BABI NA BIYAR

3K 194 2
                                    

ASALIN LABARIN

Mallam Hashimu Masinja sunan mahaifina. Asalinshi mutumin kafin madaki ne ta jihar Bauchi wato karamar hukumar Ganjuwa. Allah ya azurta mahaifina da matan aure guda biyu, Goggonmu mai suna Asiya sai kuma Sakinatu wacce muke kira da Umma.

Goggo asalinta mutuniyar kano ce, biki suka zo kafin madaki inda Allah ya haďa su da Baba kasancewar shi babban abokin ango ita kuma tana ďaya daga cikin 'yammatan amarya. Biki bai tashi ba sai da soyayya ta kullu tsakanin Hashimu da Asiya wacce ta kaisu ga aure.

Zama suke yi cikin kauna da aminci gwanin sha'awa don ko kusa ba'a taba jin kansu ba, sosai suke nunawa junansu kulawa. Shekararsu uku da aure amma har wannan lokacin Allah bai basu haihuwa ba, abinda yaso ya shafi zaman lafiyar gidan don dangin Mallam Hashimu sun sako Asiya gaba da gori akan rashin haihuwa yayinda Mallam Hashimu ya saka auduga ya toshe kunnuwanshi daga jin dukkan surutansu akan maiďakinshi yace shi dai yake zaune da matarshi haihuwa kuma nufi ne na Allah samu ko rashinta ba zai kawo nakasu a cikin zaman lafiya da kwanciyar hankalinsu ba.

A Shekararsu ta biyar da aurene Allah ya haďa shi da Sakinatu 'ya a wurin kishiyar Innarshi kanwar mahaifiyarshi. Tunda Mallam Hashimu ya kyalla idanu ya gano Sakinatu ya rasa sukuni da nutsuwar zuciyarshi har saida ya dangana da gidan Innarshi don neman iri.

Bai sha wahalar shawo kan Sakinatu ba ta amince dashi a matsayin mijinta don haka ba'a ďauki dogon lokaci ba aka sha bikinshi da Sakinatu. Zaman lafiya akeyi a gidan Mallam Hashimu don kuwa Asiya ta kama girmanta sosai take jan Sakinatu a jikinta, inda kuma aka yi sa'a Sakinatu ba mai fitina bace don haka tana bawa Asiya girmanta sosai.

Watannin Sakinatu goma a gidan Mallam Hashimu ta haifo ďiyarta mace mai matukar kama da mahaifinta. Murna a wajen Asiya tamkar ita ta haifi yarinyar ba kishiyarta ba. Ranar suna aka sakawa jaririya Saratu. Tun bayan suna rainon Saratu ya koma hannun Asiya, tsakaninta da Sakinatu shan nono dalilin da yasa da ta isa yaye Sakinatu bata kai ta gidansu ba kamar yadda Inna ta bukata sai ta barta a hannun Asiya tunda daman dukkanin hidimarta a hannunta take.

Bayan Saratu ne ta haifi Ali sai dai shi baiyi tsawon rayuwa ba don yana da shekara ďaya da rabi ya rasu a sanadiyyar zazzabin cizon sauro. Bayan Ali ne ta haifi Adamu sai Yusuf sannan kuma ni Khadija. Sai da Umma ta shekara biyar da haihuwata sannan tayi mini kanne tagwaye wato Hassana da Husaina sai kuma Gambonsu mai suna Bilkisu wacce ta kasance auta. Har wannan lokacin Allah bai bawa Goggo haihuwa ba don haka ta kama mu ta rike tamkar ita ta haifemu don idan ba faďawa mutum akayi ba babu yadda za'ayi ya gane cewar ba ita ce mahaifiyarmu ba.

Tun daga kan Aunty Saratu har zuwa Yaya Adam da Yaya Yusuf duk a wurin Goggo suka taso, daga kaina ne tace ta barwa Umma don itama ta samu yaro a ďakinta. Akwai shakuwa sosai tsakanina da Umma ko don daďewar da tayi ne bata yi mini kanne ba ko kuma don nice babbar 'ya a ďakinta ban sani ba.

Abinda na sani shine tun ina karamata Umma take sakani a ďaki tana koyar dani ilimin zaman duniya. Tun tasowata na kasance yarinya mai tsananin wayo da hankali don duk wasu shirmen yarinta bana cikinshi. Kullum zaki sameni a kusa da Ummata ina taya ta aiki ko kuma ina tayata da rainon su Hassana.

Haka nan a makaranta na kasance mai tsananin kwazo don ko jarabawa akayi ban taba wuce ta uku ba. Ina da shekaru goma akayi bikin Aunty Saratu da saurayinta Mallam Zakari headmaster mu na makarantar boko.

A shekarar ne kuma na samu gurbin karatu a Government Girls College Kafin Madaki, tunda na karbo admission letter ďina nake murna, na kasa aiwatar da komai sai list ďin kayan bukatar kowanne ďalibi da aka haďo da admission letter ďin.

