chapter 5

39 3 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
    *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_jiddah S Mapi_

*Chapter 5*

              ~Haneefa cikin jin daɗi tayi bacci ranan, noor kuma sai taping fuskanta take tanason gane bacci take ko idanunta biyu, wannan wani irin zubar da class haneefa tayi? meyasa zata kira shi? na shiga uku, duvet ɗin ta yaye daga kanta ta leƙa fuskan haneefa, gani tayi tana bacci hankali kwance murmushi akan fuskanta, kallon wayan tayi dama tasan password, cirewa tayi ta kalli numbern da tayi waya dashi last, danna block tayi kana ta ajiye wayan ta koma ta kwanta.

Anwar bayan sun gama waya ya kurawa wayan ido yana kallon numbern data kirashi dashi, taɓe baki yayi kana ya aje wayan a gefe baiyi zaton zata kirashi ba, rufe idonshi yayi a hankali bacci ya fara ɗaukanshi, wayan ya kumaji yana ruri, yatsina fuska yayi, idonshi da suka lumshe ya buɗe sannan ya ɗaga yaga sunan Jameel yana yawo a gaban wayan, received ya danna ya kara a kunne.
"saina fara bacci kake kirana me kuma ya faru?"
"kai tashi albishir nazo maka dashi"
tashi yayi daga kwancen da yake ya zauna tareda janyo Pillow ya ɗaura kan kafanshi yace "albishir na me?"
"companyn AY ventures sun fara ɗiban ma'aikata gobe da safe suke bukatan takaddu zasuyi screening"
jijjiga kai yayi "mashs Allah gobe zamuje Allah yasa muna da sa'a, kasan banida burin da ya wuce naga na samu aiki ina kula da inna, koma wani irin aiki ne zanyi"
"na sani ka kwana da niyya gobe saimu je mu jarraba Allah yasa wannan karon ba zamu rasa ba"
"Ameen"
sallama sukayi ya kashe wayan ya kwanta, haƙiƙa yana son aiki idan ya samu ba karamin farin ciki zaiji ba, ya nemi aiki da dama Allah bai bashi ba, kullum yana addu'a Allah ya zaɓa mishi aiki mafi alkhairi.

washe gari bayan ya idar da sallan asuba yana zaune akan sallaya yana azkhar kamar yadda ya saba, jallabiya ne a jikinshi ruwan kasa, saida gari yayi haske sannan ya mike ya ninke sallayan, jallabiyan ya cire sannan ya ɗaura towel babba a ƙugunshi, toilet nashi madaidaici wanda yake cikin ɗakin ya shiga, pompo ne a ciki ya kunna ya tara ruwa a roba kana yayi wanka tareda kara ɗaura towel ɗin ya fito, mai ya shafa ya buɗe akwatin dake gefe ya ciro wani yadi coffee color wanda yake a goge, sawa yayi kayan ya karɓeshi sosai, sajenshi ya taje tareda gashin kanshi wanda yake a kwance kamar na balarabe, agogo ya ɗaura kana ya fito daga ɗakin hannunshi rike da takalmin da zaisa, ɗakin inna yaje yayi sallama, shiga yayi ya sameta tana zaune akan tabarma tana lazimi, saida ya jira ta gama ta juyo tana kallonshi
"Anwar Ina zuwa da sassafe haka?"
gaisheta yayi ta amsa tana kara tambayanshi ina zashi?
tashi yayi ya buɗe drower dake kusa da ita ya ciro wasu takaddu yace "wani company zanje suna neman ma'aikata"
shiru tayi batace komai ba, tasan koda yaje ba dole ya samu ba, lamarin kasan sai kana da uwa a gindin murhu zaka samu aiki, koda ka samu saide su danne su baiwa yaransu, kallonta yayi kana ya cigaba da gyara takaddun yana sawa a envelope, yasan tunanin da take, saida ya gana yace "inna ta? kada kisa komai a ranki Allah yana tare damu, kiyimin addu'a kawai"
"kullum cikin yimaka addu'a nake kuma Allah zai karɓa watarana"
fita yayi yana murmushi, mashin nashi me kafa biyu ya ɗauka kana ya fita ya buɗe kofa, unguwansu na talakawa ne, kana gani ka san marasa karfi ne a cikinta, a nutse yake tuka mashin ɗin, yayi tafiya me nisa kafin ya isa gidandu jameel, kiran layin jameel ɗin yayi yana ɗagawa yace "ina kofa"
jameel shima ya shirya ya yiwa ummanshi, addu'a tayi musu Allah ya bada sa'a, ya amsa da ameen.

ya sameshi ya harɗe hannu a kirji yana zaune akan mashin, leɓenshi na kasa yake ciza da karfi kaɗan yana kallon cikin unguwan, murmushi yayi kana yace "har ka fito?"
jijjiga kai kawai yayi, jameel ya hau bayan mashin ɗin, saida ya tada mashin suka fara tafiya yace "ya su umma?"
"suna lafiya meyasa baka shiga ba?"
kallon agogo yayi "banso muyi latti kusan karfe 7 fa yanzu"
"gaskiya ne, yau kam ba fita sana'a ko?"
tsaki yaja kaɗan kana yaci gaba da tuƙi kamar ba zaiyi magana ba, sai can sunyi nisa har jameel ta cire rai da magananshi yaji yace "zan fita idan mun dawo da wuri"
inda sabo ya saba da halin Anwar wani lokaci yanaji kana mishi magana zai shareka kamar baiji ba, sai idan yaga dama zai amsa, tun abin yana ɓata mishi rai yana ganin kamar girman kai ne, har ya gane ba girman kai bane haka nature ɗinshi yake, har suka isa company Jameel ne yake magana shi anwar saide yayi murmushi kawai, tun a bakin get aka duba takaddunsu sannan aka bari suka shiga, mutane ne dayawa a wurin kowa rike da takadda, jameel ya kalli Anwar shima anwar jikinshi yayi sanyi da ganin mutane da yawa da alama yauma ba sa'a suka fito.

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now