BABI NA TALATIN DA BAKWAI

4.8K 268 39
                                    

A washegarin dawowarmu daga Abuja ne Farouq yayi wa gidanmu tsinke. Ban san da zuwan shi ba don Habib bai sanar dani ba. Kallon shi na tsaya yi a lokacin da yayi mini umurni da na kai kayan tarbar bako sitting room ďin shi na kuma je mu gaisa, Farouq ne yazo.

Wato kenan shine dalilin da yasa ya dage a jiya sai mun taho da Manal lokacin da muka je gaida su Hajiyar da dare duk da ta nemi da a barta ta kwana tunda ta riga tayi bacci amma yaqi, ashe yasan abinda ya qulla.

Ni na rasa irin wannan abu, duk da na nuna mishi bana son wata alaka ta qara haďa mu da Farouq amma ya kasa tsayawa ya saurareni, yace wai duk abinda yake yi saboda Manal ne.

Ba da son raina ba na tashi naje na haďa drinks da doughnuts haďe da cupcakes akan tray na ďauka na nufi sitting room ďin. Ciki-ciki nayi sallama don ban yi zaton ma sun jini ba.

Akan center table na ajiye tray ďin sannan na zauna a kusa da Habib akan kujera mai zaman mutum biyu. Zaune yake akan single chair dake kusa da bakin kofar shigowa ya ďora Manal akan cinyarshi yana yi mata tambayoyi tana amsa mishi.

A dakile nace mishi "ina yini" ba tare dana kalli inda yake ba. "Lafiya lau Khadija, ya gida?" shima ya amsa yana wani sussunkuyar da kai kamar wani munafuki.

Mikewa nayi zan fita Habib ya janyo hannuna ya dawo dani na zauna, ina lura da Farouq yana satar kallon mu. A kunnena ya raďa mini wai "har kun gama gaisawar?"

Kasa-kasa na amsa mishi ta  yadda babu mai jin abinda zance sai shi "akwai wani abu da zan yi mishi ne da ya wuce gaisuwa, ina ce 'yarshi yazo gani kuma ya ganta, anya ma kuwa Yaya Habib kana kishi na?" na karashe maganar a kufule don sosai naji haushin maganar da yayi.

Saboda Allah ta yaya zai nemi ya tursasani zama a wuri ďaya da Farouq. Bai san yadda na tsani ko sunan shi naji an ambata a kusa dani ba ne da bai soma gigin kawo mini shi gida ba.

"Zan shiga ciki don ina da abinyi" nayi maganar a hankali. Tashi nayi na fita shima kuma Habib bai yi gigin tsayar dani ba kamar yasan bani da niyyar tsayawar ko da yayi hakan.

Ďakina na wuce na kwanta a kan gado yaraf, zuciyata sai suya take yi. Ban kara saka Farouq a idona ba tun bayan da kaddarar samun cikin Manal ya gifta a tsakanin mu don ko nacin zuwan da ya dinga yi gida bayan komawarmu Kafin Madaki kafin aurena da Habib kenan ban yarda na ganshi ba.

Don haka ganin da nayi mishi a yau tamkar fami ne akan tsohon ciwon da ya ji mini a zuciyata wanda nake tunanin shuďewar lokaci yasa ya warke ashe dai yana nan ďanye jagab.

Ba karamar tsana nayi wa Farouq ba don kuwa yayi amfani da matsanancin son da nake yi mishi yayi mini yaudara mafi muni.

Ya rabani da budurci na ya rabani da iyayena da 'yan uwana haka nan ya rabani da karatuna da nake matukar so a lokacin, sannan ya tafi ya bar ni ba tare da ya waiwayeni ba ko don yaji a halin da nake ciki.

Tunda ya samu abinda yayi dalilin zuwanshi wurina shikenan ya rufe babina a cikin rayuwarshi, sai ma na samu labarin yayi aure da irin matar da yake so ni kuma ko oho.

Hawaye ne naji yana neman kwace mini sai dai nayi kokari kwarai wajen ganin na hanashi zubowa don alkawari ne na ďaukar wa kaina na daina yin kuka saboda Farouq.

Na samu akalla mintuna talatin da shigowa kafin Habib ya biyo bayana. Ďagoni yayi ya zaunar dani sannan ya zauna a kusa dani ya kamo hannuna na dama ya rike a cikin nashi yana murzawa.

Ďauke kaina nayi don bana so ya fahimci abinda yake yi mini yana tasiri a jikina, so nake yi ya fahimci fushin da nake yi dashi.

Cakulkuli ya fara yi mini yana cewa "wa kike yiwa fushi, um?" Tuni na fara zillo ina neman kwace kaina ina dariya.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now