BABI NA BIYU

3.6K 221 1
                                    

A tashar na samu Mustapha (abokin Yaya Adam) yace "na daďe ina jiranki", ya miko mini kuďi a cikin envelope yace "gashi inji Adam" na saka hannu na karba ba tare da na kirga ba. Ina kokarin shiga mota ne ya miko mini waya yace "ga Adam ďin zaiyi miki magana".

Ina karba Yaya yace "kina jina Khaddo? Kije Kano gidan Baba Sule wan Goggo, ai kin san gidan ko"? Nace "eh" yaci gaba da cewa "Goggon ce tace kije zata yi musu waya, ki zauna acan kafin komai ya warware, kiyi hakuri kinji, kiyi ta addu'a komai zai wuce kinji"? Nace "nagode Yaya" ina kuka. Shima kukan yake yi yace "shi kenan kada Baba yaji, zamu rinka kiranki" nace "kuma ku yafe mini na saka ku a matsala" yace "babu komai Khaddo, kaddara ce, na fahimce ki, sai nazo gobe ko jibi kinji"? Ya kashe wayar. Mikawa Mustapha wayarsa nayi na juyana shiga motar don dama ta cika ni kawai ake jira motar ta tashi.

Mota na ta sharara gudu, ni kuwa tunani nake yi "ba zani gidan Baba Sule ba, ni kaina kyamar kaina nake yi, banga laifin Baba ba ko kaďan, na san yana sona kai dukkansu ma suna sona amma dame na saka musu? Sai da tukuicin cikin shege, gaskiyar Baba ne zama na a gida ba karamin batanci zai janyowa sauran kannena ba, watakila ma su rasa miji domin na watsa kyakkyawar tarbiyyar da akayi mana".

To yanzu ina zan dosa, wacce irin rayuwa zanyi a inda na nufa, wanne irin hannu zan faďa mummuna ko kishiyarsa, waye ma zai amshe ni a halin da nake ciki da ko iyayen da suka haifeni suka gaza rikeni.

Idan dai har ba ina so na faďa cikin wata mummunar rayuwa ba to dole ne na tafi gidan Baba Sule na zauna kamar dai yadda Yaya Adam yace. Inata sake-saken zuci har muka shigo Kano daidai ana kiran Sallar Magriba, kasancewar lokaci ne na hunturu karfe shida da 'yan mintuna ake yin Sallah.

Mota ta ajiyemu a tashar Kano Line dake Na'ibawa. Fitowa nayi waje ina kalle-kalle, duk da cewa duhu ya fara sauka hakan bai hana yawaitar hada-hadar jama'a ba. Na fara takawa a hankali na nufi titi, ina tafe ina tunanin yadda zan iya kallon Baba Sule da iyalin gidanshi da irin wannan abin kunyar dake tare dani.

Ina karasawa titi na samu a daidata sahu na faďa mishi sunan unguwar da gidan Baba Sule yake wato Hausawa nace mishi nan zai kaini. Sai da ya kare mini kallon da ya saka na fara tsarguwa ina tunanin yin gaba yace mini "ďari biyar zaki baki bani don yanzu dare ya fara yi ba lallai na samu fasinja ba".

Ba tare da jinkiri ba na hau a daidaita sahun nace mishi "muje". Muna tafe gabana yana faďuwa don sai yanzu na fara dana sanin tahowata Kano don sosai nake jin kunyar kallon idon sani da abin kunyar dake tare dani. Dana sani wani wurin na nufa inda ba'a sanni ba ba'a san usulina ba na zauna har Allah ya saukeni lafiya, da ko aikatau na nema don samun abinda zan rike kaina da abinda ke cikina.

Maganar ďan a daidata sahun ce ta katse mini tunanin da nake yi yana cewa "mun shigo Hausawa, ina muka nufa"? Ďagowa nayi na kalli inda muke, gidan Baba Sule ba yada nisa daga nan don haka na hau nuna mishi hanya har muka je kofar gidan.

Cikin sanyin jiki na sauko daga cikin a daidaitar na ciro kuďinshi na mika mishi sannan na juya na nufi cikin gidan zuciyata tana wani irin bugu tamkar ta faso kirjina ta fito. Na saka kai na shiga cikin gidan bakina ďauke da sallama. Hasken lantarki ya haske ilahirin tsakar gidan tamkar rana.

Hajiya dake zaune a kan babbar tabarmar dake shimfiďe a kan barandar dake gaban ďakunan gidan ta saukar da ajiyar zuciya tace "Alhamdulillah, hala matsalar mota kuka samu don a yadda Adamu ya sanar damu yace tun wurin biyar ya kamata ku karaso garinnan. Shima hankalinshi ba'a kwance yake ba don sai waya yake yi yaji ko kin karaso".

Kan tabarmar na hau na zauna sannan na russuna na gaisheta ina sussunkuyar da kai tamkar wata munafuka. Bata tsawaita gaisuwar ba ta kwalawa Humaira kira, daga cikin ďaki ta amsa kiran kafin ta fito tace "Hajiya gani". Tana ganina fuskarta ta yalwatu da fara'a tace "ashe Khadija ta iso, sannu da zuwa, lallai kin sha hanya".

