BABI NA HUĎU

3.2K 232 2
                                    

A gigice ta shigo gidan tana kwaďa sallama tun daga soro. Umma dake kwasar tuwo a madaidaicin kicin ďin dake tsakar gidan ta amsa sallamar da Saratun tayi ta kara da cewa "ke kuma lafiyarki kika shigo mana gida kamar wacce aka koro". Saratu ta saki ajiyar zuciya tace "lafiya ba lau ba Umma, wani labari mara daďin saurare Adamu yaje yana sanar mini. Garin yaya haka ta faru Umma, da gaske ne Baba ya kori Khadija? Saboda Allah yanzu ina zata? Bakwa gudun ta faďa cikin wata mummunar rayuwar Umma? A gaskiya ni dai ban ji daďi ba sam".

Da ace Saratu ta lura da yanayin fuskar Umma da tun lokacin da ta fara magana ta ďinketa tamkar bata taba fara'a ba da bata cigaba da maganar ba amma sam hankalinta bai kai nan ba abinda ke cikin ranta kawai take faďi. "Ai Umma idan rai ya baci hankali baya gushewa, duk lalacewar Khadija taku ce bai kamata ace kun haďu ke da Baba kun yanke wannan ďanyen hukuncin a kanta ba tunda inda ta tafin ba'a san wacce irin rayuwa zata yi a can ba, duk abinda Khadija ta zama a gaba Umma kune sanadi haka nan kome ta zama dole a dangantata daku, to irin haka ina..."

"Keee" Umma ta daka mata tsawa tace "ki kiyaye ni kina jina ko, idan har kina son kanki da arziki kada ki kara zuwa gabana da zancen Khadija, ni nan da kike ganina na tsameta daga cikin ahalina. Tunda irin rayuwar data zabarwa kanta kenan taje tayi tayi babu abinda yayi wa Sakinatu zafi, tunda kinyi abinda ya kawoki sai kizo ki wuce ki tafi gidanki".

Saratu da hawaye ya wanke mata fuska da jin maganar da Umma ke yi tace a cikin muryar kuka "kiyi hakuri Umma tunda ba kya son zancen Khadija In Sha Allahu bazan kara tayar miki dashi ba" ta saka gyalenta ta goge hawayen dake ta faman sunturi akan fuskarta tace "Goggo bata nan ne tunda na shigo ban ganta ba".

A ďakile Umma tace "eh ta shiga can wajensu Hajiya ta dubata don tayi fama da zazzabi kwana biyu". "Allah sarki Allah ya bata lafiya idan na samu lokaci naje na dubata, bari na koma gida Umma nasan yanzu yara sun taso daga islamiyya idan Goggon ta dawo a gaisheta", "to" kawai Umma tace don sosai Saratu ta bata mata rai da zancen Khadija da tazo mata dashi duk da har yau ta kasa yardarwa da zuciyarta wai Khaddonta ce ta iya aikata wannan mummunan laifin.

*****

Cikin bacci naji Humaira tana tashi na "Khadija ki tashi kiyi sallah fa don uku ta kusa". A hankali na buďe idanuna na saukesu akan agogon bango mai fuskar mickey mouse kalar pink dake manne a bangon ďakin. Karfe uku saura minti biyar agogon ya nuna.

Da hanzari na mike daga kwancen salati ďauke a bakina ganin yadda lokaci yaja, lallai na jima ina bacci. Sauri nayi na dafa Humaira don ji nayi jiri yana neman kayar dani. "Sannu Khadija, baki da lafiya ne naga kina neman faďuwa?" Girgiza kaina nayi nace "a'a lafiyata kalau, watakila baccin da nayi ne yasa jikina ya saki".

Banďaki na wuce na ďauro alwala sannan na fito na sallaci azahar, ban tashi daga wurin ba har sai da nayi sallar la'asar ganin lokacintq yw riga yayi. Bayan na idar ne naje na gaida Hajiya sannan na dawo ďaki inda na tarar Humaira ta shirya mana abinci tana jirana.

Zama nayi na saka hannu a cikin abincin muna ci don sosai nake jin yunwa, har muka kammala cin abincin Humaira ta tattare kwanukan ta fita dasu babu wanda ya tanka a cikinmu. Tashi nayi na koma kan gadon na kishingiďa don yanzu bqbu abinda nake jin daďi irin kwanciya.

Kallona Humaira ta tsaya yi bayan dawowarta đakin. "Ba dai bacci zaki koma ba?" tace mini. Murmushi nayi nace "haba dai bacci yanzu da yammar nan kawai dai na gaji ne shine na kwanta", "iyye kaga 'yar hutu, to aikin me kika yi da zaki gaji ke da tun barina gidannan kike bacci hqr na dawo baki tashi ba shine zakice wai kin gaji. Hmm Allah ya sanya mu a danshinki" tace a cikin yanayi na tsokana.

Tsaki kawai nayi nace "kya ji dashi". Dariya tayi tace "ai kuwa dai kwanciya bata ganki ba don Hajiya ta aikemu can bayan layi". Tashi nayi zaune ina cewa "kai amma naji daďi har na motsa kafafuna don dama na gaji da zaman wuri ďaya bana aikin komai".

