BABI NA ASHIRIN DA BIYAR

2.5K 217 19
                                    

This page goes to my darling little sister, my best friend, my confidant and my everything Maryam Ahmad Eshak aka Little Mary aka Maarmie. Happy birthday dear, may Allah bless ur new age. Have a blast.



Sai da aka sallaci la'asar sannan Baba ya shigo gida suka gaisa da Hajiya yana ta godiyar rikenin da suka yi. A daidai wannan lokacin ina ďakin Umma a kwance akan gado muna waya da Yaya Habib.

Wai sai na fito mun yi sallama don ba zai iya tafiya ba tare da ya kara ganina ba. To kawai nace mishi don a zauna lafiya amma ba wai don zan iya fita wajen shi a wannan lokacin ba.

Har ďakin Umma Hajiya ta shigo tana ce mini "to Khadija mu zamu koma, sai an kwana biyu kenan" tasowa nayi na biyota don nayi mata rakiya. Duk wannan lokacin Manal na makale da Hajiya watakila kuma ta gane tafiya zata yi ta barta ne yasa ta kasa matsawa daga jikinta.



Har Baba ya shiga mota Hajiya kawai suke jira. Kuka ne naji ya taho mini don sosai naji kewar Hajiya ta kamani tun kafin ma su tafi. Rungumeta nayi ina cewa "nagode Hajiya, Allah ya saka muku da alkhairi ya qara girma. Don Allah Hajiya ki yafe mini ban sani ba ko na bata miki". Itan ma kukan ne yake son kwace mata, sai dai tayi kokari matuka wajen hana hawayenta zuba.


A hankali take bubbuga bayana tana cewa "haba Khadija, miye na kukan kuma? Sai kace mun rabu kenan, yi maza ki share hawayen ki kinji, bana son wannan koke-koken naki".



Hannu nasa na share hawayen. Murmushi tayi tace "to ko kefa, don Allah ki dinga kulawa da Manal kinji?" Ďaga mata kai nayi alamun amsawa. Buďe mata motar nayi ta shiga sannan na matsa kusa da Baba Sule nayi mishi sallama.


Kasa kallon Yaya Habib nayi duk da yadda zuciyata ke son yin hakan. Manal na ganin Hajiya ta shiga mota ga kuma Daddynta da Baba Sule a ciki sai ta saki ihu. Goggo ce ta riketa don nema take yi ta kwace ta nufi wurin Daddynta.


Har suka tafi muna tsaye a kofar gida sai ihun Manal daya cika mana kunne. Da kokowa aka shigar da ita gida sai faman zillo take yi wai sai an barta ta bi su Hajiya.


Ni dai ďakin Umma na koma na zauna Manal na makale a jikina. Taraddadin haďuwata da Baba nake yi don tunda muka zo bai zauna ba bare nasan matsayina.


Ko minti biyar ba'ayi ba Umma ta shigo ďakin tace mini "kizo Mallam yana kiran ki". Tashi nayi zan fita Manal ta biyoni. Harararta nayi nace "ina kuma zaki bini sai kace wacce zan gudu na barki" kuka ta saki abinda ya kara kular dani na kai hannu zan doke ta.


Da sauri Umma ta rike hannuna tace "a wanne dalili zaki doketa banda dai ďaukar alhaki". Fita nayi na barsu a ďakin Umma na rarrashinta.


Da sallama na shiga ďakin Baba, kirjina kuwa sai dukan tara-tara yake yi. Daga bakin kofa na tsuguna nace "gani Baba". "Karaso ciki ki zauna" ya umurceni. Tashi nayi cikin sanyin jiki na shiga cikin ďakin sosai na zauna a kan tabarmar dake shimfiďe a gefe shi kuma yana zaune akan sallaya na sunkuyar da kaina.


Gyaran murya yayi, abinda ya kara saka ni shiga cikin taitayina. "Kalle ni nan Khadija, tambaya zan yi miki kuma bana son jin wata magana daga bakinki face gaskiyar abinda zan tambayeki".


"Waye ke da alhakin cikin da kika tafi dashi?" Shiru nayi tamkar ruwa ya cinyeni, duk da nasan dole su Baba su so sanin wanda yayi mini ciki tunda a wancan lokacin basu bani damar da zan sanar dasu ba amma haka nan naji gabana ya faďi ina tsoron sanar da Baba cewa Farouq ke da alhakin yi mini ciki don kuwa nasan ba karamar yarda yayi mishi ba.


"Umhm, ina jinki" ya maimaita. Shiru na kara yi ina mai tsiyayar da hawaye daga idona. "Zaki buďe baki kiyi mini magana ko kuwa sai na saba miki anan wurin?" yayi maganar cikin tsawa.


