BABI NA TARA

2.9K 191 5
                                    

Tunda na koma makaranta na dukufa da karatuna sai dai wannan bai hana mini kewar Faruq ba. Kullum ne idan muka zauna sai na yiwa Ramlatu hirar Faruq don a yanzu dai babu wata hira da nake jin daďinta irin tashi, abinda ke bawa Ramlatu mamaki a kullum don tace bata taba zaton zanyi irin wannan zurfin a cikin soyayya ba a yadda ta sanni da rashin bawa maza fuskar kusantowa inda nake sai gashi a cikin ďan kankanin lokaci Faruq ya canja mini alkiblata a yanzu babu wani abu da yake sanyani farin ciki irin zancen Faruq.

Ni kaina na sani ina yiwa Faruq wani irin so ne mai wuyar fassarawa, komai nake yi da tunaninshi nake yi saukinta ďaya shine da bana wasa da karatuna duk da yadda nake bata lokaci wajen tunanin Faruq hakan bai saka na watsar da abinda naje makaranta domin shi ba.

Muna hostel a cikin kwanarmu ni da Ramlatu, ita tana kwance a up bunk ni kuma ina daga kasa. Hira muke yi sama-sama don dai ni hankalina baya kanta yana ga tunanin Faruq. Tun kwanaki biyu da suka wuce na samu wasika daga gareshi yana sanar dani cewa wannan visiting ďin ba zai samu damar zuwa mini ba saboda zai yi tafiya zuwa abuja workshop Kasancewar shi ma'aikaci da ma'aikatar lafiya ta jihar Bauchi.

"Wai ke Khadija idan kika fara tunane-tunanenki bakya ji bakya gani ne? Wallahi tun wuri gara ma ki sake tsari, yanzu ba lokacin da zaki zauna kina tunanin soyayya bane, komai yana da lokacinshi, amma yanda kike yi ďinnan ba zai haifar miki da ďa mai ido ba. Bance ki cire Faruq daga ranki ba ko ki daina sonshi ba amma ya kamata ki gane komai da lokacinshi, ki ajiye soyayya a gefe a duk lokacin da kike makaranta kiyi abinda ya kawo ki idan yaso idan kin koma gida sai ki cigaba daga inda kika tsaya, shima Faruq ďin naki ba aiki ya tafi yi ba ya saka ba zai samu zuwa ba shi me yasa bai ajiye abinda ke gabanshi ba ya zauna don ya ganki, soyayyarki ce tafi tashi karfi ko kuwa abinda ke gabanshi ne yafi naki muhimmaci? Yanzu ma fa magana ce nayi miki amma baki san ina yi ba, sai ki tashi muje admin block su Goggo sun zo".

Cikin hamzari na mike na saka uniform ďina don dama ban riga na saka su a jikina ba saboda kada su cukurkuďe sannan muka fita. Har muka isa admin ďin Ramlatu bata kara yi mini magana ba nima kuma ban tankata ba don dai banga wani abu da nake yi na rashin kyautawa ba.

Goggo ce da 'yan biyu suka zo mini. Bayan mun gaisa ne nake tambayar su Umma da Baba dasu Yaya Yusuf. Ramlatu kam da 'yan biyu kawai take hirarta yayinda na maida hankalina akan hira dasu Goggo.

Muna nan dasu Goggo 'yan gidansu Ramlatu suka zo. A kusa dasu Goggo muka ajiye su dama kuma dai sun saba don kusan duk visiting suna haďuwa. Sai bayan da aka sallaci la'asar sannan muka yi sallama dasu Goggo da 'yan gidansu Ramlatu muka koma ďebi kayan da suka kawo mana muka koma hostel.

Akan hanyarmu ta komawa ne na dubi Ramlatu da har lokacin take faman shan kamshi nace "wai har yanzu baki huce ba besty? Ban san yaya kike so nayi ba, kinsan fa shi tunani yin kanshi yake yi amma kiyi hakuri In Sha Allahu zanyi kokarin ganin na rage yawan tunanin da nake zama inayi sai dai banyi miki alkawarin cire honeyna daga cikin zuciyata ba don wallahi ni kaina ban san wane irin so ne nake yi mishi ba, abinda na sani kawai shine bazan iya rayuwa babu Faruq ba".

"Ai nima ban ce ki cire honeynki daga zuciyarki ba" ta faďa cikin ba'a "kawai dai nace ki maida hankalinki akan karatunki, yanzu ba lokacin soyayya bane a'a to".

Dariya nayi nace "ni dai ba zanyi faďa dake ba Hajiya don na lura yau rigima kike ji".

A kwana a tashi babu wuya wurin Allah, a lokacin da na gama ss2 ne muna hutu iyayen Faruq suka zo gidanmu wajen Baba neman aurena inda ba tare da bata lokaci ba Baba ya yanke musu rana bayan gama school ďina da sati biyu.

Zuwa wannan lokacin soyayya ce mai karfi a tsakanina da Faruq, sosai muka shaku da juna don har ta kai idan muna hutu bama iya kwana biyu bamu haďu ba hakanan idan na koma school baya wuce weekends biyu bai zo wajena ba.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now