BABI NA GOMA SHA HUĎU

2.5K 179 2
                                    

Ina idar da sallar la'asar na tashi na shirya a cikin atamfar Mitex Holland ďinkin plain zani da riga three quarter mai zanen manyan ganye kalar dark green and orange. Farin hijabi na saka sai flat slippers ďin vine shima fari dana saka a kafafuna.

Ďakin Hajiya naje na iske itama ta gama shiryawa don haka ko zama banyi ba muka fita. Wani private hospital muka je anan cikin hausawa don bayada nisa daga gidan don haka ma a kafa muka tafi.

A teburin receptionist muka tsaya. Hajiya ce ta bada details ďina ta buďe mini folder. Bayan an buďe folder ne ta nuna mana kujera tace mu zauna sannan ta wuce da folder tawa zuwa ofishin likitan.

Bamu daďe a zaune a wurin ba ta fito tace mana mu shiga. Tare da Hajiya muka shiga ganin likitan don haka ita ta sanar dashi abinda ya kawo mu. Sai da ya ďauki b.p ďina sannan ya nuna mini siririn gadon dake ďakin yace mini na kwanta.

Gabana ne naji yayi mummunan faďuwa. A take jikina ya fara rawa. Hajiya ce ta lura da hakan don haka tace mini "tashi mana Khadija, kina bata mishi lokaci". A cikin sanyin jiki na tashi na hau kan gadon na kwanta akan hannuna na dama kamar mai kwanciya bacci. Murmushi yayi har yana fitar da sauti yace "akan bayanki zaki kwanta ki ďaga rigarki".

Da sauri na kai dubana wajen Hajiya. Ďaga mini kanta tayi alamun nayi yadda yace don haka na juya nayi rigingine tare da ďan ďaga rigata. Hannu ya saka ya janye rigar sosai sannan ya hau latsa mini ciki, ni dai runtse idona kawai nayi don ba son abinda yake yi mini nake yi ba sai don babu yadda zanyi, dama da don tani ce babu asibitin da zani to don dai Hajiya ce tace ni kuma bazan taba iya yi mata musu ba.

Yana cewa na sauko nayi maza na diro daga kan gadon don dama tamkar akan kaya haka nake jina. Komawa nayi kujerar dana tashi na zauna, shima likitan ya koma kujerarshi ya zauna sannan ya ďauko lab request form ya cike ya mikowa Hajiya yana yi mata bayanin cewa muje ayi teats ďin da ya rubuta a jiki da kuma scanning, bayan sati huďu sai mu dawo.

Godiya Hajiya tayi mishi sannan ta mike nima na tashi muka tafi. Sai da muka tsaya muka jarbi magungunan da likiran ya rubuta mini Hajiya ta biya sannan muka tafi. Har muka je gida jinjina karamci irin na su Hajiya da Baba Sule nake yi.

Duba dai kuga a cikin halin da nazo musu amma suka saka hannaye biyu suka karbeni suka yi mini abinda iyayen da suka haifeni basu iya yi mini ba suka kuma rikeni tamkar 'yar cikinsu babu tsana bare tsangwama duk da abin kunyar dake jikina sai ma wani tattalina da suke yi suna tattalin lafiyata data abinda ke cikina. Ni kuwa a rayuwa ai babu abinda zanyi na iya saka musu alkhairin su a gareni sai dai nayita yi musu addu'ar gamawa da duniyar nan lafiya da fatan cikawa cikin imani.

Haka na cigaba da rainon cikina cikin koshin lafiya, duk ranar da zani antenatal Hajiya ke rakani haka nan idan akwai test ďin da zanyi ita ke kaini lab nayi sannan mu dawo gida har cikina ya shiga watan haihuwa.

Babu abinda Hajiya bata tanada ba na daga kayan haihuwa sai jiran lokacin haihuwar kawai. A kullum na kalli kaina naga yadda cikin jikina yayi girma sai naji wani abu ya tokaren zuciyata ba don ina bakin ciki da kyautar da Allah yayi mini ba sai don ina bakin ciki da yadda na samar da abinda ke cikina duk da cewa ba karamin son abinda ke cikin nawa nake yi ba tun ma kafin na sakashi a idona to inaga kuma ranar da nayi tozali dashi wato ranar da zai ziyarci duniya.

A yau asabar tun bayan dana idar da sallar asuba nake fama da ciwon mara dana baya kaďan-kaďan ina kannewa ban bari kowa ya fahimta ba, sai ma zamana da nayi a ďaki naki fitowa. Da kaďan-kaďan ciwon ya dinga karuwa amma har wannan lokacin ban yarda kowa ya sani ba.

Zuwa lokacin sallar azahar ciwo ya taho gadan-gadan. Kafin kuce miye wannan nayi biji-biji dani don azaba. Hajiya ce ta leko ďakin don ta duba ni dama kuma haka take yi kullum cikin shigowa take don ta duba lafiyata har cikin dare kuwa, ganina da tayi inata faman matagugu ne yasa ta fice daga ďakin da sauri ta shiga ďakinta tana cewa Humaira "maza kira mini Yayanki a waya don yanzu nan ya bar nan nasan baiyi nisa ba ya taimaka yazo mu kai Khadija asibiti, ashe yarinyar nan nakuda take yi amma tayi shiru bata faďa ba ta kuma yi zamanta a ďaki tana fama da ciwo ita kaďai".

