BABI NA GOMA SHA TARA

2.4K 209 22
                                    

Ina idar da sallar isha na nufi ďakin Hajiya don nayi mata barka da dare. A  ďakin baccinta na same ta, Manal na kwance akan gado tana bacci. Bayan na gaishe ta ne na samu wuri na zauna ina darurar ta yadda zanyi mata maganar dake cina a zuciya tun ďazu.

Da kyar dai na iya mustering up courage nace mata "um Hajiya, dama ina so ne idan mun sami hutu naje gida na gaishe su. Su kuma san cewa ina nan gidan duk wannan lokacin duk da dai da sanin Goggo a zamana a nan ďin amma i doubt idan zata sanarwa da Baba inda nake duba da yadda ya haneta da shiga maganar a wancan lokacin".

Ina maganar ne kaina a kasa don sai naji ina kunyar haďa ido da Hajiya kada taga rashin karata akan maganar da nayi.

"Alhamdulillah" naji ta faďa. Ďagowa nayi na kalleta, bata kula da kallon da nake yi mata ba ta cigaba da cewa "na daďe ina so nayi miki maganar nan nace bakya ganin lokaci yayi daya kamata ki waiwayi gida haka nan? Sai dai nayi shiru nace bari na gani ko za kiyi wannan tunanin a karan kanki, idan har bakiyi ba to dama akwai adadin lokacin dana kayyade da zanyi miki maganar da kaina sai kuma gashi ma kinyi maganar tun kafin lokacin dana ďiba ya cika, na kuma ji daďi da hakan da kika yi.

Su iyaye da kike gani Khadija ba'a fushi dasu koda kina ganin sunyi miki ba daidai ba, to bare kuma ke da kika watsar da kyakkyawar tarbiyyar da suka ďora ki  akai. Kika bi takan dukkanin wata yarda da amana da suka baki kika watsa musu kasa a ido.

Yaya kike tunanin Ummanki taji a lokacin da ta gane cewa ashe aikin banza take yi wajen ganin ta ďora ki a turba mai kyau duba da yadda kika yi watsi da tarbiyyar data wahala wajen ďora ki akai kika iya bawa namijin da ba halalin ki ba kanki ya sanki ďiya mace?

Kina tunanin wannan bakin cikin zai taba gogewa daga cikin ranta? Don haka don Allah Khadija kiyi kokarin ganin kin tsare kanki daga faďawa mummunar kaddara irin wacce ta afku dake a baya, duk da dai zan iya bada shaida a kanki cewa wancan ďin ma ba halinki bane tsautsayi ne ya afka miki to amma fa akwai son zuciya ma. Babu yadda za'ayi namijin da ba halalin ki ba ya nemi kasancewa dake idan har ba fuska ya gani ba".

Tunda Hajiya ta fara magana nake kuka don kuwa sai nake ji tamkar yanzu ne hakan ya faru dani. Har abada ba zan taba daina kukan biyewa son zuciyata da nayi ba na amincewa Farouq, ashe ma shi da manufarshi ta zuwa wurina tun da farko.

"Zan yiwa Babanku maganar In Sha Allahu idan kuka samu hutu sai a shirya miki tafiyar. Wannan tafiyar ma da mu ya kamata ayi ta don su san cewa kina tare damu duk wannan lokacin. Tashi kije ki kwanta ki kuma bar kukan haka nan" tace tana mai dafa kaina da hannunta.

Ďaki na tafi na kwanta ina kuka. Duk yadda na matsu da son ganin su Umma, dana tuna cewa zanje musu da 'yar gaba da Fatiha sai naji gabana ya faďi. Nasan ganina da Manal bakin ciki kawai zai karawa Umma akan wanda na saka ta a ciki. Tun Humaira na lallashina akan son jin dalilin kukana har ta gaji ta kyaleni.

A haka satin bikin Humaira ya shigo, dole na ware na shiga cikin hidimar bikin don kuwa komai na kawaye a hannuna yake. Ba wasu events zamuyi ba, kamu ne za'ayi a The Afficent ranar alhamis da yamma, sai yini washegari juma'a anan gida sai kuma dinner da za'ayi duk dai a ranar ta juma'a a Marhaba Event Center sai ďaurin aure ranar asabar a kuma kai amarya a yammar asabar ďin.

