chapter 14

37 3 0
                                    

*HAƘƘI NA*

By
_jiddah S Mapi_

14.

                ~Jin karan faɗuwa sukayi a tare suka fito daga ɗakin, momy ce tayi salati ganin noor kwance kasa idanu a rufe, hannu ta aza akai ta tsala ihu "na shiga uku itama noor ta mutu na shiga uku Alhaji"
share zufan dake fuskanshi yayi a hankali yasa hannu ya ɗaga ta, ɗaki ya shiga da ita ya kwantar akan kujera, momy ce ta ɗauko ruwa aka shafa mata a fuska, a hankali ta buɗe ido bakinta yana motsi da alama magana take, momy ta kai kunnenta wajen bakinta bataji komai ba kuma har yanzu bakin noor bai daina motsi ba, a ɓangarenta cewa take "meyasa? meyasa kuka auramin shi? da wanne zanji? da mutuwan haneefa ko auren wannan?"
waya Abba ya ɗaga ya kira layin Dr rukayya itace take kula dasu idan basuda lafiya, kiran gaggawa ya mata, cikin kankanin lokaci tazo, duba noor tayi tasa mata drip tareda alluran bacci sannan ta wanke ciwukan da taji lokacin da take gudu zata dawo gida, momy kam tana tsaye in tears, tausayin kanta da ƴarta take, a hankali ta rufe idonta bacci ya ɗauketa, momy ta zauna a gefe tana rera kuka, Abba yace "kije kiyi kuka a waje saboda kada ta tashi"
ko kallonshi batayi ba saima kara sautin kuka da tayi.

anwar jameel ne yazo hankalinshi a tashe, rikeshi yayi suka fita zuwa waje, Dr yace "ku dawo bamu sallameku ba"
Daga inna har anwar har jameel babu wanda ya kalleshi, a tare suka fita zuwa kofan hospital ɗin taxi suka tara, anwar hawaye ya kasa tsayawa a idonshi, zama yayi a baya jameel da driver a gaba, bini-bini yana share hawaye hannunshi a haɓa, inna ma tana cikin tashin hankali barinshi tayi batayi mishi magana ba, har suka isa kofan gidansu haneefa saida sukeje driver yayi parking Anwar ya kasa cire kafanshi daga motan ganin dandazon mutane a kofan gidan, kuka ya kara fashewa dashi jameel ne ya zagayo ya buɗe marfin motan, kallonshi yayi shima idonshi yana cika da hawaye, sharewa yayi ya durkusa gabanshi cikin sanyin murya yace "abokina? dan Allah kayi hakuri ka rungumi ƙaddara, babu wanda yafi karfin ƙaddara ka daure zuciya ka fito muje dan Allah, ko so kake muma muyi kuka ne?"
tashi yayi daga kan kujeran motan ya rungume jameel, wani irin ɗan marayan kuka ya fashe dashi yace "haneefa ta nunamin so wanda duk duniya babu wacce ta taɓa nunamin irinshi, ku maidani gida ba zan iya ƙarasawa ba, jameel zuciyata zata fashe"
bayanshi jameel ya bubbuga yace "sorry ka daina kuka ka daure mu karasa Allah yana ganin komai"
da kyar shida inna suka rike hannunshi suka karasa wajen mutanen dasu, a time ɗin Abba ya fito jikinshi a mace kana ganinshi kasan yana cikin damuwa, ganin inna dasu anwar yaje ya yiwa inna iso har cikin gidan, a ɗaki me kyau ta zauna kana ya dawo ya samu anwar wanda ya zauna ya haɗa kanshi da bango yana rera kuka, hannu yasa ya dafashi kana yace "anwar hakuri zamuyi haneefa ta tafi kuka ba zai amfaneta da komai ba, addu'a take bukata, mu kuma neman wanda ya aikata wannan aika-aikan zamuyi yanzu ba wai kuka ba"
ɗagowa yayi idanunshi sunyi jajur, bakinshi yana rawa yace "Abbaaa.."
cigaba yayi da kuka ya kasa magana, Abba ma hannu yasa yana share hawaye, mutanen wajen kowa saida yayi hawaye, masu taron biki sun koma taron mutuwa, cikin gidan shiru babu me magana, Yah faruk yana gefe yayi tagumi hawaye yana wanke mishi fuska.

momy tana zaune a gefen noor bataci komai ba har dare ya tsala, duk yadda akayi da ita taci abu taki yadda ko ruwa tasha, bata taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba, kusan karfe 3 na dare noor ta fara buɗe ido a hankali tana kallon cikin ɗakin, kallon hannunta tayi an cire drip ɗin, a hankali ta mike tana cije baki ta zauna tana kallon momy wacce ta zuba mata ido, hawaye taji yana sauka daga idonta cikin sanyin murya tace "da gaske unty haneefa ta mutu?"
jijjiga kai momy tayi "kwarai ta mutu noor"
ido ta fara lumshewa alaman zata kara suma, hannu momy tasa ta riketa cikin kuka tace "dan Allah noor kada kiyi haka, ki rufamin asiri kar kibi haneefa idan kin mutu nima kashe kaina zanyi wallahi"
zama tayi tana nishi sama sama, momy tace "ban san wani mugun ne ya kashemin haneefa ba, me mukayi mishi? wani laifi muka musu da zasu saka mana da wannan ɗanyen hukuncin? Allah ya isa, Allah ya isa ban yafe ba.." dogayen hannunta masu ɗauke da ja da bakin kunshi
tasa ta toshe bakin momy, girgiza mata kai tayi "dan Allah momy kada kisa zuciyata ta tarwatse, ki daina furta wannnan kalman idan baso kike nima ki rasani ba"
cire hannun tayi tace "me kike nufi noor? kada nayi Allah ya isa ga wanda ya kashemin yarinya?"
girgiza kai tayi hawaye yana cigaba da wanke mata fuska "momy kiyi shiru dan Allah"
kuka ta fashe dashi, momy tasa hannu ta janyota jiki, ji take kamar ta gayawa momy abinda ya faru amma tana tsoron abinda zai biyo baya, kada su tsine mata tabi duniya, noor bata taɓa dana sanin abinda takeyi ba sai yau, tana kwance a jikin momy kanta yayi nauyi bakinta ma haka, ba abinda yake tsaya mata a rai kamar idan ta tuna itace sanadin mutuwan haneefa sai wani sabon kukan ya kwace mata.

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now