BABI NA GOMA SHA BAKWAI

2.3K 201 14
                                    

A gajiye kwarai na shigo gida daga school, sallar azahar kawai na iya yi na kwanta bacci a inda ban farka ba sai karfe huďu da kusan rabi.

Ina tashi na faďa banďaki na watsa ruwa sannan na ďauro alwala na fito. Doguwar rigar material na saka na saka hijabi na sannan na tada sallah. Koda na idar ban tashi ba sai da nayi tilawar Suratur Rahman.

Ban iya cire hijabin jikina ba na wuce kitchen na ďebi abinci don wata irin yunwa nake ji. Parlour Hajiya na shiga, sai da na gaisheta sannan na zauna akan kujera na fara cin abinci.

Bayan na gama ne tace mini "dama ke nake jira ki tashi daga baccin na aike ki gidan A'i mai waina ta baki a rubuce lissafin waina da sinasir ďin da muka yi magana akai" nace "to" ina mai mikewa tsaye.

Sai da na ajiye plate ďin dana gama cin abinci a kitchen sannan na wuce wajen aiken da Hajiya tayi mini. Shirye-shiryen bikin Humaira ake yi don haka Hajiya ta kasa zama, bare yanzu ne za tayi auren 'ya mace.

A kofar gida naga Yaya Habib da Manal suna zaune akan benci da ledar aya a hannunta. "Ina yini" nace mishi ina mai russunawa duk da nasan ba lallai ne ya amsa ba. Ga mamakina sai naji ya amsa mini da lafiya.

Biyoni Manal tayi tana cewa "Maami zan raka ki". Hannunta na kama muka cigaba da tafiya tana mini surutu. Har muka isa gidan A'i mai waina. Da sallama na shiga gidan, a tsakar gida na sameta don haka bayan mun gaisa na isar mata da sakon Hajiya.

Bakuwar dake tare da ita ce ta kalleni sama da kasa kafin tace "wannan ba Khaddon Umman Ali bace?" Cikin faďuwar gaba na ďago kai na kalleta, ba wata bace illa Mairon Iliya mai icce. "Eh nice" kawai na iya ce mata na sunkuyar da kaina ina jiran A'i ta gama rubuta mini breakdown ďin na tafi don har ga Allah ban so ganin Mairo ba don nasan yanzu ne labari na zai watsu a cikin garinmu kasancewarta mace mai ďan karen surutu.

"Ikon Allah" tace tana mai rike haba. "Ashe nan garin kika taho?" nace mata "eh". "To anan ďin a gidan wa kike? Ko dama kuna da 'yan uwa a garin nan?" ta kara tambayata. "A gidan Kawuna nake Yayan Goggo" na bata amsa.

Sai cewa tayi "ayi ashe gidan Kawunki kika gudo, ai wallahi Khaddo kin bani kunya don sosai nayi mamakin jin abinda kika aikata kika kuma iya saka kafa kika gudu kika bar Ummanki da bakin ciki, hala wannan ce 'yar da kika haifa? Ko kuwa dai zubar da cikin kika yi?"

Kwalla ce naji ta cicciko a idunana. Sai a lokacin A'i ta saka baki tace "kin santa ne kika sakata a gaba kina yi mata tambayoyi?" cikin ďaurewar fuska tayi maganar don haka Mairo ta shiga taitayinta ta amsa mata da "eh, 'yar makotanmu ce" kawai.

Ina samu A'i ta miko mini takardar data rubuta breakdown na kuďin aikin waina da sinasir ďin na tashi tare da kama hannun Manal nayi musu sallama na fice ina goge hawayen dake zuba daga idanuna.

Khadija na fita A'i ta kalli Mairo tace "wanne irin yada girma ne wannan zaki saka yarinya a gaba kina neman titsiyeta gashi nan har kin sakata kuka? Nifa bana son kinibibi kin sani".

