chapter 26

88 5 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
   *HAƘƘINA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_Jiddah S Mapi_

*Chapter 26*

             ~Jabeer yace "wacece take cewa mom nata?"
tsaki khairat tayi tana hararan noor wacce ta kwantar da kai a kirjin Jabeer tana ɓoye fuskanta, cikin ɓacin rai tace "wata banzan kucaka ta gani wai itace mom nata, I will slap this girl idan ta kara wannan maganan"
hannunshi anwar ya rike yace "let's go in I miss you so much"
"miss you too broh"
kallon jameel yayi yace "my J meet my brother jabeer"
hannu yasa cikin na Jabeer suka gaisa, da muryanshi me sanyi yace "bro kayi sabon aboki ne?"
giɗa kai yayi "kwarai wannan shine sabon abokina sannan ɗayan ya tafi karatu a egypt sunanshi nasir muna cemishi nas"
"ina wuni"
jameel yace "lafiya sannu da hanya"
mami dake tsaye a gefe tana aikin share hawaye tazo wajen tace "jabeer?"
shiru yayi kamar ba zaiyi magana ba, saida ta kara maimata sunan kafin yace "na'am"
hugging nashi tayi da mamakin jameel yaga baiyi respond ba, kuka ta fashe dashi, a hankali ya zame jikinshi daga nata yace "let's go"
Inna tana tsaye a gefe gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, saida zasu wuce ta tace "ba zaka tambayi Hajiya babba ba?"
murmushi yayi yace "hajiya babba tawa, me kika ajemin?"
"babu abinda na aje maka sai duka"
dariya sukayi su duka suka shiga ciki, akan sofa Anwar ya zaunar dashi ya bashi ruwan sanyi da drinks yace "have it"
karɓa yayi ya kasa ɓoye murnan da yake ciki yace "yau ina cikin farin ciki marar misaltuwa Bro"
"nima haka J"
mami suna barin wajen ta wuce ɗakinta, ɗaki ne me kyau sosai ga wani babban gado wanda aka ƙawata da kayan kyale-kyale, kwanciya tayi akan gadon ta fashe da kuka, yi take kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu, turo kofan akayi da sauri ta mike tana goge idonta, kirkiro murmushi tayi tace "Feenah?"
kallonta feenah tayi bata amsa ba kawai ta karaso ciki, ɗaga bayan riganta wanda yake jan kasa tayi ta zauna a gefenta, ido ta zuba mata tana ganin yadda take kokarin ɓoye damuwanta "meya faru feenah?"
"komai ma ya faru mami tunda kika ɓuya kina kuka"
"ba kuka nake ba Ina murnan ganin jabeer ne"
"murna? shine harda kuka mami? i don't know what is happening in this house, kowa kuka kullum kuka, baku iya manta baya ne? nida leemah me kukeso muyi idan ku kuna kuka? mami kinsan ba zan juri ganin hawayenki ba ko?"
giɗa kai tayi tace "insha Allah ba zan kara ba feenah Allah muku albarka"
"Ameen kimin murmushi"
murmushi tayi "that's my mom lets go and have dinner"
tashi tayi suka fita tare, Abba da kanshi ya fito yana zaune akan ɗaya daga cikin kujerun dining gefenshi jabeer ne sai murmushi yake yana bashi labari, mami ta ɗauke kai taje gefen anwar ta zauna, inna ma ta zauna, sai feenah da leemah da kuma little noor, khairat ce tazo daga karshe kujeran dake facing Anwar ta zauna akai tana kallonshi, kowa ya zuba favorite food nashi baka jin komai sai sautin haɗuwan cukola da plate, Anwar ba yadda baiyi da jameel ba ya zauna dasu suci abinci yaki yadda, yace zai bashi privacy da family ɗin shi, anwar ya maida hankali kan abinci yanaci cikin nutsuwa, khairat data zuba mishi ido tana kallonshi ta kalli kasa, kafanshi ta gani tayi murmushi, a hankali ta ɗaura kafanta kan nashi, yatsunta ta fara gogawa akan nashi, janyewa ya fara ta hanashi ta hanyan danna kafarta akan nashi, ɗago ido yayi yana kallonta hannunshi rike da spoon wanda ya ɗibo rice a ciki, murmushi tayi mishi tareda kashe mishi ido ɗaya, ranshi ne ya fara ɓaci da sauri ya janye kafarshi ya tashi a wajen bai tsaya ya koshi bama tsabar yadda ranshi yake tafarfasa, gaba ɗaya suka juya suna kallonshi itama khairat kallonshi tayi, kana ta taɓe baki taci gaba da cin abincin, feenah ta kalli leemah, taɓe baki leema tayi, Jabeer yace "bro Anwar?"
"baya nan yanzu ya tafi"
cewar little noor,
"har ya koshi?"
"no unty khairat ke shafa kafarta a nashi shine yayi fushi ya tafi"