Ba karamin farin ciki nayi da ganin Goggo ba don tun barowata gida bata zo Kano ba. Kuka ta saka da Hajiya ta nuna mata Manal a matsayin 'yar dana haifa nima ina tayata. Haka muka sha kukan mu kafin muka hakura muka hau hirar yaushe gamo. Babu abinda nake tambayar ta sai "Ummata fa Goggo, tana lafiya dai ko?"

Don duk wannan lokacin da tunaninta nake kwana nake kuma tashi, ban taba zaton zan iya yin waďannan shekaru ba tare da Umma ba. "Kowa na nan lafiya Khadija sai kewarki da take damunmu" ta amsa mini. Na share hawayen daya zubo mini nace "ai na kusa zuwa Goggo, In Sha Allahu da mun samu hutu zan zo don har Hajiya ta sanar da Baba har yace ma dashi zamu je idan lokacin yayi, fatana dai Allah yasa Baba ya huce yanzu kada muje ya kara koroni,idan hakan ta kasance ban san yaya zanyi da rayuwata ba Goggo. Ina tsoron Baba ina tsoron fushin shi".

Na karashe maganar cikin rishin kuka. Rungumoni jikinta tayi tana cewa "ba zai koreki ba Khadija don kuwa sosai yayi dana sanin korarki da yayi bare da yaga an shekara baki waiwayi gida ba sai ya fara damuwa da son sanin halin da kike ciki, sai dai rashin sanin inda kike yasa dole ya hakura yake binki da addu'a".

Cikin kukan dai na sake cewa "kuma Goggo shine baki sanar dashi inda nake ba, da na san yana son ganina da tuni ban koma gida ba?" Dariya tayi tace "to bashi ya koreki ba Khadija, don me zan sanar dashi inda kike bayan na samu hankalinki ya kwanta har kina cigaba da karatunki, nasan cewa dole wata rana ki waiwayi gida don babu yadda za'yi Yaya Sule ya kyaleki a gabanshi na tsawon lokaci ba tare da ya mayar dake gida ba to amma ni na hane shi da yin hakan nace ya bari kiyi nisa a karatun da kika fara kafin ki koma gida zuwa lokacin Mallam ya huce gaba ďaya".

Allah sarki Goggo. Sosai nake son ta don kuwa bata ďauke mu 'ya'yan kishiya ba. Duk wani abu da zata yi a kanmu ko zata aiwatar zaku ga akwai kyakkyawar manufa a bayan abin.

Plain swiss material ne a jikina kalar coffee, ďinkin straight gown ďin da akayi adon stonework kalar orange a jiki. Sai sarka da ďankunne kalar orange kirar kamfanin viennois da nayi amfani dasu.

Golden stilettos na kamfanin aldo na sanyawa kafafuna sai golden clutch bag ďin Michael Kors da nayi amfani da ita. Mayafin dana yi amfani dashi orange ne mai manyan dots kalar coffee a jiki. Kallon kaina nayi a madubi na kara ina mamakin anya kuwa nice Khaddon Umma don kuwa idan ba wanda yayi mini farin sani ba ba lallai ne ya gane ni ba.

Kyauna ya kara fitowa, na kara girma. Ga ilimi da wayewa dana kara samu. Na fito ina taku ďaiďaya, stilettos ďin da na sanya suka kara kawata tafiyata. Kusan dukkanin motocin da zasu tafi wajen kamun sun watse.

Tsayawa kawai nayi ina kallon wurin ina tunanin yadda zan kai maina wurin event ďin. Motar da amarya zata shiga ce kawai ta rage ita kuma da best friend ďinta zasu tafi.

Ban san me yasa na biyewa Humaira ba na zauna makeup artist ďin da zatayi mata kwallliya ta yi mini kwalliya gashi sun janyo duk motocin sun tafi sun barni. To ni yanzu ya zanyi?

"Maami! Maami!!" naji Manal na kwala mini kira daga cikin mota kirar Lexus RX 350 2017 model. Ďauke kaina nayi sanin da wanda take tare a cikin motar. Horn naji ya danna mini kafin yayi reverse ya tsaya daf da inda nake tsaye yace mini "shigo mu tafi ko ba wurin bikin zaki ba?"

UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now