"Uhm Yaya kenan, don baki san abinda ta aikata ba shi yasa kike ganin kamar titsiye nake son yi mata, amma kafin nan ina so na tambaye ki don Allah a gidan wa take duk da dai tace a gidan wan Goggonta take na kuma san cewa itan 'yar nan Kano ce to amma ba wai na yarda bane don a yadda na samu labari cewa akayi ta shiga duniya sai kuma na ganta anan".

"Hmmm... Mutanen duniya kenan, nutsatsiyar yarinya irin Khadija za'a kalla ace tana yawon duniya, to ni tun sani na da ita ban taba jin an faďi wani mummunan hali nata ba, duk wanda ya buďi baki kuwa zakiji yana yabon halayenta ne, tsakaninta da kowa girmamawa ce. Yarinyar da bata zuwa ko ina daga makaranta sai aike irin wannan idan anyi mata, kuma gidan da take ba karamin gida bane ba zasu yarda da shashanci irin wanda kike faďa ba".

"To ko acan garin namu ai an shaidi nutsuwarta amma wannan bai hanata buďewa kato cinyoyinta ya santa ďiya mace ba, bullowar ciki a jiknta ne ya sakata barin garin, ashe nan ta taho. Ko kuwa zaki ce mini bada ciki tazo nan ba?" Mairo ta faďa a kufule don taga Yayarta na neman karyatata akan abinda tasan tabbas anyi.

Murmushi A'i tayi sannan tace "kina bani mamaki Mairo, don Allah dubi kiga yanda kike zakalkalewa akan maganar nan duk a kokarinki na ganin kin bata yarinyar nan a idona. Banyi miki musun tazo da ciki ba amma ba damuwa ta bace sanin yadda akayi ta same shi, shi ďa da kike gani na kowa ne, tsakaninmu dasu addu'a ce da fatan shiriya. Bai kamata don kin santa kin san tarihinta ba kizo kina bazata a inda ake ganin mutuncinta, tamkar kin fallasa asirin da Allah ya rufa mata ne.

Yanzu da kike kokarin ganin kin batata a idona ribar me zaki ci? Ke yanzu ba 'ya'ya gare ki ba, idan irin haka ta kasance dasu zaki so aje ana talla dasu lungu-lungu kusfa-kusfa? Ai abinda baka so ayi wa naka kada kayiwa ďan wani, ko kuwa bake bace kike mini kukan cewa Lawwali na nema ya lalace don ya fara bin abokan banza suna neman koya mishi shaye-shaye? Idan akayi miki irin abinda kike neman yiwa Khadija akan Lawwali zaki ji daďi?

To ahir ďinki kinji na faďa miki, a kullum kika san ba alkhairi zaki faďa ba to kiyi kokarin kame bakin ki. Ita kuma Khadija idan har halinta ne abinda kika ce tayi sai kiyi mata fatan shiriya don babu wanda zai so ganin nashi ya lalace".

Zuwa wannan lokacin jikin Mairo yayi sanyi don kuwa tasan tana ďaya daga cikin waďanda suka dinga yayata maganar cikin Khadija gida-gida don dama suna jin haushin yadda kowa ya buďi baki sai ya yabi nutsuwar ta don da ita ake kwatance ta wajen tarbiyya da nutsuwa a unguwarsu, yanzun ma kuma niyyarta taje gida ta baza cewa ta ganta a garin Kano da 'yarta.

Karin abin haushin ma shine yadda samari ke ďaukar yarta Bahijja suna ajiyewa, ga abin magana nan a karkashin ta bata gani ba sai na wasu take hangowa.

Ina isa gida na mikawa Hajiya sakonta na wuce ďaki na kwanta, gaba ďaya raina a jagule yake da abinda Mairo tayi mini, duk da nasan cewa gaskiya ta faďa, ko meye ya faru kuma ni na jawowa kaina amma sai da naji zuciyata ta tabu.

UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now