A ruďe Humaira ta danna wayar ta kira Habib. Tana jin ya ďauki wayar ta fara yi mishi bayanin dalilinta na kiranshi ba tare da ta bari yayi magana ba,da dai ta tabbatar yaji abinda tace sai ta katse kiran. Ba'afi mintuna biyar ba kuwa sai gashi ya shigo cikin gidan.

A ďakin Humaira ya tarar dasu, suna ganinshi suka mike. Hajiya ta kamo Khadija dake ta faman mirgina kai saboda azabar ciwo ko addu'ar ma bata iya yi suka fita. Humaira kuma ta biyo su da akwatin da suka shirya don tafiya asibiti.

A cikin mota ma sai faman sannu Hajiya da Humaira suke yi mini. Har muka isa asibitin, muna fito daga cikin motar ne zamu shiga cikin asibitin naji Yaya Habib na cewa Hajiya "ai zan iya tafiya ko?" Wani irin kallo ta watsa mishi sannan tace ban gane da zaka iya tafiya ba idan kuma muna da bukatar ka a kusa fa, sai an kira ka?"  "Kiyi hakuri Hajiya, bari na gyara parking sai na fito" yace mata.

Muna shiga Hajiya ta sanar da nurse ďin da muka iske a reception ďin cewa mun zo haihuwa ne. Tambayarta tayi number file ďina ta mika mata karamin kati na ita kuma ta duba number sannan ta ďauko folder ta shiga consulting room dashi.

Tana fitowa ne tace mu shiga. Hajiya ta kara tarairayo ni muka shiga ďakin ganin likitan. Muna shiga yace wa Hajiya ta ďora ni akan gadon dake ďakin. Da taimakon Hajiya na hau kan gadon na kwanta.

Hand gloves ya saka sannan yazo ya tsaya a kaina yana ce mini wai na gyara zaiyi mini V. E wato vaginal examination. Duk da halin ciwon da nake ciki ban san lokacin dana galla mishi harara ba sannan nace "ashe kuwa sai dai idan a fasa haihuwar idan har sai ka duba ni sannan zan haihu to kuwa na fasa, ďan yayi ta zama a cikin bana so".

Duk sanyin Hajiya sai da ranta ya baci da jin abinda nace don haka cikin faďa-faďa tace mini "Khadija ki kiyayeni fa, kina nufin bazaki bar shi yayi aikinshi bane ko me? Zaki gyara ya duba ki ko sai kinga bacin raina tukunna?"

Babu shiri na tsaya yayimini V. E ďin. Inaji yana gayawa Hajiya cewa na kai 8cm don haka a wuce dani labour room don gaf nake da haihuwa.

Bamu fi mintuna talatin da shiga ďakin haihuwar ba na sullubo 'yar kyakkyawar ďiyata mai kama dani sak don babu ta inda ta ďauko Faruq sai ta hasken fata don kuwa yarinyar fara ce tas.

Nurse ďin da ta karbi haihuwar na gama shirya yarinyar ta miko mini ita waina gwada bata nono. Da taimakonta na sakawa yarinyar nono a baki, ina kallon yadda ta kama tana zuka duk da babu ruwa a lokacin.

Hawaye ne ya sulmiyo daga idanuna, kallon yarinyar kawai nake yi ina jin wata irin kaunarta tana ratsa dukkanin sassan jikina. Karbarta nurse ďin tayi ta fita da ita wajen su Hajiya sannan ta dawo tace mini na tashi na shiga bathroom nayi wanka.

Tashi nayi na shiga wanka ina cigaba da zubar da hawaye. Bayan na gama wankan na shirya aka kaini ďakin da zan zauna kafin likita ya dubamu ni da baby.

Ina shiga ďakin Hajiya ta taso ta rungumeni tana ce mini "sannu Khadija" na gyaďa kai don haka nan naji na kasa buďe baki nayi magana. Humaura ma sannun take yi mini. Akan gadon Hajiya ta zaunar dani sannan ta haďa mini tea a cikin katon kofi ta miko mini.

Ina gama shan tea ďin Hajiya tace mini "karbi yarinyar ki sake gwada mata nonon". "To" kawai nace sannan na kalli wajen da Yaya Habib yake a zaune don tun shigowata naga baby ďin a hannunshi ya kamata ya rungume.

Tasowa yayi ya miko mini baby sannan ya fita. Kara gwada mata nonon nayi, cikin ikon Allah har ruwan ya fara zuwa don haka ta kama tana ta sha kamar wacce ta shigo duniyar da yunwa.

Tana cikin sha tayi bacci don haka tana gamawa Hajiya ta karbeta ta kwantar da ita.

Ba'a sallame mu ba sai da dare. Zuwa wannan lokacin munyi magana da Yaya Adam da Goggo a waya don Yaya Adam yace mini ma zai zo ya duba mu nida baby. A lokacin ne nake tambayar shi "har yanzu Umma bata nemana ko Yaya, har yanzu fushi take yi dani? Nima fa nayi nadamar abinda na aikata, kai har na bar duniya bazan daina dana sanin biyewa son zuciyata ba." Ina maganar ne cikin kuka.

Lallashina yayi tayi har ya samu nayi shiru sannan yayi mini sallama akan cewa yana nan zuwa a cikin satin.

UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now