BABI NA TALATIN DA UKU

2.4K 184 11
                                    

Hajiya na zaune a parlour tana kallon shirin gari ya waye a tashar Arewa24 na shiga da sallama. Karasawa nayi kusa da ita na zauna kafin na gaisheta. "Lafiya lau Khadija, ya gidan naku kuna lafiya dai ko" nace "lafiyarmu lau Hajiya".

Tace "madallah, akwai abinci a kitchen sai ki ďauko muku" nace "ni kam a koshe nake ban san ko Manal ba ko Daddynta don tare muke sun tsaya a wurin Baba". Jefi-jefi muke hira da Hajiya don yanzu bana iya sakewa da ita kamar da sosai nake jin nauyin ta.



Habib ne ya shigo yana ďauke da Manal dake bacci, ďakin Hajiya ya shiga ya kwantar da ita sannan ya fito ya zauna suna gaisawa.


Tashi nayi na koma ďakin Hajiya na zauna. Humaira na kira a waya muka shiga hira sai kace ba ďazun nan muka rabu a school ba.


Bamu bar gida ba sai da muka sallaci isha muka ci abinci sannan. Mun fito zamu tafi ne Hajiya ta ďauko fura da nono daga fridge ta bamu tace "ga fura nan na sanku ma'abota shan ta ne, jiya Alhaji ya kawo mana da yaje Jigawa".


Sosai nayi wa Hajiya godiya don kuwa na kasance ma'abociyar shan fura da nono, shima kuma Habib ďin haka yake.


A hanyar mu ta dawowa ne Habib ya tsaya a Yahuza suya dake nan kan titin court road ya saya mana gasashiyar hanta. Muna isa gida na wuce kitchen na juye hantar a cikin plate na ďora akan tray sannan na fito da gorar ruwa daga fridge na haďa da cups na ďora akan tray ďin na ďauka na fita.


Yana zaune akan kujera three sitter yana tuning channels, Manal kuma na zaune a gefenshi tana shan ice cream. Ajiye tray ďin nayi akan center table nace mishi "Bismillah".


Kallon tray ďin yayi sannan yace "furar kuma fa? Nayi zaton ita kike damawa ai".


"Fura yanzu da dare Yaya, na bari ne sai gobe sai na dama amma idan kana da bukata sai na damo maka. Ni dai ba zan sha fura yanzu ba don ina tsoron kiba".


Dariya ya saka yace "ba kya exercise ne shi yasa kike tsoron shan fura da dare, ni kam nasan babu abinda zata yi mini don haka damo mini na sha". Komawa nayi kitchen na damo furar na kawo mishi.


Manal na gani tace "Maami nima zan sha furar kin ji". Harararta nayi nace "ban hana ki roko ba?" Kafin ma na rufe bakina Habib yace "ďauko cup ki zuba mata ai zata ishemu".


Kitchen na tafi na ďauko kofin sai dai har ga Allah bana son yadda Habib yake sangarta Manal. Babu dama nayi mata faďa idan tayi ba daidai ba yanzu ne zai fara faďa yana cewa na fiya takura mata da yawa, shi a wurin shi komai tayi daidai ne, na rasa wane irin so ne yake mata da baya ganin laifinta na kuma kasa nuna mishi cewa hakan da yake yi ba daidai bane.


Furar na zuba mata na bata sannan na zauna naci hantar tunda ni ba fura zan sha ba na rage musu tasu na tashi na shige ďaki.


Bathroom na shiga nayi wanka sannan na fito na shirya a cikin wata very short and sexy black nightie. Daga wajen kirjin aka yi mata gida kamar na brazier sai kuma aka tsaga ta har kasa gefe ďaya yayi lapping akan ďayan, don haka a buďe take boobies ďina ne kawai a cikin riga.


Silk thong kalar baki na saka. Sosai na wadata jikina da turaruka masu sanyin kamshi. Abaya na ďora akan kayan na fita parlour. Ko zama ban yi ba na tashi Manal ganin alamun bacci a idonta na kaita ďaki nayi mata wanka sannan na shiryata a cikin nightie ďinta na kwantar da ita.


Addu'a nayi mata sannan na zauna har sai da tayi bacci sannan na tashi na koma parlour wajen Habib. Ban same shi a parlour ba don haka na bi shi ďakin shi.


Ina shiga yana fitowa daga wanka. Karasawa nayi na amshi towel ďin hannunshi na taya shi goge jikinshi. Da taimakona yayi shirin bacci sannan muka yada zango akan gado.


"Woww" yace bayan dana cire abayar dana ďora akan kayan barci na. Hannu nasa na rufe idona don sosai naji kunya ta kamani. A kunnena naji yana yi mini raďa "buďe idonki mana baby, buďe kiga wani abu".


Pillow na ďauka na ďora a kaina ina dariya kasa-kasa. Wai ni Habib zai yi wa wayo. "Ba zaki buďe ba?" na jiyo shi yana cewa. "Um" nace ina mai kara kudundunewa akan gadon.


