BABI NA GOMA SHA UKU

2.4K 200 5
                                    

A kwance nake a ďaki ina karatun littafi, tun bayan tafiyar Humaira school ban samu na koma ba sai tunane-tunane da nake yi, daga baya ne ma nayi tunanin ďaukar wani littafi na addini mai suna THE GLEAM OF FAITH da Yaya Adam ya kawo mini a wancan zuwan da yayi nake karantawa.


Sallama naji daga kofar ďakin. Kafin in kai ga amsawa ya shigo ďakin fuskar nan a murtuke. Da sauri na tashi tare da yayibar ďankwali na daya cire daga kaina na ďaura sannan na russuna ina daga zaune a kan gadon nace "Ina kwana".


Ďan siririn tsaki ya saki kafin yace "lafiya. Ina Humaira?" ya tambaya cikin ďaurewar fuska. A hankali kamar mai yin raďa nace "ta je school" don haka nan nake jin faďuwar gaba a duk lokacin dana ganshi. Tun bayan zuwanshi na nemi nutsuwata na rasa, gashi dai ba shiga harkata yake yi hasali ma gaisuwa ce kawai take haďa mu amma wani irin tsoronshi nake ji don har Allah-Allah nake yi ya bar garin ya koma inda ya fito.


Juyawa kawai yayi ya bar ďakin ba tare da ya kara cewa komai ba. Ajiyar zuciya na sauke tamkar wacce aka rutsa a gaban sarki tayi karya don ban ma san cewa ina rike da numfashi na ba sai bayan daya fita sannan.


Komawa nayi na kwanta sai dai ban iya cigaba da karatun da nake yi ba don kuwa bani da nutsuwar da zan fahimci abinda nake karantawa. Tunanin Faruq ne ya faďo mini, wasa gaske dai yanzu ya samu watanni huďu ana cikin na biyar da tafiyarshi amma ko da wasa baiyi tunanin ya kamata ya nemeni ba ko don yaji lafiyata.


A yanzu kam na fara sarewa da al'amuran Faruq, ina ganin dama ba son gaskiya yake mini ba, tunda kuwa ya samu na sarayar mishi da abu mafi girma da daraja a tare dani shikenan ya shafe babina a rayuwarshi.

Hawaye ne naji ya cika idona. Ban damu da na goge ba don kuwa kukan kaďai zanyi ya rage mini zafi da raďaďin da zuciyata keyi. Tunda abin nan ya faru ban yi nadamar sanin Faruq ba sai yau, tunda gashi ta dalilinshi na aikata abinda ban taba tunanin zan aikata ba ko da a cikin bacci ne sai gashi na aikata shi idona a buďe tare kuma da yardata.


Gashi kuma amincewar dana yi mishi tayi sanadin bacin ran iyayena abinda ya janyo mini rabuwa dasu ba tare da ni ko su mun shiryawa hakan ba. Motsi yaron cikina yayi, hannu na kai ina shafa cikina abinda ya kara assasa kukana don sai naji tausayin babyn ya kamani ganin irin kazamar haihuwar da zanyi mishi.


"Faruq baka kyauta mini ba, gashi ta dalilinka yau zan haifi ďan gaba da Fatiha. Haďuwata da kai bata kareni da komai ba sai bacin suna da bakin ciki, don yanzu har tsufana na sayawa kaina abin gori. Kaicona ni Khadija, na cuci kaina dana biyewa son zuciyata na yabawa kaina bakin fentin da har na bar duniya ba zai taba goguwa ba".


Kuka sosai nake yi irin mai cin zuciyar nan wanda na daďe banyi irinshi ba da har ban san lokacin da Hajiya ta shigo đakin ba sai ji nayi ta saka hannu ta ďagoni daga durkushewar da nayi akan gado.


Rugumeni tayi a jikinta tana bubbuga bayana a hankali tare da ce mini "ya isa haka nan kukan Khadija. Ashe ba zaki dinga sanyawa zuciyarki hakuri ba. Ina amfanin irin wannan kuka da kike yi. Zaki kankare kaddararki ne?"


