page 3

44 3 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸
    *HAƘƘI NA*
🌸🌸🌸🌸🌸

By
_jiddah S Mapi_

*Chapter 3*

              ~Ba magana nake ba? wa yake surutu?
shiru ƴan class sukayi kowa yana rarraba ido, noor ta zuba mishi idanunta tana kallonshi leɓenta na kasa a cikin bakinta tana tsotsa, idanunta masu kalan bacci ta lumshe kana ta kara buɗewa tana kallonshi, yasan itace hakan yasa yace "noor Aminu sadauki tashi kije kiyi kneel down a waje"
tashi tayi ta ɗau jakanta da sauran milk shake ɗin daya rage, cikin nutsuwa da raini take takawa har ta isa gabanshi, kallon banza tayi mishi kana ta fita daga class ɗin, zama tayi a gefe tana kallon mutanen dake cikin class suna karatu.

gaban haneefa ne ya faɗi ganin an fitar da noor waje, tasan laifi ta yiwa malami, dafe kai tayi "Innalillahi noor me kikeso ki zama a rayuwa?"
karatu ake a aji amma hankalinta baya kan malamin, gaba ɗaya ta tattara ta maida hankali kan noor, yatsa ɗaya ta ɗaga kana tace "excuse"
amsa mata yayi da "Yes"
tashi tayi tace zataje fitsari yace "okay"
fita tayi bata tsaya ko ina ba sai inda noor take, tana zuwa ta rankwashi kanta, juyowa tayi cikin masifa zatayi zagi, ganin haneefa tace "wash kaina unty hanee me na miki?"
tsaki taja cikin gajiya da halinta tace "noor me haka? kina ganin ƴan uwanki suna karatu ke an fitar dake? meyasa bakya ji ne?"
"sorry"

"sorry for your self, sabida kanki kike cuta bani ba, ki nutsu ki san me kikeyi a rayuwa"
turo baki tayi har haneefa ta gama ta tafi, har aka tashi noor tana waje ganin ana fitowa itama ta mike tana kaɗe jikinta, minal ce tazo tace "ke noor baki da tsoro ace malami yana magana kina kallonshi up and down?"

"to ni nace yazo ya koyar damu ne? kinga bani na ɗan sha kafin haneefa tazo"
komawa aji sukayi ba kowa a ciki sukaje bencin baya kana Noor ta jona pot ya fara zuƙa, saida tayi tatil har ta fara jin kanta yayi nauyi tana gani bibbiyu kana ta mike tace "na tafi" cikin muryan maye, fita tayi daga class ɗin ta bar minal aciki direct inda driver ɗinsu yake tsayuwa taje ta tsaya tana jiranshi, ita haneefa ta koma ciki tana duba noor ganin bata nan ta fito tana dubata, abin mamaki bata ganta ba sai tambayan ƴan class nasu take "Ina noor?"
kowa sai yace "ta fita ai"
sai daga baya ta hangota zaune a gefe ta ɗaura kanta a gwiwa kamar bacci take, bugunta tayi kaɗan kana tace "noor meya sameki?"
a hankali ta ɗago kai ta zubawa haneefa ido, da sauri ta waro ido ganin yadda idon noor ya canja yayi launin bacci da alama a buge take, dafe kirji tayi idanunta har suna cika da hawaye tace "noor? me nake gani?"
mikewa tayi kamar zata faɗi tana tangal-tangal, faɗawa tayi jikinta cikin muryan maye tace "unty haneefa kaina yayi nauyi"
daidai lokacin driver ɗinsu ya iso, janta haneefa ta fara har ta buɗe mata mota ta shigar da ita, sai ɗaga hannu take tana magana, shiga itama haneefa tayi da sauri ganin mutane suna kallonsu, tana shiga ta rufe marfin motan kasancewar tinted glass ne yasa babu me ganinsu, hannu tasa ta wanketa da mari, idonta ya fara zubar da hawaye cikin kuka tace "noor ba kincemin kin daina ba? dama ba dainawa kikayi ba?"
hannu tasa a idon haneefa tana share mata hawaye ɗayan hannun kuma ta dafe kunci inda ta mareta dashi tace "ki daina kuka kaɗan fa nashaaa.."

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un me zan gayawa abba? me zan gayawa Abba idan ya tambayeni meya sameki?"
lumshe ido tayi kana ta jingina kanta da seat tace "kice mishi kaɗan nasha"

kuka ta fashe dashi sosai, driver da yake tuƙi ya juyo yace "hajiya ki daina kuka"
lips nata ta ciza da karfi tace "ta yaya zan daina kuka? ka duba halin da kanwata takesa kanta a ciki"
"Hajiya addu'a zakiyi mata"

"malam babu abinda ya saka cikin maganan mu, ka cire tsamin bakinka daga maganar daya shafeni, gargaɗi nake maka"
noor tayi magana kamar zata mareshi, tsit yayi dan yasan zata iya marinshi, da haka har suka isa gida, a hankali haneefa ta rike hannunta ta fitar da ita daga motan, saida ta leka falo taga ba kowa kafin ta janyo hannunta da sauri ta wuce da ita zuwa room nasu, kwantar da ita tayi akan gado kana ta janyo bargo ta rufata, bacci me nauyi ya ɗauketa, zama tayi a gefe ta riko hannunta tana kallonta idonta yana zubda hawaye, ba abinda muka rasa a rayuwa meyasa noor take haka? duk wani gata Abba ya basu, kuɗi ilimi kyau Allah ya basu saide noor tana nema ta ɓata kyaunta da shaye shaye da kuma raina mutane.

HAƘƘI NAWhere stories live. Discover now