Hannu yasa ya ďago ni na faďo jikinshi sannan ya cire hannuna daga kan fuskata. "Wai ni kike jin kunya?" gira na ďaga mishi alamar amsawa fuskata ďauke da murmushi. "Ai na ďauka na cire kunyar ashe da akwai saura ban sani ba, dole ashe na dage don ganin na raba ki da ita" ya kara faďa.


Mun daďe muna hira da 'yan wasannin mu kafin mu kwanta bacci.


Duk sati biyu Habib yake zuwa Kano har muka samu watanni huďu da aure. A wannan zuwan da yayi ne ya samu mun yi hutun 1st semester don haka yace na shirya idan zai koma tare zamu tafi Abuja don mu gaisa da matarshi kasancewar tunda akayi auren bamu haďu ba duk da cewa ta zazzo Kano wajen sau uku amma bata sauka a gidan ba sai dai ta sauka a gidansu duk kuwa da cewa tana da part ďinta a gidan, hasali ma ni part ďin Habib ne aka saka ni a ciki.


Haka nan kuma ina ďauke da ďan karamin cikin da ba zai gaza wata biyu ba don ko Habib ban sanarwa ba. Shiri sosai nake yi na tafiya Abuja duk da sosai nake fargabar haďuwata da Nabila don ban san wacce irin tarba zata yi mini ba.


A son Habib mu tafi tare da Manal to kuma basu yi closing school ba don haka yace a barta wajen Hajiya idan yaso sai ake kaita school daga nan.


Karfe goma na safiyar lahadi muka bar Kano zuwa Abuja. Muna tafe muna hira har Allah yasa muka isa da karfe uku na rana. Gidan shi na nan a wuse zone 2.


Bungalow ne mai ďauke da ďakuna huďu da sitting room guda ďaya, sai wadatacciyar compound. Yana gaba ina biye dashi a baya muka shiga gidan da sallama.


Gidan tsit tamkar babu mutane. A parlour na zauna shi kuma yabi wata corridor da nake ganin zata sada mutum da ďakunan bacci bayan yace mini "2 minutes bari nayi magana da Nabila".


Tare suka fito da ita. Babu yabo fallasa ta karbe ni, zama tayi muka gaisa. "Ban ga su Walid ba" nace bayan mun gama gaisawa. A dakile tace mini "suna islamiyya".


Habib bai zauna yayi komawa ciki, nasan wanka zai yi don shine abu na farko da yake fara yi bayan yayi tafiya. Tashi tayi ta koma ciki ta bar ni anan wurin a zaune gashi ina so nayi sallah sai dai ban ga alamar matar gidan zata bani wuri ba don ko arzikin ruwan sha ban samu ba.


Nafi minti talatin a zaune a wurin sannan Habib ya fito. Sosai fuskarshi ta nuna mamakin ganina a zaune a parlour har lokacin. "Nabila" ya kwala mata kira.


Shiru babu amsa har sai da ya kara ďaga murya ya kirata sannan ta ansa ta fito tana yatsina fuska. Bai kula da yadda take ta faman ciccin magani ba yace "me Khadija take yi a parlour har yanzu baki kaita ďaki ba?"


Wai sai ce mishi tayi "bani da ďakin bata ne ai kaima ka sani". A mamakance ya kalleta yace "ban gane da baki da ďakin bata ba, ina ce tun kafin na tafi mun yi magana nace ki sa a gyara mata spare bedroom room ďin can don tare zamu zo".


A dakile take amsa mishi tamkar tana magana da wani ďanta, "amma ai kasan su Jamila na nan kuma a ďakin na sauke su" tace tana wani shan kamshi.


Ni dai baki da hanci da ido na saki ina kallon ikon Allah. "Bana son fitina fa Nabila, me zai sa bazaki sauki su Jamila a ďakin ki ba kamar yadda kike yi a baya".


"Sai kuma kayi" tace mishi sannan tayi tafiyarta ta barshi anan wurin a tsaye. Sosai ranshi ya baci sai dai yayi kokari kwarai ya danne zuciyar shi.


A ďakin shi ya saukeni ganin matar gidan tace bata da wurin da zata ajiyeni ya fita don ya shigo mana da kayanmu. Ni dai bath na faďa na watsa ruwa sannan na ďauro alwala na fito.


Akwatina na gani ajiye a gefe don haka na buďe na ďauki kayan da zan saka na mayar na rufe. Ina gama shiryawa na kabbara sallah.


Ko da na idar gado na haye na mike don sosai nake cikin gajiya bare da ba wani baccin kirki na samu ba jiya. Ina ďora kaina akan pillow bacci ya ďaukeni, sai ji nayi Habib yana tashina wai na fito naci abinci.


Tashi nayi ina mutsika idanuwa don sosai na fara jin daďin baccin da nake yi.


UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now