BABI NA ASHIRIN DA BIYU

2.5K 199 8
                                    

A safiyar ranar lahadin data kasance kwana takwas da bikin Humaira na kasance a ďaki ina karanta notes ďina kasancewar gab muke da fara exams.

Karatun kawai nake yi amma ba wai ina fahimtar me nake karantawa bane saboda zuciyata dake tafiya yawo wajen tunanin abinda ya hanawa Yaya Habib turo mini message kwanaki biyun nan.

Ban san cewa nayi sabo da buďe ido da messages ďinshi ba a duk safiya haka nan duk dare message ďinshi ne abu na karshe da nake karantawa kafin na kwanta bacci, sai kwana biyun nan daya daina turowa.

Tun ina tunanin ya turo matsalar network ce ta hana shi isowa har na dawo na fahimci cewa turowar ne gaba ďaya bai yi ba. Dana ji 'yar kara a wayata zan janyota na duba tare da fatan ganin message ďinshi, duk bayan wasu 'yan mintuna nake duba wayata with the hope of seeing his message amma shiru kake ji.

Tattare books ďin nayi na ajiye a gefe na gyara kwanciyata don naji daďin yin tunanin daya aureni kwana biyu. Me yake shirin faruwa dani ne ni Khadija? Yau na shiga ukuna. Amma zuciyata baki yi mini adalci ba ganin yadda kike neman tarwatsa duk wasu matakan tsaro da na saka na katange ki dasu.

"Ya Allah" nace ina mai nutsa hannyena a cikin gashina. Ina ma zan samu bacci ya ďaukeni ko zan samu sassaucin wannan nacaccen tunanin daya addabe ni.

Ina kwance ban sani ba ashe bacci ya ďaukeni sai ji nayi Manal na tashi na wai "Maami kizo inji Daddy" tare da girgiza ni. "A ina kika ga Daddyn?" nace mata bayan na buďe ido. "Yanzu yazo yana parlour Hajiya shine yace na kira ki" ta amsa mini cikin 'yar karamar muryarta.

Tashi nayi na shiga toilet na wanke fuskata sannan na fito na ďauki hijabina na saka na kama hannun Manal muka fita. Da sallama na shiga parlour. "Wa'alaikissalam" ya amsa mini tare da maido da fuskarshi gareni.

Zama nayi akan kujerar dake kusa da kofa yayinda Manal ta saki hannuna ta tafi wajen Yaya Habib ta zauna. "Ina kwana" nace mishi ina mai sunkuyar da kaina don haka nan naji na takura da kallon da yake mini.

"Lafiya lau Khadija" yace yana mai cigaba da kassara ni da idanuwanshi. "Ďago kanki ki kalleni Khadija, magana nake so muyi".
Ďagowa nayi na kalleshi sai dai babu shiri na sauke idanuna kasa don bazan iya jurar kallon da yake jifana dashi ba.

"Gani a gabanki Khadija na kawo kaina na kuma zo da kokon barata ina fatan zaki dubeni da idon Rahama ki amsa bukatata ta son aurenki".

Rasa me zance nayi don sai naji maganarshi tamkar saukar aradu a kaina. Duk da na tsammaci jin hakan daga gareshi duba da yanayin messages ďin da yake turo mini masu nuni da tsantsar soyayya.

Shiru ne ya ratsa parlour na wasu dakikai sai kuma karar tv dake kunne don hatta da Manal tayi bacci a jikinshi.

"Kinyi shiru Khadija ko bakiyi na'am dani bane?" ya katse shirun ta hanyar jefo mini tambaya. Girgiza kaina nayi. "To yaya ne? Kada ki damu fa ki faďa mini abinda ke zuciyarki i promise you zan fahimce ki, ba kuma zan tilastaki akan abinda ba kya ra'ayi ba".

Ji nayi inama kasa zata buďe na shige ciki don kunya. Ta yaya zan iya dubar idonshi nace mishi nayi na'am dashi a matsayin mijina a gaba In Sha Allahu. Ko don son da yake yiwa Manal ai ya cancanci naso shi to bare kuma nima ďin na faďa tarkon shi tsundum, kwana biyun nan da bai waiwayeni ba ji nake yi tamkar bani da lafiya gaba ďaya na rasa kuzarina.

"Da kin daure Khadija kinyi mini magana don nasan matsayina, kinga da a sona zan yiwa Baba maganar ne kafin ya fita don anjima kaďan zan koma Abuja" da sauri na ďago na kalleshi, ban san lokacin da na ce mishi "wai har hutun naka ya kare?"

"Yayi saurin karewa ko? Nima naga saurin wucewarshi, kamar kada na tafi haka nake ji". Kunya ce ta kamani jin nayi subutar bakin yin maganar da ban shirya ba. "Kinyi shiru Khadija, bana so Baba ya fita ban samu nayi magana dashi ba".

