chapter 8

37 5 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
    *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_jiddah S Mapi_

*Chapter 8*

              ~hannu tasa tana ɗagoshi ya cije baki ya daure ya mike, idonta ya cika da hawaye tasa hannu tana share mishi jikinshi daya ɗan ɓaci da ƙura, jin hawaye ya ɗiga a kafanshi ya ɗago fuskanta yana kallonta, kuka ta fashe dashi lips nata yana rawa, kallon yadda take kuka yayi, duk wani yanayi kyau yake mata, a hankali yasa hannu yana share mata hawayen, ganin tana kara sauko da wasu yace "shiiii ki daina kuka shikenan"
cikin kuka tace "kayi hakuri"
"ba komai bakiji ciwo ba?"
girgiza kai tayi, yace "yawwa to ki daina kuka"
a hankali tace "kaji ciwo ko?"
girgiza mata kai yayi "bayana ne kawai ya ɗan bugu"
"sannu"
janshi da hira tayi tana bashi hakuri, yace "ba komai" har ta rakashi ya hau mashin nashi tana ɗaga mishi hannu har ya tafi, komawa ciki tayi ta samu megadi tace "motan waye wanda ya fita yanzu?"
"a ciki aka kawo amarya"
jijjiga kai tayi kana ta koma ciki, neman noor ta fara taga bata nan, yah faruk kawai ta gani suna zaune da abokanshi suna hira, elham ma ta zama busy tana hira da mijinta, gefe ta samu ta zauna tayi tagumi, waye yayi musu wannan abin? tuna lokacin data faɗa kanshi tayi, a hankali ta runtse ido tana kallonshi yana cije leɓe, "koma wanene yayi wannan abin ya kara kusantani ne dashi"
da sauri ta bigi bakinta, tunawa da rashin kyaun abin a addini, noor ce ta shigo fuska ba yabo ba fallasa hannunta rike da katon flask tana tafiya kamar zata tashi sama, a cike take ba abinda take gani idan ta rufe ido kamar haneefa da wannan me raken, ji take kamar ta ɗaura hannu aka ta tsala ihu, murmushin jin daɗi haneefa tayi ganin noor ta shigo, buɗe flask ɗin tayi ta fara rarraba snacks ɗin akan.duk wani plate data gani empty, yah faruk ya lura da yanayinta sharewa yayi watakila ƴan rashin kunyan nata ne suka motso, saida ta gama rabawa ta bawa wata flask ɗin ta kai mota, zama tayi a gefe tana kallon mutanen wajen, da akwai abinsha wanda zai bugar da ita ya cireta daga wannan tunanin da ba abinda zai hanata sha, haneefa ta taso a hankali ta karaso inda take, dafata tayi tace "ina kikaje?"
ba tareda ta juyo ba tace "naje ɗauko sako"
"okay"
tashi tayi a wurin har aka gama dinner kusan karfe 11 kafin suka fito da yan faruk, ya rike hannayensu su duka, mota sukaje noor ce a gaba yanzu, ita kuma haneefa a baya, ta kwanta ta fara jin bacci, kallon noor yayi wacce take cika tana batsewa, hannu yasa akan goran dake gefenshi ya mika mata, karɓa tayi ta buɗe ta ɗaura a bakinta, fita sukayi daga wurin, ta shanye ruwan tass kana ta rike goran a hannunta ta murza da karfi, saida ta lanƙwasa kafin ta rike da karfi tana kallon titi, wannan yaron zata koya mishi hankali, ko hanyan da haneefa tabi ba zai kara yadda yabi ba.

yah faruk yasa hannu ya karɓe goran ya sauke glass ya wurgar, hannu yasa ya buɗe wani bowl ya ciro chocolate babba ya mika mata, karɓa tayi ta ɓare ta cinye duka kana ta yasar da ledan, murmushi yayi kana ya mika mata tissue ta karɓa ta goge bakinta da hannunta, ganin har yanzu bata runtsa ba ya ciro wayanshi ya shiga game ya mika mata, karɓa tayi ta fara game ɗin, saide tanata faɗuwa dan tunaninta baya nan, itafa idan ranta ya ɓaci sai tasha syrup take sauka, amma duk abinda za'ai mata ba zaisa ta sauko ba.

karɓan wayan yayi ya kashe kana yace "noory?"
"na'am"
"meya faru?"
ji tayi kamar ta sanar mishi abinda ke faruwa sai kuma tace "ba komai"
kallonta yayi sannan ya maida hankali kan titi yace "waya taɓaki?"
kuka ta fashe dashi, ya san akwai abinda yake damunta, hannu yasa ya janyota jikinshi yana cigaba da tuƙi yace "it's okay"
bubbuga bayanta yake kaɗan kaɗan har itama tayi bacci kamar yadda haneefa ma tayi, a hankali ya juya ya kalli haneefa kana ya kalli noor ɗin, bayan Abba da momy babu wanda yakeso a duniya kamar noor da haneefa, Allah yaci gaba da kare mishi kannenshi ameen, har suka isa gida aka buɗe musu get suka shiga, a compound yayi parking kana ya juyo yana taping haneefa "ke haneefa tashi"
tashi tayi tana murza ido yace "munzo gida"
buɗe motan tayi ta fita ba tareda ta ɗau jakanta ba dan yanzu 11:30 ana neman karfe sha biyu, "noory noory? tashi"
mika tayi kamar zata tashi sai kuma taci gaba da baccinta, tsaki yaja shiyasa baiso tayi bacci ai saika ɗauke ta, kallon haneefa yayi wacce take tafiya tana gyangyaɗi yace "ga wayanta rike"
karɓan wayan tayi ya ɗaga noor suka tafi ciki, Abba yana tsaye sai kallon agogo yake, ganin sun shigo ya sauke ajiyan zuciya "tare kuke?"
jijjiga kai yayi "eh Abba"
"meyasa kuka jira dare?"
"wallahi Abba basu gama da wuri bane"
yana magana da noor a hannunshi, "kaita ka kwantar kazo munada magana"
"okay Abba"
wucewa yayi da ita ya kaita har ɗaki, kwantar da ita yayi akan gado itama haneefa ta kwanta, rufasu yayi da blanket ya kashe wutan ɗakin kana ya fita tareda janyo musu kofan ya wuce kasa domin yin magana da Abba.

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now