BABI NA GOMA SHA BIYU

2.7K 201 9
                                    

A GAREKU 'YANUWANA, KAWAYENA DA ABOKAN ARZIKINA NA DUKKANIN GROUPS DA NAKE CIKI DAMA WAĎANDA BANA CIKI, NAGODE SOSAI DA ADDU'O'INKU GA MAHAIFINA, ABBAH YANA SAMUN LAFIYA SOSAI. ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI YA BAR ZUMUNCI YA BARMU TARE HAR A GIDAN TSIRA JANNATUL FIRDAUS. AMEEN.

A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah don kuwa gashi yau na samu watanni biyu cif a gidan Baba Sule, cikin jikina kuma yana da watanni huďu. Bazance bani da damuwa ba domin kuwa idan na faďi hakan karya ce kawai nake yi sai dai yanayin zamana a gidan na Baba Sule na babu tsana bare tsangwana ya gaftare kaso mafi girma daga damuwar dake cikin raina.

Don kuwa babu dama Hajiya taga na ware kaina a gefe da sunan yin tunani ko wani abu makamancin haka yanzu ne zakuji tana faďa tana cewa "ashe ban hanaki ware kanki daga cikin mutane kina zama kina tunane-tunanen da ba zasu haifar miki da komai ba sai cuta, ashe bazaki yarda da kaddara ba Khadija? Abinnan fa ya riga ya faru sai dai a kiyaye gaba tunda yawan tunani da koke-koken da kike yi bazai goge abinda ke tare dake ba, to don miye ba za kiyi hakuri ba ki rungumi kaddararki ko don lafiyar abinda ke cikinki da bai san hawa ba bai san sauka ba".

Ire-iren waďannan maganganun na Hajiya ne ke hanani zama ina tunanin makomar rayuwata bayan na haihu, dole nake warewa na hana kaina zaman kaďaici duk da koyaushe Humaira tayi mini sallama da zummar ta tafi makaranta sai naji kwalla ta cika idanuna don nasan idan banda hakan ta faru da yanzu nima ina cikin school ina ďaukar karatu da shirin zana jarabawar fita, don dole nake haďiye kukana tunda nasan ko miye ya faru dani ni na janyowa kaina.

Yau mun tashi da aiki kasancewar babban ďan Hajiya kuma Yaya guda ďaya jal a wurin Humaira zai shigo gari. Ni da Humaira ke da alhakin kula da abinci don haka tun bayan da muka yi breakfast muka shiga kitchen. Tuwon alkama muka yi da miyar ďanyar kubewa don Humaira tace shine abinci mafi soyuwa a wurinshi sai farar shinkafa da miya sai kuma haďin salad da drink ďin da muka haďa da farin zoborodon da muka dafa shi haďe da na'a-na'a wato mint leaves da kayan kamshi sai sugar ďan dai-dai da muka zuba a ciki muka sanya a fridge don yayi sanyi kafin bakon ya karaso.

Sai kusan karfe sha biyu muka gama haďa abincin don haka muna gamawa na shiga wanka don ba karamar gajiya nayi ba, ko don na daďe banyi aiki irin haka bane ya saka shine ban sani ba. Bayan na fito ne na shirya a cikin buďaďďiyar doguwar rigar atamfar Holland Batik.

Kasancewar na ďauro alwala ya sanya ban zauna ba sai na shimfiďa sallaya na sallaci nafila raka'a huďu sannan na bada faralin sallar azuhur. Bayan na idar ne na naďe sallayar haďe da hijabin da nayi sallar na ajiye a gefe na haye kan gado don kuwa sosai nake jin bacci. Ina ďora kaina akan pillow kuwa baccin ya ďaukeni don bana jin na idasa addu'ar kwanciya bacci dana fara.

Sama-sama a cikin bacci naji Humaira nace mini "bacci kike yi Khadija? Kenan ba zaki iya fitowa ku gaisa da Yaya ba?" Hannu kawai na ďaga mata na koma bacci. Bani na tashi daga baccin nan ba sai karfe huďu da rabi shima kuma yunwa ce ta tashe ni.

A daddafe na faďa toilet na yiwo alwala nazo nayi sallah. Ina idarwa na fita kitchen don neman abinci, ban koma ďaki ba sai na tafi ďakin Hajiya don nasan a can zan samu Humaira. Ina shiga tace mini "kin tashi kenan?" Harararta nayi sannan nace "kin ce haka mana bayan baki tashe ni ba har sai da yunwar cikina ta tashe ni don dole".

Dariya tayi tace "ai kinga kin tashi dole da yake yunwa ce ta tashe ki ita da ba'a sha mata La Haula, ni wane irin tashi ne banyi miki ba kika ki tashi sai yanzu zaki zo kina mini mita, har cewa nayi ki tashi ku gaisa da Yaya amma kika ki" ta karashe maganar tana turo mini baki.

Dariya ma ta bani ganin yadda take abu kamar wata karamar yarinya. "Ayya ban jiki ba wallahi, bacci ne sosai a idona. Amma babu komai In Sha Allahu ai zamu gaisa ne" nace mata. "Haka ne kam" itama ta faďa.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now