya ɗaura akan centre table ɗin sannan ya ɗaura laptop akan kafarshi, buɗewa yayi ya ciro card reader ya fara kokarin sawa a cikin laptop, a hankali take tafiya kamar wacce take tsoron wani abu, koda ta ganshi a falo bata kulashi ba ta nufi hanyan fita, kallonta yayi da mamakin haka zata fita da wannan dressing ɗin? da alama sa kaya kanana da bayyana sura bai dameta ba, idan inna ta ganta fa? koda shike dama batada kunya, buɗe kofan tayi, koda taga baya kallonta ta buga da kanta, ihu tayi tana rike da goshinta wanda ya fara jini, aje laptop ɗin yayi yana cewa "meya faru?"
ido ta rufe tana mika hannu alaman ya riketa ta bugu, jinin ya fara sauka kan idonta, tashi yayi zaije gabanta nan ta zube kasa, da karfi tace "wayyo Allah kafata wayyo Allah"
da ɗan gudu ya karasa wajenta yana riketa.

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now