"To kaje zan yi maka message don gaskiya kunya nake ji" nayi maganar ne a hankali tamkar mai yin raďa.

Murmushi yayi mai sauti yace "to shikenan Khadija nayi hakuri kiyi mini message ďin amma please kada ki bar ni ina jira". Ďaga mishi kaina nayi alamun "to". "Bari naje wajen Baba" yace yana mai mikewa bayan ya gyarawa Manal kwanciyarta akan kujerar.

Bayan fitar shi ne na tashi na koma ďaki. Ni me ya kaini cewa zan yi mishi message, yanzu nasan yana can yana jiran amsata. Ďaukar wayata nayi don yin composing message ďin da zan tura mishi. Ga abinda na rubuta "Special people see heart to heart even when they don't see face to face. You're indeed special to me because i always see you in my heart". Na karanta message ďin yafi a kirga kafin nayi kundunbalar tura mishi.

Yana zaune a kan carpet ďin tsakar parlour Baba yayinda Baban ke zaune akan doguwar kujera. Sallama Habib ďin keyi mishi akan tafiyar da zaiyi a yau ďin don komawa bakin aikinshi a gobe yaji shigowar message.

Da sauri ya fito da wayarshi daga cikin aljihu. Murmushi ne ya kwace mishi ganin abinda ta rubuto a message ďin. Sai yaji ta kara burgeshi ta yadda ta iya tsara kalamin da tayi amfani dashi wajen yi mishi message ďin.

Maida wayar yayi cikin aljihun shi sannan cikin kaskantar da murya yace "am Baba dama akwai maganar da nake son sanar maka". Kallonshi Baba yayi yaga yadda yake sussunkuyar da kai kamar yana gaban surukinshi.

"Umhm ina jinka" Baba yace mishi. "Um dama Baba akan yarinyar nan ne Khadija, mun daidaita kanmu don haka nake ganin ya kamata ta koma gaban iyayenta kafin ayi maganar auren, ko me ka gani?"

Gyara zamanshi yayi kafin yace "haka ne, dama kwanaki Hajiyarku tayi mini magana akan ya kamata ta koma gida haka nan kuma nima naga dacewar hakan har ma nace tare dani za'ayi tafiyar don iyayenta zasu fi yarda cewa tana hannunmu duk wannan lokacin.
Ka dai tabbata ba tilasta mata kayi ba yasa ta amince zata aureka ko?"

Da sauri yace "wallahi Baba ban tilastata ba, ita da kanta ta amince kafin na kawo maganar gabanka". Yace "to ai shikenan, idan na yanke ranar tafiyar zanyi maka magana don kaima ya kamata ace anyi tafiyar da kai".

Sunkuya yayi yace "nagode Baba, Allah ya kara girma" daga nan suka cigaba da hira irin ta ďa da mahaifi.

Na fito daga wanka kenan naji wayata na kara. Da sauri na ďauka don kada kiran ya tsinke. Yaya Habib ne yake kira, duk da har yanzu banyi saving number shi ba amma har na hardaceta a kaina.

"Hello, Assalamu Alaikum" nace bayan nayi swiping kiran. "Wa'alaikissalam, ki sameni a parlour Hajiya" yace kawai ya katse kiran.

A tsanake na shirya a cikin swiss atampar da nayi wa ďinkin doguwar rigar A shape. Hijabina na saka sannan na fita. Suna zaune tare da Hajiya, tana ganina ta tashi ta fita daga parlour. Sai naji kunya ta kamani, fatana dai Allah yasa bai sanar da ita ba don ban san ta yaya zan iya kara haďa ido da ita ba.

Zama nayi akan kujerar dana zauna ďazu sannan nace mishi "gani". "Do you really mean what you wrote in your message?" ya tambayeni. A hankali na ďaga kaina alamun amsawa.

"Wow" yace "thank you very much my dear" gaba ďaya fuskarshi ta cika da annurin farin ciki. "Yau zan koma amma In Sha Allahu babu jimawa zan dawo" ya kara faďa. "Allah ya kiyaye hanya ya kareka daga dukkanin wani abin ki dake kan hanya" na faďa cikin sassanyar murya.

"Amin Khadija, nagode" yace yana mai mikewa. "Babu rakiya?" ya faďi cikin zolaya. Dariya nayi nace "akwai amma ba yau ba".

Cikin dariya yace "oh really, to sai yaushe?" Kasa amsa mishi nayi sai murmushi kawai da nayi. "Dama nasan ba amsawa zakiyi ba, sai mun yi waya" yana faďin hakan ya fice daga ďakin ya barni da mamakin ashe dama yana magana har haka?

Taahi nayi na koma ďaki ina cigaba da karatuna sai dai lokaci zuwa lokaci tunanin Yaya Habib na zuwa cikin raina. Fahimtar ba gane karatun nake yi ba yasa na tattara na ajiye na tashi na fita kitchen don ďora sanwar rana.

UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now