Ni dai yake kawai nake yi. Hajiya ce tace "jata kuje ďakinki Humaira tayi wanka tayi sallah sai ki kai mata abinci". "To" Humaira tace tana mai kamo hannuna, mikewa nayi na bita zuwa ďakinta. Muna shiga ta wuce banďaki ta haďa mini ruwan wanka ni kuwa sai kalle-kalle nake yi.

Duk da ba yau na fara zuwa gidannan ba amma kullum na shigo ďakin Humaira zama nake yi 'yar kauye don yadda nake sakin baki ina bin ďakin da kallo. Ba wani tarkace bane a ďakin illa karamin gadon da baifi ya ďauki mutum biyu ba kirar Dubai kalar pink da ratsin fari a jiki sai wardrobe ďinshi mai kofa biyu da madubi, shi kuma ďakin wallpaper ce aka bi dukkan bangon ďakin da ita kalar lilac mai ďauke da zanen kananan furanni masu ban sha'awa. Sai shoe rack mai ďauke da ďima-ďiman takalma da bag hanger ďin da aka cika da jakunkuna tamkar a shago. Ďakin 'yar gata dai.

Fitowa tayi daga banďakin tana ce mini "gashi can na haďa miki ruwan wanka ki shiga kiyi, ni bari naje wurin Hajiya kafin ki fito". Ďaga mata kai nayi nace "nagode" sannan na wuce banďakin. Nayi kusan minti biyar a tsaye a banďakin ba tare da na cire kayan dake jikina ba. Kiran Sallar Isha'i na jiyo daga wani masallaci anan kusa, abinda yasa na tuba cewa ko Sallar La'asar banyi ba bare Magriba gashi har Isha tayi.

A gaggauce na hau cire kayan jikina, tsayawa nayi a gaban madubin banďakin ina karewa shafaffen cikina kallo ian tunanin yanzu wai nan ďane a kwance a marata, kuka ne ya kwace mini. Durkushewa nayi anan kasan banďakin ina kuka ina cewa "ka yafe mini babyna, banyi maka adalci ba dana samar da kai ta kazamtacciyar hanya. Ba'a son raina hakan ya kasance ba, kaddara ce ta faďa mini wacce bawa bai isa kauce mata ba".

Sai da nayi kukana ma'ishi sannan na tashi nayi wankan tare da ďauro alwala na fito. Akan gadon naga kayan dana tabbatar ni Humaira ta ajiyewa. Goge jikina kawai nayi na ďauki doguwar rigar atamfar data ajiye mini na saka ba tare dana tsaya shafa mai ba sannan na zura hijabina na tada Sallah.

Bayan na idar da dukkanin Sallolin da ake bina na ďaga hannu ina neman gafarar Ubangiji akan laifin da son zuciya ya kaini ga aikatawa. Na tashi daga kan sallayar kenan ina naďewa Humaira ta dawo ďakin hannunta ďauke da flask ďin abinci. "Kin idar da sallar kenan, ai na shigo naga baki idar ba shine na koma" tace tana mai ajiye kayan abincin data shigo dasu akan rug ďin dake shimfiďe a tsakar ďakin. "Hajiya tace na tabbatar kin ci abinci sosai don haka zo ki zauna ko nayi miki ďura" tace cikin yanayi na tsokana.

Murmushin da bai gama cika fuskata ba nayi kawai na zauna ba tare dana tanka mata ba. Wallahi sam bana jin yunwa don gaba ďaya cikina a cushe nake jin shi. Rabona da abinci tun karyawar safe kuma ko da wasa banji ina jin yunwa ba.

Caccakalar abincin kawai nayi na ture gefe, kallon plate ďin tayi taga ba wani abin kirki naci ba tace "amma dai ba wai kina nufin kin koshi ba ko"? Nace mata "umh" tace "ban san miye matsalarki ba Khadija amma kowa ya ganki yasan kina cikin damuwa, sai dai bacin rai da bakin ciki ba shine abinda zai hana miki cin abinci ba. Ko miye yake damunki hakuri zakiyi kiyi ta addu'a sai kiga ya wuce miki tamkar ma ba'a yi ba. Don haka ki daure ko yaya ne ki kara abincin tunda zama ba zai warare miki matsalarki ba".

Ďaukar plate ďin nayi na kara abincin da bai fi loma biyar ba na ajiye don bana jin daga haka zan iya kara wani abu a cikina. Muna zaune a ďakin munyi zugum, har Humaira ta gama cin abincin ta tattare kwanukan ta fita dasu sannan ta dawo tace mini "Hajiya tace ki sameta a ďakinta".

Tashi nayi muka fita tare, ita ta tsaya a parlour ni kuma na wuce uwar ďakin Hajiya. Da sallama a vakina na shiga ďakin. Ta amsa mini sallamar ba tare da ta ďago ta kalleni ba, ganin haka da nayi yasa jikina ya kara yin sanyi. Zama nayi a kasa akan carpet ďin dake shimfiďe a tsakar ďakin nace "Hajiya gani Humaira tace kina kirana".

UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now