da mamaki khairat take kallon yarinyar, batayi tsammanin ta gansu ba, ashe mugun waye ne da ita sai taga abu sai kuma tayi kamar bata gani ba, Abba ya kalli khairat da take hararan noor, cigaba da cin abinci yayi Jabeer yayi murmushi kawai shima yaci gaba da cin abinci, feenah tana koshi ta mike ta tafi ɗakinsu, wani haɗaɗɗen ɗaki ne, zama tayi akan sofan tayi tagumi, leemah ce ta turo kofan, koda ta shigo turawa tayi ta tsaya jikin kofan ta harɗe hannu a kirji tana kallon feenah, gyaran murya tayi ganin kamar batama san da zuwanta ba, ɗago kai tayi ta kalleta sannan ta maida kai taci gaba da tunani, takowa tayi har zuwa inda take ta zauna a gefe, hannu tasa ta rike na feenah tace "feenah yah Anwar har yau bai dawo hayyacinshi ba, ga khairat ta kasa hakuri ta bashi lokaci tana takura mishi, da wanne zaiji? mutuwan matarshi? wacce yafi sonta fiye da rayuwarshi ma, ko dai takuran da kanwarta take mishi bayan mutuwar ta?"
giɗa kai tayi "tabbas yah Anwar yana jin wannan ciwon har yau a cikin zuciyarshi, amma wani abu yana ɗaure min kai"
"menene abinda yake ɗaure miki kai?"
gyara zama tayi akan kujeran kasaita da take kai, "wannan yarinyar da sukazo tare bata miki kama da...."
"my lovely sister's where are you?"
a tare suka mike sukaje gareshi, Jabeer ne ya shigo dan ance mishi sun tafi ɗaki, hannu ya buɗe musu suka faɗa jikinshi, cikin kulawa yace "i miss you so much"
feenah tace "we miss you too ya jabeer"
sakinsu yayi ya rike hannunsu "muje na baku gift ɗin dana dawo muku dashi"
da murna suka fara binshi jin ance za'a basu gift, ɗakinshi ya kaisu yace su ɗauko babban kwalin dake gefe, ɗaukowa sukayi yace "yawwa ku buɗe"
har suna rige-rige wajen buɗewa, feenah ce ta buɗe, ganin abinda yake ciki ta daka tsalle ta rungumeshi tareda mishi kiss a goshi, leema tace "necklace gold wow"
buɗewa tayi ta ciro daga cikin tsadadden ledan da akayi raping nasu, feenah ta ɗau ɗaya tasa a wuyanta tace "yaya kaga yadda gold ɗin nan yamin kyau?"
dariya yayi "ina zan gani feenah?"
leemah tace "watarana zaka gani yaya"
gwada nata tayi itama tace "amma yaya yanada tsada ko?"
giɗa kai yayi "wannan shine abu mafi tsada dana siya a wannan shekaran ku adana sosai domin kuɗinshi ba karamin kuɗi bane"
"To yaya amma wannan na ledan na waye?"
ɗagawa leemah tayi taga shigen nasu ne amma wannan anyishi kamar design na heart, murmushi yayi yace "wannan na wata ce wacce take da muhimmanci a rayuwata"
buɗewa leemah tayi taga anyi ado me kyau a jiki da love a jiki, kallon feenah tayi suka waro ido a tare, feenah tace "bro ya faɗa love"
giɗa kai yayi yana murmushin da har kasan zuciyarshi, hannunsu ya rike suka zauna, cikin shauƙi yace "babban albishir da nazo muku dashi, shine ma samu wacce nake so, ina matukar sonta har cikin tuciyata, da tunaninta nake bacci dashi nake tashi, zan iya komai akanta"
da sauri leemah tace "harda rabuwa damu?"
giɗa kai yayi "kwarai idan tace batason zama dani a cikin gari zan iya binta daji muje mu zauna"
"bro wani irin soyayya kake mata?"
"ba zaku fahimta ba saikun shiga zuciyata kun gani, wannan sarkan nata ne ku ɓoyemin gobe zan karɓa"
"okay to bro"
"wace yarinya me sa'a ce ta shigo rayuwar kanina wanda baya kula mata baya shiga harkan kowace mace?"
"yah Anwar dama kana jina?"
shima zama yayi a gefenshi yace "kwarai ina jinka, har naji yarinyar ta kwantamin a rai tun ban ganta ba"
"yah Anwar kenan haka take da shiga rai saima ka ganta, wallahi ji nake kamar na cinyeta na huta da azababben soyayyarta dake damun zuciya ta"
shafa gefen fuskanshi yayi "easy mana Bro ya kake irin wannan zazzafan soyayyan? kasan illan da yamin ai ko?"
giɗa kai yayi yace "but yaya i love her, yaya har cikin zuciyata nake jinta"
"karka damu abinda kake so yana tare da kai"
kallon necklace ɗin yayi "umm sunyi kyau kuma tsadaddu ne, feenah ku adana kunji?"
"toh yaya"
fita sukayi suka barsu, kallon Jabeer yayi yace "to sarkin soyayya shirun me kayi?"
murmushi yayi "yah ai ban kaika ba kaide kawai ina iya jure soyayya ne ka ɓoye a ranka amma ni bana iyawa" murmushi kawai anwar yayi suka fara hira na yaushe gamo.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 24, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now