BABI NA TALATIN DA ĎAYA

2.7K 200 35
                                    

Wanka nayi na shirya a cikin lace cotton ďinkin fitted riga da skirt. Kayan sun yi mini cif tamkar a jikina aka ďinka, sannan nabi dukkanin jikina da turaruka masu sanyin kamshi bayan na shafe duk wata gaba ta jikina da haďin kulacca mai daďi da humra.


Ban ďaura ďankwalin leshin ba sai mayafi siriri daya shiga da kayan na yafa a kaina. Flat slippers ďin aldo na saka a kafafuna na fita parlour.


Tun shigowata gidan a jiya da magriba ban fita daga cikin ďakina ba sai yanzu don haka ban san yaya fasalin gidan yake ba. Sosai na yaba da tsarin sitting room ďin.


Babu wasu tarkace a ciki, daga saitin leather seats ďina kalar coffee sai labulaye orange da ratsin coffee ďin sai kayan kallo, sai kuma Chinese table da aka ajiye daga kusurwar dake kallon kofar shigowa da cloth ďinshi kalar golden and coffee. Sai dakakkun ornaments da aka jera akan chinese table ďin.


Daga gefe kuma karamin dining table ne mai kujeru huďu a ajiye. Kofar dana gani a wurin dining ďin na shiga, anan na samu madaidaicin kitchen ďauke da duk wasu kaya na bukata a harkar girki.


Wani irin farin ciki ne ya lullubeni don duk gidan kitchen ďin yafi burgeni. Store na shiga na tarar da kayan abinci a jibge don haka na ďebo irish potatoes na wanke a sink sannan na hau fira.


Sai da na bare kusan rabi sannan na fito da frying pan na wanke na zuba mai na ďora a wuta na fara soyawa. Sauran dankalin na cigaba da barewa.


Ban ankara ba kawai naji hannuwa sun zagaye ni, ya ďora kanshi akan kafaďata ta hagu, sai da yayi kissing gefen wuyana sannan yace "Morning my dear, shine baki tasheni ba ko?"


Cikin rawar murya nace "naga ne kamar kana jin daďin baccin shi yasa ban tashe ka ba amma ayi mini afuwa" saboda yadda hannayenshi ke bin jikina, tuni ya sakar mini da kasala.


"Ba laifi kika yi ba sweetheart. Yanzu me kike dafa mana don da wata irin yunwa na tashi". "Chips ne da scrambled egg sai tea" na amsa mishi.


"Ok, to yanzu me zan tayaki da shi?" Dariya nayi nace "babu komai, ai na kusa gamawa". Yace "to shikenan, bani 2 minutes yanzu zan je na dawo". "To" kawai nace shi kuma ya fita ya barni na karasa haďa breakfast ďin.


Har na gama na shirya abincin akan table bai fito ba. Parlour na dawo na zauna akan kujera three sitter. Ban daďe da zama ba sai gashi ya fito. Hannunshi ya miko mini, kamawa nayi ya mikar dani tare da rungumoni a jikinshi.


A haka muka isa wajen table ďin, janyo mini kujera yayi na zauna sannan ya zauna a kujerar dake kusa da tawa. Tea na haďa na ajiye a gabanshi sannan na haďa nawa, a plate ďaya na shirya mana abincin don haka tare muka ci har muka koshi.


Tattare kwanukan nayi na kai kitchen, sai da nayi wanke-wanke na gyara kitchen ďin sannan na fita. Yana kwance akan doguwar kujera yana danna remote ďin tv. Zama nayi akan single chair, tun kafin na ida zama ya miko mini hannunshi tare da cewa "zo nan sweetheart".


Tashi nayi na koma kusa dashi na zauna. "Oya bani labari" yace mini, "yaushe bakonki zai tafi?" A kunyace na kauda kaina nace "wane bako kenan?"


"Aw baki ma san shi ba? To ina nufin yaushe period ďinki zai ďauke don sosai ya kawo mini cikas kasancewata ango" ya karashe maganar tare da kashe idonshi guda ďaya.


Tafukan hannuna na saka na rufe fuskata don sosai ya sakani jin kunya. "Baki amsa mini tambayata  ba fa Khadija", kauda kaina nayi nace "nima ban sani ba, kamar yadda bai sanar dani ba lokacin da yazo haka yanzu ma bai sanar dani ranar tafiyar shi ba".


BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now