chapter 23

35 4 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
  *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_Jiddah S Mapi_

*Chapter 23*

             ~Har suka isa gida bata daina kuka ba, inna sai hakuri take bata har ta gaji tayi shiru, da mamakin inna taga ta tura kofan ɗakinta ta shiga, anwar kuma ya wuce room nashi, inna ma ta shiga ɗakin, kwance take akan kujera tayi rub da ciki tana kuka kamar ranta zai fita, inna tace "ki daina kuka kada kanki yayi ciwo"
kamar tace ki kara sautin kukan ne, haka taci gaba da kuka har ta gaji wani wahalallen bacci ya ɗauke ta, tagumi inna tayi tana kallonta, tashi tayi ta fita domin duba halinda anwar yake ciki, a hankali ta tura kofan ɗakinta, tayi sallama kusan sau uku bai amsa ba, shiga tayi bata ganshi a falo ba, kai tsaye ta wuce bedroom, yana kwance akan gado yayi watsi da duk kayan ɗakin, kuka yake yi sosai me tsuma zuciyan me saurare, jiki a mace ta karasa, zama tayi a bakin gadon, kanshi ta shafa tace "Anwar ban sanka da raunin zuciya ba"
ɗago kai yayi yana kuka yace "ya zanyi inna? ya zanyi da rayuwa ta? babu abu me daɗi tunda na tashi sai bakin ciki?"
kanshi ya ɗaura akan cinyarta ya lumshe ido tareda mikar da kafanshi akan gadon, hawaye yana sauka a gefen idonshi yace "me nayi ake min wannan hukuncin?"
shafa suman kanshi kawai take tanajin hawayenshi yana jika mata kafa, lumshe ido yayi wasu sabbin hawaye suna kara gangara yace "ki gayamin me nayi?"
"bakayi komai ba, Allah ne yake sonka shiyasa yake maka jarrabawa, bakaji yace zamu jarabci muminai ba?"
giɗa kai yayi kana cikin murya kamar ya fara jin bacci yace "why always me?"
"ka daina faɗin haka kamar saɓo kakeyi, kai jarumi ne shiyasa Allah yake jarabtanka, kuma kai mumini ne,  bakaji Allah yace (man kana yu'uminu billahi wal yaumul akhiri fa yu'uminu bil kadari khairihi wa sharrihi)
duk wanda yayi imani da Allah da rana ta karshe, yayi imani da ƙaddara alkhairi ko sharri, haka kaddaranka yake, kayi addu'a Allah ya haka ikon cinye jarabawa"
"ameen"
ya faɗa cikin muryan bacci daya fara ɗaukanshi, "yawwa anwar na inna, zakaci abinci?"
jin yayi shiru ta leka taga har bacci ya ɗauke shi, kanta ta jingina da jikin gadon, hawaye masu ɗumi suka fara sauka daga idonta zuwa fuskan anwar, a hankali tasa hannu ta share, shafa kwantaccen gashin kanshi tayi kana ta janyeshi tasa mishi pillow, kara gudun fanka tayi zuwa number 5, ta rufashi da blanket sannan ta fita, ɗakinta ta koma inda noor take bacci sosai akan kujeran, kumatunta duk busashen hawaye, hannu tasa ta gyara mata hannunta wanda ya karkace, cire mata mayafin tayi sannan ta rage gudun fanka saboda akwai sanyi kaɗan, alwala taje tayi ta dawo ta shimfiɗa sallaya ta tada salla, cikin sujjada ta kaiwa Allah kukanta, koda ta idar bayan ta gama lazimi ta rinƙa rokon Allah ya kawo mafita da sauki a wannan al'amarin.

fita tayi ta hura wuta ta girka taliya da wake na dare, tana girki tana tunani har ta gama ta zuba a flask biyu, ɗaya ta kai ɗakin anwar ɗaya kuma ta kai ɗakinta, kwanciya tayi itama a kasa nan take bacci a ɗauke ta.
saida aka idar da sallan mangrib noor ta buɗe ido tana kallon cikin ɗakin, turo karamin bakinta tayi tana karewa inna dake bacci kallo, santala santalan kafanta wanda yake fari sol ta sauke zuwa kasa, a hankali ta fita daga ɗakin, ta wuce ɗakinsu, kai tsaye ta shiga ciki, ganin yana bacci ta ɗau pillow tazo kanshi, kokarin danna pillow take, kamar a mafarki yaji mutum a kanshi, tureta yayi da karfi ta faɗi a gefe, kunna wutan yayi yana murza ido, ganinta yayi tana huci tana kallonshi, a zafafe ta mike taje gaban mirror ta ɗau wani kwalban turare, kanshi ta nufa, dirowa yayi daga gadon ya rike hannunta da karfi ya murɗa ya maida baya, ihu tayi "ka sakeni mugu azzalumi"
kin sakinta yayi sai matseta hannunta da yake yi da karfi, cikin kuka tace "kaine kasa komai yake faruwa kaine ka shigo rayuwarmu"
matse hannunta yayi ya matso da bakinshi kusa da ita, "me laifina dan ni talaka? talaka bai dace ya auri ƴar me kuɗi bane? be dace yayi rayuwa ke kyau bane?"

"bai dace ba, kwarya tabi kwarya"
sakin hannunta yayi yace "okay haka kikace kwarya tabi kwarya?"
"kwarai haka nace saika sakeni idan ya maka zafi"
girgiza kai yayi "ba zan sakeki ba, saina rama abinda kika yiwa haneefa"
"miye haɗinka da ita? kai ɗin banza talaka wulakantacce wanda baida komai sai abinda mahaifina ya bashi"

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now