Zama tayi a gaban mudubi tana kwalliya ni kuwa sai aikin kallonta nake yi. Ta juyo ta kalleni tace "ba zaki ďanyi makeup ďin bane Khadija?" Na mike zaune nace "bari dai na ďan shapa powder amma ni kwalliya ba damuna tayi ba".

Murmushi tayi tace "kodayake ma ai ko bakiyi kwalliya ba aje dake, don your beauty is natural, kin haďu sosai Masha Allah". Na harareta nace "zaki fara ko, a dai rika godewa Allah Humaira ke da kike fara ma tas ni kuwa chocolate ak kyau yana wurinki".

Tace "ai baki sani ba Khadija ni farar fata bata birgeni, shi yasa ma ban taba yin saurayi fari ba. Ai da ace akwai man mayar da farare baki da tuni na shiga kanti" ta karasa faďi cikin dariya. Nima dariyar nayi sannan nace "gara ki tashi mu tafi aiken da Hajiya tayi mana kin zauna kina zuba zance".

Ashe gidan telar dake yi musu ďinki ne Hajiya ta aikemu mu kai mata atamfofin da Hajiyar ta bani ta ďinka mini ganin ban taho da kayana ba tunda tafiyar tawa ba ta shiri bace.

Tunda muka fita Humaira ke waya da saurayinta har muka je gidan telar sannan suka yi sallama haka nan muna fitowa taďora daga inda ta tsaya. Ni dai kallonta kawai nake yi ina mamakin irin zurfin da tayi a cikin soyayyar da babu komai a cikinta sai zallar karya da yaudara da ha'inci. Maza a yanzu ai ba abin yarda bane.

Kwanana uku a Kano Yaya Adam yazo. Sosai nayi murna da ganinshi don ko da yace mini zai zo na ďauka faďa kawai yayi don ya kwantar mini da hankali ban taba kawowa zan ga wani nawa a kwana kusa ba. Ina ganinshi abinda na fara tambayarshi shine yasu Umma. Sosai nake cikin kewar Umma don akwai shakuwa mai yawa a tsakanina da ita.

Yaya Adam na zaune a parlour Hajiya yana cin abincin da na kawo mishi ni kuma ina zaune a kujerar dake kusa da wacce yake zaune a kai ina jira ya kammala cin abincin. Bayan ya gama ne ya miko mini wayata yace "ita kaďai na iya ďauko miki don bana so su Umma su san cewa na san inda kike, wayar ma Goggo ce ta bani don tace a ďakinta kika barta sai dai na canja miki layi idan kin kunna zaki gani. Ina fatan dai baki da wata matsala?"

Kwalla ce ta ciko a idanuna na saka hannu na share nace "Yaya matsala kam ai kasan a cikinta nake tunda nayi sanadin bacin sunanku a gari, don Allah Yaya ku yafe mini wallahi tsautsayi ne ya kaini ga aikata hakan".

Ďaga mini hannu yayi yace "maganar nan ta isa haka Khaddo bana sonta, kada ki damu kanki ni nasan kaddarace ta afka miki amma ai kowa zaiyi shaidarki da cewa lalacewa ba halinki bane suma su Umma bacin rai ne ya saka su yanke hukuncin da suka yi a kanki amma na tabbata duk ranar da suka huce da kansu zasu nemeki. Abinda kawai nake so dake shine ki kwantar da hankalinki know  kama mutuncinki don Allah kada kisa su Baba Sule da Hajiya suyi dana sanin karbar ki da suka yi. Ki daure ki cire komai daga ranki In Sha Allahu komai zai wuce ya zama labari kinji?"

Bayan tafiyar Yaya Adam ne na kunna wayata wacce Faruk ne ya bani a zuwana gida wancan hutun wai gift ne na tayani murnar karbar kyautar ďaliba mafi kwazo (overall best)  a cikin set ďinmu da nayi. Hotuna na buďo ina kallon hotunan Faruk da suka cika wayar.

Na tsaya akan wani hotonmu ni dashi da ya ďauke mu a ranar da ya kawo mini wayar anan a tsakar gidanmu. Ina sanye ne da atamfar cote d'ivoire  a jikina kalar brown mai haske da mai duhu sai farin hijabi da nayi amfani dashi, shi kuma a sanye yake da jeans kalar blue sai shirt ja mai dogon hannu da ďigo-ďigon baki a jikinta.

Ina tunawa da kyar na iya tsayawa ya ďaukemu hoton saboda kunyarshi da nake ji don har sai da ya nuna bacin ranshi sannan na tsaya ya ďaukemu hoton, sai kuma ya kasance hoto mafi soyuwa a gareni a duk cikin Hotunan dake cikin wayata. Kullum ne sai na buďe hoton na kalla don har taba gaya mishi nayi cewa idan lokacin aurenmu yayi wannan hoton nake so ayi amfani dashi wurin buga kalanda.

Kuka ne ya kubce mini na kwanta ina rera shi a hankali, wai kuma don abin haushi na kasa ďauke idona daga kan hoton Faruk abinda ke kara tura kukan da nake yi. Tunda abinnan ya faru nake kokarin cusa wa zuciyata tsanar Faruk banci nasara ba sai yanzu da naga a halin da ya jefa ni a ciki ya gudu ya barni.

UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now