BABI NA ASHIRIN DA SHIDA

2.7K 215 18
                                    

Washegari da safe sai ga sallamar Aunty Saratu don ko karyawa ba muyi ba a lokacin. Da murnarta ta rungumeni a jikina, nima na kankame ta ina kuka. Itan ma kukan take yi.

Sai da muka sha kukanmu ma'ishi sannan muka zauna muka gaisa muna hirar yaushe gamo. "Ashe duk wannan lokacin kina Kano gidan Baba Sule? Kuma Goggo ta san kina can?" nace "ta sani mana, ita fa ta turani can a lokacin da Baba yace bai yarda naje gidan kowa ba a cikin danginshi ko na Umma. Yaya Adam ma yasan ina can don yana yawan zuwa ya ganni, a wurinshi nake samun labarin 'yan gida".

Tace "kai Allah dai ya sakawa Goggo da alkahiri, yayi mata sakamako da gidan Aljanna" nace "Amin". Tace "kinga fa saboda ita ne ďanuwanta ya rike ki tamkar 'yarshi ba tare da ya duba abin kunyar da kika je mishi da shi ba, gashi kuma ya nemawa ďanshi aurenki ba tare da kyamaci al'amarin ba".

Nace "ai Aunty Baba Sule da iyalanshi sun yi nisa wajen nuna halin girma da dattako. Wallahi duk zamana a gidan idan ba wanda ya sani ba babu mai cewa ba 'yar gidan bace ni don babu ta inda suka bambantani da Humaira 'yarsu, komai tare ake yi mana babu nuna bambanci, ga kuma Manal son ta suke yi ba tare da sun kalli kazantar dake tare da ita ba".

Tace "ai fa na gani, ga yarinya nan kowa ya kalleta ai yasan 'yargata ce. To amma yaya zakiyi da ita ke da zakiyi aure? Ko anan zaki barta wurinsu Umma?" Nace "ban san me su Baba zasu tsara ba amma idan a sona ne ace tana wurina don nasan Yaya Habib ma zai so hakan dama kuma ai yaso ďaukarta Baba Sule ne ya hana. Yanzu haka ma a makaranta da sunanshi take amfani".

Tace "haka ne, nima kuma zan fi so ki tafi da 'yarki don idan aka barta anan kananun maganganu ne zasu yi ta tashi, gara dai tana nesan yafi, a hakan sai kiga an manta da ita ma".

Muna zaune a nan muna hira makota suka fara shigowa wai sun zo wa su Umma murnar dawowata. Duk wacce ta shigo sai ta tambaya "ina kuma Khaddon?" don naki zaman tdakar gidan ma bare suga idona.

Sai su Umma suce "ku shiga ciki, tana ďaki". Masu kunyar ciki suce a gaishe ni ai ba sai sun shiga ba, mara sa kunyar kuwa 'yan ganin tunkwal uwar daka sai sun bini har ďakin sun yada mini da habaici duk a sunan ana murnar dawowata gida.

Ni dai daga gaisuwa bana kara tanka musu. Dama kowa ya sayi rariya ai yasan zata zubar da ruwa, ko me suka ce mini ai ni na janyo wa kaina, da ban aikata abin kunya ba babu matar data isa ta biyoni har tsakar ďakin uwata ta gaya mini magana.

Ni na zubar da mutuncina shi yasa har kowa ya samu  damar takawa. Ban san a ina Farouq ya samu labarin dawowata ba sai gashi ya kwaso 'yan kafafunshi yazo gidanmu wai ayi mishi sallama dani.

Tun kafin naji ma waye nace ba zani sai Goggo tace a dai bari a ji ko waye kafin na yanke hukunci. Ďan aiken ya dawo yace "wai ace mata inji Farouq". Saura kiris ban saki ashariya ba don na gane wallahi Farouq ya raina ni ma.

"Kai jeka kace bazan zo ba, ajiya ya bani da zai zo ya dameni" na faďawa yaron. Jim kaďan sai gashi ya dawo wai ana sallama da Baba. Goggo ce tace "kace mishi Mallam na nan waje don tunda ya fita masallaci sallar magriba bai shigo ba".

Sai bayan da Baba ya dawo ne naji yana sanar wa dasu Umma da Goggo cewa wai Farouq ne yazo yana bashi hakuri ya kuma yi mishi tuni akan maganar aurenmu shine Baban yace mishi yayi hakuri amma maganar aure babu ita don yanzu ya bada aurena ga Habib. Shine fa Farouq ďin yace yana so a bashi abinda na haifa domin nashi ne.

Kara buďe kunnuwa nayi don naji amsar da Baba ya bashi don daya kai nan a maganarshi shiru yayi saboda sallallami dasu Umma suka ďauka. "Amma dai wallahi Farouq baya da kunya" nace a cikin zuciyata.

"To me kuma kace mishi Mallam?" naji Goggo ta jefawa Baba tambaya. Har tashi nayi na koma jikin window yadda zan jiyo su sosai don nima na matsu naji amsar da Baban ya bawa Farouq. "Haba Asiya, sai yau na tabbatar yaron baya da kunya wallahi. Ko da wasa da da Adamu ke faďi ban taba yarda ba, gani nake yi ai Farouq ba zai yi haka a gidana ba. Ashe ja'irin yaron nan shine sanadin duk wani bakin ciki da muka kunsa.




BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now