BABI NA ASHIRIN DA ĎAYA

2.6K 212 30
                                    

Washegari asabar aka ďaura auren Humaira anan kofar gida da misalin karfe sha ďaya na safe. Kasancewar babu sauran event da za'ayi yasa sai kawayen Humaira na kusa ne kawai a tare damu Zainab da Fadila.

Muna ďaki ana ta hira sai dai ni tunanin Yaya Habib ne fal a raina ganin yadda yake son ya takura rayuwata. Jiya bayan dawowarmu daga dinner sai ga wayarshi yana tambayata dalilin tahowa na barshi bayan nasan saboda ni yaje wajen dinner .

Ni rasa ma abinda zance mishi nayi, ta yaya ma za'ayi yace saboda ni yaje wurin dinner alhalin kuma bikine na tilon kanwarshi ake yi. Ai kowa ya ganshi a wurin nan yasan yaje don ya taya 'yaruwarshi murnar aurenta ne.

Messages kuwa har sun fara isata. A jiyan kafin na kwanta sai da ya turo mini wani, haka nan yau da safe da message ďin shi na buďi ido. Messages ne dai masu nuni da soyayya a dunkule, ni kuwa a yanzu ai na wuce wannan matakin. Tsakanina da soyayya sai dai gani daga nesa amma ba dai a kaina ba ni Khadija.

Ana yin sallar la'asar aka fito da amarya don wucewa da ita gidanta. Ba Humaira ba hatta ni kaina kuka nake yi saboda shakuwar dake tsakanina da Humaira.

Da aka je gidan ma cewa nayi bazan zauna ba sai da su Goggo suka saka baki sannan na yarda na zauna. Ai kuwa ana gama sayen baki na mike nace zan tafi gida. KB da tun da aka fara hidimar biki yake neman yadda zai samu kebewa dani yayi zirif ya mike tare da cewa "muje na kaiki ranki ya daďe".

Bata rai nayi tare da cewa "kada ka damu akwai da wanda zan tafi, nagode". Fita nayi waje bayan nayi wa Humaira sallama. Nacaccen naku kuwa bai daddara ba sai da ya biyoni yana mini magiya akan nayi hakuri nazo ya ajiyeni.

Haka nan na daure na bishi duk da baso nake yi ba, yadda yayi kalar tausayi ne yasa ni binshi ba don na shiryawa hakan ba. A hanya ma duk wani kokarinshi na ganin ya cusa kanshi ne amma ban bashi fuska ba.

Wallahi babu abinda na tsana irin namiji mai naci. Muna zuwa gida na saka hannu na buďe motar tare da cewa "nagode". "Ranki ya daďe sai kuma yaushe?" Ba tare da na kara kallonshi ba nace "sai wata rana" na fice daga motar.

A soron farko ne muka kusa yin karo da Yaya Habib. Da sauri na ja baya ina cewa "yi hakuri don Allah ban lura bane". Tsare ni yayi da ido yana kallona sannan cikin dakewa yace "daga ina kike a daren nan?"

Haka nan naji gabana ya faďi. "Daga gidan Humaira nake" nace ina mai sunkuyar da kaina. "Wai kina nufin tun yamma kina gidan Humaira, kinje kin zauna kin bar mini yarinya tana kukan nemanki alhalin kin san ba lafiya ce da ita ba".

Da sauri na ďago kaina na kalleshi nace "waye ba lafiya Yaya, wai Manal? Sosai ya hassala jin nace ban san Manal bata da lafiya ba. "Wacce irin uwa ce ke ace yarinyar ki bata da lafiya amma baki sani ba saboda baki damu da ita da al'amuranta ba, to eh Manal ce babu lafiya, ba kuma najin zan kara barinta a wurinki tunda ba kula kike yi da ita ba".

Ficewa yayi ya barni a tsaye a soron tamkar wacce aka dasa. Nayi kusan mintuna goma a tsaye a wurin kafin da kyar na iya janye jikina na shiga cikin gida.

Ďakin Hajiya na wuce na faďa mata dawowata. Zama nayi ina so na tambayi jikin Manal sai dai kuma ina jin kunyar yin halan don haka na mike nace mata sai da safe. "Tsaya ki tafi da yarinyar nan don yau rigimarta ta motsa kuka ta dinga yi har da birgima wai kin tafi kin barta, abinda ya haddasa mata zazzabi. Yanzu suka dawo daga asibiti, ga magungunan ta nan akan drawer ďauki ki tafi dasu".

"To" kawai na iya cewa na ďauki Manal tare da ledar maganin nayi wa Hajiya sai da safe na tafi ďaki. Kwantar da ita nayi akan gado na lullubeta sannan na wuce toilet na watsa ruwa haďe da ďauro alwala na fito nayi shirin kwanciya na haye gadon na janyo Manal jikina, har yanzu jikinta da zafi.

Na tofe mu da addu'a sannan na rufe ido don sosai nake cikin gajiya. Ina kin karar shigowar message a cikin wayata, janyota kawai nayi na kashe gaba ďaya na koma na kwanta.

