BABI NA TAKWAS

2.5K 185 12
                                    

Soyayyarmu da Faruq ta kankama tamkar mun daďe tare, ni kam ma dai abin har mamaki yake bani yadda na shaku da shi a cikin ďan kankanin lokaci irin wannan. Kowa dake gidanmu yasan abinda ke tsakani na dashi don kusan kullum ne sai yazo wurina.

Duk lokacin da yazo kuma zai shigo har cikin gida ya gaida su Goggo haka nan yayi ta jan su 'yan biyu da Bilkisu da wasa, sosai yaran suka saba dashi don kullum ne sai ya kawo musu tsarabar kayan lashe-lashe shi yasa yaran suke murnar ganinshi har kiji duk ranar da yayi lattin zuwa suna cewa yau Yaya Faruq bai zo ba ko lafiya?

Yanzu ma dai a zaune nake a ďakin Umma ina tsantasar wa fuskata kwalliya don Faruq yace mini zai zo, abinda sam da bai dameni ba kenan ada wato kwalliya amma haďuwata da Faruq yasa na koya duk don dai na burgeshi.

Wani swiss lace ďina da Aunty Saratu ta bani kwance kalar blue mai zanen fulawoyi kalar pink a jiki na ďauko na saka na fesa turaren Zandaria a dukkanin jikina sannan nayi kyakkyawan ďaurin ďankwalin da ya rufe mini kaina sai na ajiye hijabina kalar pink a gefe ina jiran isowar Faruq. Babu jimawa kuwa na jiyo muryarshi a tsakar gida yana gaisawa dasu Goggo.

Umma ce ta shigo ďakin, kallona tayi ta kawar da kai sai kuma dai tace mini "duk wannan kwalliyar wa Faruq ďin kika yi?" Sunkuyar da kaina nayi ina mai jin kunyar Umma don nasan bata cika son irin waďannan al'adun ba na idan saurayi zaizo zance sai anyi wani sabon wanka da kwalliya anyi wasu uban girke-girke duk a zuwan saurayin akayi wa to nima dai ban ďaukarwa kaina yin wani girki ba amma dai a ganina mutum yazo ya iskeka tsaf ba wai ace duk shigar dake jikinki ba a lokacin da yazo da ita zaki fita.

Bilkisu ce ta shigo tace mini naje Yaya Faruq na kirana. Hijabin da dama na feshe da turare tuni na ďauka na saka sannan na saka flat takalmi na fita. A ďakinsu Yaya Yusuf dake soron gidanmu muke zama don yin hira.

Da sallama a bakina na shiga. Sai da ya sakar mini kayataccen murmushin da a duk lokacin da yayi mini irinshi sai naji dukkan gabban jikina sun mutu kafin ya amsa sallamar tawa, ban sani ba ko ya lura cewa yana mini illa da wannan murmushin nashi ne ya saka yake mini shi oho.

Zama nayi daga gefen katifar su Yaya dake shimfiďe a tsakar ďakin shi kuma yana zqune akan kujera guda ďaya tal dake ďakin. "Ina yini" nace mishi ina mai sunkuyar da kaina. "Come-on baby ďago kanki ki kalleni bana son kina gwada mini wannan kunyar taki wallahi tana cutar dani, yanzu fa idan kika koma school gobe bazan kara ganin kyakkyawar fuskarki ba har sai nan da 1 month wato ranar visiting ďinku" ya faďi maganar cikin wata irin kasalalliyar murya.


A kunyace na ďago kaina ina murmushi cikin shagwaba nace "har yanzu fa baka amsa gaisuwata ba, Allah zanyi fushi" na juyar da fuskata ina kallon gefe tamkar dai nayi fushin da gaske.


"Awwwn baby kada kiyi fushi mana kema kinsan kallon beautiful face ďinki yana mantar dani komai amma idan banda haka me zai hanani amsa ki, to lafiya lau na amsa shikenan. Please juyo da fuskarki ki kalleni ifan baso kike yi na zauce ba". Juyowa nayi ina murmushi nace "kaga nima na rama, don kqnq yon maganar komawa school ďinnan sai naci raina ya baci don wallahi bana son rashinka a tare dani ko na second guda ne amma yaya zamuyi karatu dole ne" na karashe maganar ina mai goge kwalla don haka nan naji bana son komawa makaranta domin kuwa nasan kewar Faruq sai ta dameni. Tun yanzu na fara jin ina kewarshi, ban taba jin tsanar boarding school ba irin yau, watakila dana tsaya a day da duk haka bata faru ba da zan dinga ganin Faruq ďina a duk lokacin da naso yanzu kuwa daga visiting day sai visiting day sai kuma lokutan hutu.


Saukowa yayi ya tsugunna a gabana yana cewa "haba mana baby kada ki kara ďaga mini hankali mana, a haka ma fa dauriya ce kawai nake yi don bana son na tayar miki da hankali ne amma wallahi duk lokacin dana tuna zaki koma school gobe sai naji gaba ďaya raina ya dagule to amma kamar yadda kika ce ne karatu ya zama dole don haka dilenmu muyi hakuri, In Sha Allahu dai kina gamawa zan ďauke ki zuwa gidanki idan yaso kya cigaba da karatun a gidanki idan kuma babyna yazo to..." ya karashe maganar yana mai kanne mini ido ďaya. Kunya maganarshi ta bani a lokaci guda kuma ta saukar mini da farin ciki don kuwa nima tun haďuwata dashi bani da mafarki sai na kasancewata mata a gareshi.


A haka dai hirar tamu ta kasance har akayi kiran sallar magriba kasancewar zuwan yamma yayi don Baba ya faďa mishi cewa baya son zancen dare gara da rana ido na ganin ido.


Bayan munyi sallama ne na shiga gida shi kuma yace mini zai shiga masallaci daga nan zai wuce gida. Ina shiga gida buta na đauka don yin alwala, ban tashi daga wurin ba yaro ya shigo da sallama hannunshi ďauke da katon kwali ya ajiye a tsakar gidan yace "gashi inji Faruq yace a bawa Khadija" tsayawa nayi kawai ina kallon yaron don nama rasa me zance.


Goggo ce ta amsa mishi da cewa "to angode kaji gashi kasha alawa" ta mika mishi naira hamsin ďin data kunto daga hannun zaninta. Ni dai tashi nayi na shige ďaki na tada sallah.  Ina jin Goggo tana cewa "idan banda sakarci irin na Khaddo kuma kyayi shigewarki ďaki ki bar kayan a nan wurin, to waye kika barwa da zai ďauke miki?"


Sai da na idar da sallah sannan na fita na shigo da kwalin da da kyar na ďaga shi don nauyi na ajiye. Ban buďe naga miye a ciki ba har sai da Baba ya dawo Umma ta nuna mishi kayan tukunna. Provision ne tun daga kan cornflakes, madara, milo, sugar, assorted biscuits da chocolates a ciki, harda su sabulan wanka da shampoo set na head and shoulders sai turaren jiki guda biyu samfurin ladies.


Dile na rage wasu kayan a gida don kuwa Baba yayi mini sayayyar kayan masarufi tuni don har na haďasu cikin akwatina. Washegari da safe na shirya na koma makaranta a cikin zangon mu na biyu a aji ďayan babbar secondary, sai dai na tafi ne da kewar Faruq a cikin zuciyata.

UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now