BABI NA ĎAYA

8.1K 409 22
                                    

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah (SWT)  da ya bani ikon fara wannan littafin mai suna Ba'a kanta farau ba. Ya Allah yadda na fara shi lafiya kasa na gama shi lafiya.

Sadaukarwar Littafin ta Fatima Binta Eshak asalin marubuciyar Ba'a kanta Farau ba. Ya Allah kaji kan Fatima Binta ka sadata da Rahamarka, ka ni'imta makwancinta kasa Aljanna Firdaus ce makomarta ka raya mata zuri'arta ka shiryar dasu shiri na addinin musulunci.

Hankalina a matukar tashe na karasa gidanmu, tunani ne fal a zuciyata. Idan har zargina ya zama gaskiya ni Khadija na shiga uku. Me zan cewa mahaifana akan irin kyakkyawar tarbiyyar da suka bani? Musamman Umma da a kullum nasiharta ita ce na kula da kaina na kare martabata da mutuncina na ďiya mace, amma na saka kafa nayi fatali dasu saboda zakin soyayya. Kaico na ni Khadija!

Nayi sallama na shiga gida. Goggo ce ke wanke-wanke a bakin famfo ita kuma Umma tana shara, nayi musu sannu da gida na wuce zuwa ďaki. Ina jin Goggo na tambayata "ya kika baro su Saratun"? Ban iya tsayawa na bata amsa ba domin kuwa abinda ya dameni shi ya dameni.

Cikin kuryar ďakin Umma na shige, can karshen gadonta na hau na kwanta, na cusa kaina a cikin filo ina kuka na a hankali. Kukan da nake jin bazan taba daina yinsa ba tun ranar da abin ya faru.

Umma ce ta shigo ta kare mini kallo sannan tace "wai Khadija lafiyarki kuwa, kin shigo babu magana, kina jin Goggonku ma tana tambayarki yadda kika baro Auntyn taki kika yi mata shiru. Ni fa abinnan naki ya fara isata, tunda kika zo hutun nan baki da walwala,  munyi tambayar kince lafiyarki kalau babu komai. To ko aljannu kika kwaso a makarantar"?

Banyi magana ba illa cigaba da nayi da kukan. Tayi kwafa tace "shikenan tunda abin naki ya kai da haka, bari na saka a kira Mallam watakila shi kya faďa mishi matsalar tunda mu kin raina mu". Da sauri na sauko daga kan gadon na rike kafafunta ina cewa "kiyi mini rai Umma zan faďa miki".

Zama tayi a bakin gadon ni kuma ina daga kasa na rike hannayenta, kaina a sunkuye nace "Umma ki yafe mini, na cuci kaina, amma wallahi Umma ba'a son raina bane. Na rike mutunci na, dukkan nasihohinki na ďauka, ban bata tarbiyyar da kuka yi mini ba amma Umma tsautsayi yasa rana ďaya shaiďan ya ribace ni na karya alkawarin da nayi miki".

Tace "ke ni kin isheni, kin sakani a duhu, me kike nufi da waďannan zantukan? Nace "kin sha faďa mini yadda mace take gane tana ďauke da ciki da yanayin da ake ji, haka ma a makaranta an faďa mana ďaukewar al'ada yana ďaya daga cikin alamar ďaukar ciki. To ni yau Umma kusan wata na biyu kenan banyi ba, kuma ina jin sauyi sosai a tare dani".

Wani irin kallo Umma ke bina dashi kafin tace "ke kin taba kwanciya da wani namiji ne"? Ras! Ras!! Gabana yaci gaba da faďuwa, na sunkuyar da kaina kasa. Ta sake maimaita tambayar nan ma shiru nayi mata, tsawa ta daka mini da ta sake firgitani, da sauri na ďaga kaina alamar "eh".

Kalmar Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir Raji'un ta dinga nanatawa kafin ta fashe da wani irin kuka ta rufeni da duka. Banyi kokarin guduwa ba, idan dai har dukan nawa zai wanke mata zuciya zan so hakan.

Kukan Umma Goggo ta jiyo ta shigo da gudu tana cewa "lafiya Umman Ali, me ya faru"? Ta janye ni, Umma sai kokarin finciko ni take yi. "Ki kyaleni Yaya, kyaleni nayi wa 'yar banza dukan da zata kasa tashi, Khadija ta cuce mu. Wai ace duk kaf-kaf ďin da muke yi dasu da irin tarbiyyar da muke yiwa yarannan duka a banza. Karshe sai zuwa tayi ta yiwo cikin shege, oh ni Sakinatu ya zanyi da kunyar duniya da faďan Mallam".

Dabar Goggo ta zauna itama ta fara salati. Ni kam addu'a nake yi mutuwa tazo ta ďaukeni ko na huta da wannan jidalin, wai suma kenan, inaga idan Baba yaji.

Nutsuwa ce ta zo wa Goggo ta matso kusa dani tace "me yasa Khadija? Ke kuwa garin yaya hakan ta kasance? Bayan kowa a unguwar nan yabon halayenki yake yi, har ana son yara su rika yin koyi daje. Wai shin ma waye yayi miki cikin"? Nayi shiru. Cikin ďaga murya tace "tambayarki nake yi da waye kuke lalacewa har ciki ya bulla a jikinki? Gara ma tun wuri ki faďa mu san abinyi tun kafin Mallam ya dawo".

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now