Girgiza kaina nayi alamun "a'a" sannan nace "ina takaicin yadda na biyewa son zuciyata ne Hajiya na aikata abinda ya janyo mini bacin suna da subewar mutunci banda tarin zunubin dana ďauka akan sabon Allah da nayi, ina kuma tausayin babyn da baiji ba ba gani ba ganin yadda ban samar dashi ta halastacciyar hanya ba, gashi tun bai zo duniya ba nayi mishi tabon da har ya barta bai zai gogu daga jikinshi ba. Yanzu duk ranar da babyn ya girma ya tuhumeni dalilin da yasa na samar dashi ta hanyar dana samar dashi me zan ce mishi Hajiya?"


Sosai kuka na ya karu a wannan lokacin. Ita kanta Hajiya sai data goge kwallar data taru a idanunta sannan tace "ai illar da zina take haifarwa da wanda ya aikatata tana da yawa Khadija. Shi yasa kullum muke gargaďinku daku nisanceta, kada ku yadda da daďin bakin namiji ku kusanceta bare har ta kai ga sun sanku ďiya mace. To amma abinda ya faru ya rigada ya faru babu abinda zamuyi akai sai kiyaye gaba. Don haka kiyi shiru ki goge hawayenki, kuka ba zai yi miki maganin komai ba sai karin bakin ciki".


A hankali na sassauto daga kukan da nake yi. Har wannan lokacin ina rungume a jikin Hajiya sai ajiyar zuciya dana ke ta faman ajiyewa. Sai da kukan ya tsaya gaba ďaya ne sannan Hajiya tace mini "dama na shigo ne na faďa miki ki shirya bayan la'asar zamu je asibiti don ki fara antenatal". "To" kawai na iya cewa Hajiya, tashi tayi ta fita.


Tana shiga parlour ta iske Habib a zaune a kasa ya jingina da jikin kujera. Ya dafe goshinshi da hannunshi na dama, idanunshi a lumshe tamkar mai yin bacci. "Kada dai ka daďe anan kana jirana? Amma dai ka fasa tafiya yau ďin ko don naga rana tayi kai kuma nasan baka son tafiyqr tsakar ranar nan?" Ta jeho mishi tambayoyin a jere.


Buďe idanunshi da suka kaďa suka yi ja yayi sannan ya sauke hannun daga kanshi tare da gyara zamanshi sannan yace "a'a yau ďin zan tafi Hajiya, kinga nayi missing office yau bazan so ace gobe ma ban je ba kinsan kuma Nabila ta shiga watan haihuwarta ban cika son ina yin nisa da ita ba tunda haihuwar zata iya zuwa kowanne lokaci".

Hajiya tace "haka ne, Allah ya raba lafiya kai kuma ya kaika lafiya ya kiyaye hanya. Amma ai dama kunyi sallama da Alhaji ko?" Yace "eh naje na sameshi ma a kasuwa ganin lokacin da nazo da safe har ya fita shine naje na sameshi acan, Hajiya an haďa mini yajin? ". Tace "eh an haďa harda su daddawa ma da kuka da kubewa don nasan kai mai son tuwo ne, kayan na kitchen bari na saka a fitar maka dashi mota".


Tashi yayi ya bita yana cewa "bari kawai na karba Hajiya na wuce, sai yara sunyi hutu In Sha Allahu zan kawo su suyi hutunsu anan". Cikin murmushi tace "ashe kace ina da 'yan hutu, to Allah ya kiyaye hanya, ka gaida su Nabila da yaran".


Bayan sunyi sallama ne ya fita ya shiga mota sai dai ya daďe a zaune a motar bai tada ita ba. Maganganun da yaji Hajiya nayi da yarinyar nan ne suka tsaya mishi a rai. Ya shigo gidan ne kawai ya hango Hajiya zata shiga ďakin Humaira shine ya bita can don suyi sallama, ga mamakinshi sai yaji suna maganganun da suka saka shi tsayawa ya saurara ba don yana da niyyar yin hakan ba.


Mamakin yadda tarbiyya ta lalace a yanzu yake yi, duba dai kuga yarinyar nan da idan ka kalleta a haka sai kace tafi kowacce 'ya nutsuwa da hankali amma ga abinda taje ta aikata. Shi yasa fa shi babu ruwanshi da Kule-kulen mata na babu gaira babu dalili. Nabilarshi ta ishe shi duk da rashin kirkinta da ake faďa shi kam a haka yake son kayarshi don yasan sai dai ace bata da kirkin amma ba dai a sameta da rashin tarbiyya irin wannan ba.

UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now