Tunda na kwanta ban farka ba sai da asuba. Lallai nayi bacci don ko qiyamul laili da nake tashi ban samu nayi ba. Brushing hakorana na fara yi kafin na ďauro alwala na fito. Raka'atainil fajr na fara yi sannan nayi sallar asuba. Ban tashi a wurin ba sai da gari yayi haske don zama nayi nayi tilawar AlQur'ani.

Ina cikin ninke hijab ne Manal ta farka. Toilet na kaita na sakata tayi fitsari, nayi mata brushing tare da ďaura mata alwala sannan muka fito na saka mata hijabinta nace "to maza ayi sallah, kinji good girl ďin Maaminta".

Data idar ne naje kitchen na haďa mata tea na bata ta sha sannan na bata maganinta. Ďaukar wayata nayi na kunna, sai a sannan ma na tuna da message ďin da akayi mini jiya wanda nasan babu tantama Yaya Habib ne ya turo shi.

Buďe message ďin nayi don ganin abinda ya rubuto. "I'm sorry for snapping at you, i was worried about Manal that's why. Have a pleasant night". Hmm... Kawai nace na cigaba da harkokina.

Karfe bakwai da rabi nayi na nufi ďakin Hajiya don jin abinda za'a shirya na breakfast. "Jeki kiyi kwanciyarki Khadija, ai akwai sauran 'yan biki da basu watse ba, sun shirya abin karyawar" tace mini.

Don haka na tafi wajen Goggo na zauna muna kara yin sallama don yau zata koma. Haka nan naji bana so ta tafi, kamar na bita haka nake ji sai dai dole ne nayi hakuri har mu samu hutu a school.

A ranar duk waďanda suka rage basu tafi ba sun watse gida ya zama sai mu kaďai. Haka nan nake jina wata iri kewar Humaira na damuna. Gashi Manal tun safe Yaya Habib yazo ya ďauketa har yanzu basu dawo ba.

*****

Ya shigo gidan yana rangaji tamkar wani bugagge. Zama yayi akan kujera ya kwantar da kanshi a jikin kujerar tare da dafe goshinshi da hannunshi na dama.

Hajiya wacce fitowarta kenan daga ďaki ta kare mishi kallo. Ita ta sani yana cikin damuwa sai dai ganin kamar baya so ta sani ne yasa ta kawo idanu ta zuba mishi, addu'arta a kanshi dai bata yankewa don kuwa shi kaďai ta mallaka.

Zama tayi a kujerar dake kusa da wacce yake kai tace "kai lafiyarka kuwa?" Tashi yayi ya zauna sosai sannan yace "lafiyata kalau Hajiya kawai na gaji ne ahi yasa kika ganni haka".

Tace "to ai da zuwa kayi ka kwanta don ka samu ka warware gajiyar sosai, yaushe zaka tafi ne ko kuwa ka fasa sai goben?" Yace "eh Hajiya ina ganin sakko zanyi goben na tafi In Sha Allahu".

Gayra zamanshi yayi sannan yace "ni Hajiya wai har yanzu ba'a samu wani labari na Khadija ba?" Kallonshi tayi a ďage sannan tace "wacce Khadija kenan?" Sosa kanshi yayi yana 'yar dariya yace "Khadija dai 'yar gidan Mallam Hashimu, wallahi Hajiya ko yau ta dawo zan aureta ko don yadda Halisa take garani kamar kwallo zan nuna mata cewa bafa ita kaďai bace mace a duniya. Ni wallahi ban ma san wane tsautsayine ya kaini ga aurenta ba".

A sakarce Hajiya ke kallonshi kafin tace "Khadijar da ta shiga yawon duniya zaka auro ka kawo mini cikin zuri'ata, to Allah ya baka sa'a".

"Hajiya kiyi hakuri amma wallahi duk abinda ya faru da Khadija nine sanadi, ban kuma yi mata adalci ba don yarinyar ta soni da gaskiya naci amanar yardar da tayi mini".

Kallonshi tayi cikin takaici tace "ni dama na zargi haka amma kayi mini musu kace kai babu abinda ya taba shiga tsakaninka da ita. Kenan kai ke da alhakin yi mata ciki Farouq? Ka kyauta mini kenan abinda kayi, don Allah da wanne idon kake son na kalli Mallam Hashimu akan irin wannan cin amana da kayi musu? Mutumin nan har nan wurin yazo yana bani hakuri akan abinda 'yar shi ta aikata yana ganin taci amanarka ta yaudareka bai san cewa kaine kayi mishi wannan cin mutuncin ba".

Tashi tayi tana goge hawaye da gefen rigarta. "Hajiya don Allah..." ďaga mishi hannu tayi tace "babu abinda zaka ce mini don haka tashi ka fita ka bani wuri tun kafin ranka ya baci".

Cikin sanyin jiki ya tashi ya fita daga ďakin sai dai cikin ranshi ya ďauki alwashin duk ranar da Khadija ta dawo zai yi kokarin ganin ya mallaketa ko don ya wanke mata bacin ran daya dasa mata. Bai san cewa yana son Khadija ba sai bayan aurenshi da Halisa ya gane cewa ashe shayi ruwa ne.

UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BADove le storie prendono vita. Scoprilo ora