BABI NA TALATIN DA BIYAR

2.6K 191 18
                                    

Yau tun safe dana tashi ban koma ba don kuwa kafin fitar Habib sai da ya jaddada mini yau nike da aiki duk da ina jin Nabila tana cewa wai bafa zata yarda ba na shigo gidanta na sameta sannan ya raba mana aiki, kowa tayi iko da inda ya ajiyeta. Ni nayi iko da gidana a Kano itama tayi iko da nata.


Ban dai ji me yace mata ba. Karfe sha ďaya da rabi na shiga kitchen. Jollof rice na dafa wacce ta wadatu da vegetables da zallan naman rago sai zobo drink dana haďa.


Ina juye abincin a warmer ne ďaya daga cikin kannen Nabila ta shigo ta ďora girki, ko kallonta ban yi ba na kwashe kayan abinci na na fita. Akan table na shirya abincin a lokacin karfe ďaya tayi sannan na sanarwa Nabila dake zaune a parlour tana kallon shirin E! News a tashar E! ďin, bata amsa ba nima kuma ban jira amsawar tata ba na koma kitchen na ďauki nawa abincin na koma ďaki nayi shirin yin sallah.


Bayan na idar ne na ďebi abincin naci sannan na mike na kwanta. Ban daďe da kwanciya ba wani daddaďan bacci ya kwashe ni. Karar waya ce ta tasheni, cikin muryar bacci na amsa wayar ba tare dana duba naga mai kira ba.


"Lallai matar nan kina jin daďinki, wai bacci ma kike yi?" Humaira tace. Tsaki nayi nace "to idan ban yi bacci ba me kike so nayi, ya gida da ďan tayi?" na karashe maganar da tsokana.


"Ďan tayi yana jikin ki" itama ta mayar mini da tsokanar. "To ya habuja da mutanen cikinta?" nace "kalau ďinsu, habuja kuma gata nan babu daďi, tunda muka zo ko kofa ban leka ba gashi Yayanki kullum yana office. Loneliness na damuna wallahi, kamar nayi tsuntsuwa na gudu Kano haka nake ji".


"Hmm... Sai hakuri, ni dama nasan haka zata kasance don mutanen gidan basa son baki su rabe su" tace cikin takaici. "Ya wajen su Hajiya?" na tambayeta da son bagarar da waccen maganar don nasan yanzu ne Humaira zata fara mita akan matar Yayanta.


"Lafiyarsu lau, jiya ma acan na yini. Manal na ta tabara wai sai Hajiya ta goyata zata yi bacci" nace "ai Hajiyan ke biye mata shi yasa tafi son zama a wurinta".


Mun daďe muna hira har akayi kiran sallar la'asar sannan muka yi sallama na tashi na faďa bathroom nayi wanka sannan na ďauro alwala na fito. A cikin doguwar rigar material na plain swiss kalar coffee na shirya.


Sai da nayi sallah sannan na zauna na mulke jikina da man Olay body quench na tsara fuskata da simple makeup na kawo ďankwalin kayan nayi ďauri na burgewa.


Kan gado na koma na zauna ina buga game a wayata. Karfe biyar da kwata Habib ya shigo gidan. Da gudu na tashi na ďane jikinshi na makalkale shi. Gaba ďaya hannayenshi yasa ya rungumeni.


Mun jima a haka kafin ya ajiye ni akan gado ya mike tsaye yana kama kugunshi yace "wash, yarinyar nan ashe haka kike da nauyi ban sani ba?" Kyalkyalewa nayi da dariya ganin yadda yake yamutsa fuska.


"Au dariya ma na baki ko?" yace yana mai jefo ni da necktie ďin daya cire daga wuyanshi. Tashi nayi zaune nace "ai kaine, ka kuwa ga yadda fuskarka ta koma sai kace wanda ya ďauki babban buhun masara" na karashe maganar ina dariya.


Ganin ya matso kusa dani yasa na mike da sauri na koma karshen gadon. Dariya yayi ya shiga bathroom. Ina zaune a wurin ya fito daga wanka. Tashi nayi na taya shi ya shirya a cikin jeans kalar blue da polo shirt ďin Ralph Lauren kalar sky blue. Turaren Classic (David Beckham) ya fesa, ash slippers ďin Toms Berkeley ya sanya sannan ya fita ina biye dashi.


Kan table ya wuce yayinda ni kuma na wuce kitchen don na shiryo abincin shi. Akan tray na haďi komai na ďauka na fito. "Wannan abincin fa?" ya tambaya tun ma kafin na ajiye tray ďin hannuna.


BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now