Goggo tayi dariya tace "su Khaddo duk murnar ce ta hana miki cin abinci, ai gara ki daure ko ďan yaya ne kici sai ki wuce gidan Auntynki ki sanar da ita duk da dai nasan bazata kasa sani ba". Na ďago kaina daga duban tsofaffin littattafan Yaya Yusuf da nake yi ina cire waďanda aka rubuta a jikin list of books ďin tamkar dai yau ne ko gobe zan tafi makarantar nace "so nake na gama haďa littattafan nan Goggo sai naci abincin, ai ma na kusa gamawa".

Kaďa kanta tayi ta wuce tana cewa "yunwar ce bata dameki ba shiyasa amma banda haka ko ganin takardar makarantar taki Mallam baiyi ba kike ta faman shiri kamar ke zaki kai kanki makarantar".

Ni dai ban tashi ba har sai da na gama haďa kan littattafaina na kai ďakin Umma na ajiye sannan na ďauki abincin naci. Ina gamawa nayi wanka na shirya a cikin atamfar nichem ďinkin sallarmu na bara na saka sannan na ďauki hijabina na saka na yiwa su Umma sallama na tafi gidan Aunty Saratu.

Cikin tafiyata ta nutsuwa tamkar mai tausayin kasa nake takawa, kasancewar babu wata tazara tsakanin unguwarmu da tasu yasa ban wani ďauki lokaci ba na isa gidanta. Da sallama na shiga cikin gidan, daga cikin parlournta naji ta amsa kafin tace mini "shigo mana Khaddo kin tsaya a waje sai kace wata bakuwa".

Karasawa nayi cikin parlour, tana kwance a kasa tayi matashin kai da pillow na durkusa na gaisheta sannan na hau kan kujera na zauna. "Yasu Goggo da Umma da kuma 'yanbiyu? Me yasa baki zo dasu ba? " nace "Lafiyarsu kalau duk suna gaisheki,'yanbiyu sun tafi islamiyya shi yasa banzo dasu ba amma naji Umma tace ranar alhamis zasu zo su gaisheki".

"Ai ya kamata don da har na fara mitar cewa Umma tana mini rowar yaranta shi yasa bata taba turosu ba, ki shiga kitchen ki ďebi abinci". Na girgiza kaina tare da cewa "a koshe nake din ina gama cin abinci na taho nan, dama zuwa nayi na gaya miki naci jarabawar tafiya secondary kuma naci sa'a na samu nan ggc".


Cikin murna tace "iyye ashe 'yar boarding ce nake tare da ita, shikenan kin kusa tafiya ki bar Ummanki kuma. Allah ya taimaka ya bada sa'a, wa yaga su Khaddo a boarding".

Cikin dariya nace "Ameen Aunty". Ban bar gidanta ba sai yamma don sai da na tayata da shara da wanke-wanke sannan". Don ďoki da kyar na iya barin Baba ya gama cin abinci sannan naje na kai mishi takardar admission ďita tare da sanar dashi makara da naci wato makarantar 'yammata ta nan garinmu.

Shima yayi murna sosai don dama baya so nayi nesa da gida saboda a ganinshi nayi kankanta da zuwa makarantar kwana a shekaruna na goma sha ďaya babu kaďan don shi a sonshi a kyaleni zuwa baďi kafin nan na kara girma sai na rubuta jarabawar tafiya secondary ďin Mallam Zakari ne yace ya kyaleni na rubuta kada a tauyeni tunda dai ina da kokari shine kuma ya bada shawarar a cike mini GGC Kafin Madaki tunda nan ďin gida zuwa ganina ba wuya zaiyi ba.

A cikin kwanakin da suka biyo baya shirye-shiryen tafiyata makarantar kwana kawai ake yi. Goggo ta daka mini yaji da kuli-kuli, an soya mini man gyaďa ga kuma kanzon da aka tara mini an dake mini shi lukui. Sai kuma Baba da yayi mini sayayyar kayan masarufi irinsu madara, milo, suga, biskit da dai sauransu. Sai kuma katifa, bokiti da jarkar ruwa da sauran kayayyakin da aka bukata.

A duk lokacin dana juya na kalli kayana sai naji wani farin ciki ya lullubeni ganin wai duka waďannan kayan nawa ne. An shirya mini kayan abincina a sabon akwatina na garwa da aka sayo mini sai kuma sauran kayan amfanina kamarsu uniform da sauran kayana na sakawa da aka shirya a cikin 'yar madaidaiciyar jakar Ghana must go.

Daren ranar da zan tafi kuwa ko barcin kirki ban iya yi ba, haka nan a wajen karyawa sai da Umma tayi mini jan ido sannan na caccakala na ture nace na koshi. Gaba ďaya na kosa Baba ya dawo daga wurin aiki inda ya tafi ya ďauko izini saboda shi zai rakani makarantar.

UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now