Ban san lokacin da na amsa mishi da "Farouq ne Baba, wallahi shine" na karashe maganar cikin kuka. "Farouq kuma?" ya ambata cikin mamaki. "Kin tabbata ba karya kike yi mishi ba, kin san idan nayi bincike na gano karya kika yi mini sai ranki yayi mummunan baci".


Nace "wallahi Baba ba karya nake yi ba" yace "to ai shikenan" sai kuma yayi shiru. Zuwa can kuma yace "Alhaji Sule yayi mini magana akan cewa kun daidaita kanku da ďan wajenshi Habibu, haka ne?" Sai naji kunya ta kamani. A hankali na amsa mishi da "eh".


Yace "to madallah, nayi farin ciki sosai da jin wannan maganar don haka ne ma nace duk lokacin da suka shirya sai suzo a tsaida magana domin nima zanfi farin ciki idan kina ďakin mijinki.


Nayi bakin ciki sosai Khadija da abinda kika aikata don kuwa ban taba zaton jin irin wannan ta fito daga gareki ba, sai dai babu yadda muka iya da hukuncin Allah. Jarrabawarmu ce wannan ina kuma fatan Allah yasa mun cinyeta duk da dai da farko bamu karbi kaddarar mu ba abinda yayi sanadin korarki da muka yi.


Sai daga baya na gane babu abinda hakan zai haifar sai karin tabarbarewar tarbiyyarki, ba karamin farin ciki nayi ba da jin cewa duk wannan lokacin kina wajen Alhaji Sule. Na kuma gode mishi da rike mini ke da yayi cikin aminci, babu da abinda zan iya biyanshi sai fatan dacewa duniya da lahira".


Ina kallon yadda ya saka hannun rigarshi ya ďauke hawaye daga idonshi abinda ya kara assasa kukana. 


"Tashi kije, Allah yayi miki albarka, sai ki turo mini Ummantaki". Tashi nayi na fita ina cigaba da sharar hawaye. Ina shiga ďakin Umma Manal ta taso ta rungumeni. Hannu nasa na cireta daga jikina don ina jin kunyar Umma, dole ne tayi hakuri don bazan iya bata kulawa yadda na saba ba.


"Umma Baba yace kije" na sanar mata sannan na zauna akan kujera kwaya ďaya dake ďakin. Tashi tayi ta fita, sai a lokacin na iya janyo Manal jikina ina rarrashinta ganin tana kuka.


Shigowar Goggo ďakin ne yasa nayi sauri zan cireta daga jikina ta tsayar dani tace "kyaleta don Allah, idan baki kula da ita ba waye zai bata kulawar da take bukata? Ni dama tambayarki zanyi azumi kike yi ne don naga tunda kuka zo baki saka komai a bakin ki ba".


"A'a ba azumi nake yi ba Goggo" nace mata. "Kuma shine ba zaki ci abinci ba? Wannan wane irin rashin hankali ne, zaki kankare kaddararki ne ko kuwa zaki ja da ikon Allah ne" Girgiza kaina nayi, ta cigaba da cewa "tunda kin san haka ne me zai sa baza kiyi hakuri ba. Ki taso kije ďakina akwai abinci a flask ki ďauka kici".


"To" nace tare da mikewa na fita, Manal tana biye ni kamar wata jela. Abincin kaďan na ďiba don a cushe nake jin cikina. Tare da Manal muka ci, bayan mun gama ne na fita da plate ďin da muka yi amfani dashi wajen wanke-wanke.


A kofar kitchen na tsaya inda Goggo ke aikin abincin dare. "Ni Goggo ina su 'yan biyu ne da Bilkisu, tunda muka zo ban gansu ba" na tambayeta. "Suna makaranta, lokacin da za'a kai Bilkisu makarantar kwana sai aka haďa da 'yan biyu tunda dama su day suke yi". "Shi yasa naji gidan shiru, ashe duk suna makaranta".


Da dare ne lokacin har mun yi shirin kwanciya a ďakin Umma nake tambayarta su Yaya Adam da Yaya Yusuf. Duk da dai shi Yaya Adam muna gaisawa a waya kuma lokaci zuwa lokaci yana kai mini ziyara a can Kano.


"Adamu yana Bauchi ya samu aiki da hukumar alhazai har ma an saka ranar aurenshi da kanwar mijin Auntynku, shi kuma Yusuf yana Jigawa yana bautar kasa" nace "Allah sarki, ashe auren Yaya Adam ya kusa. Allah ya sanya alkhairi yasa damu za'ayi. Ya wajen su Aunty Saratu fa Umma?"

Tace "suna nan kalau, nasan gobe zaki ganta don ďazu Yaya ta kirata da wayar Mallam ta sanar mata da dawowarki. Ai ďazun da Mallam ya kirani ya sanar dani yadda kuka yi, ashe dama yaron nan Farouq ke da alhakin yi miki ciki shine har yake da bakin cewa kin yaudareshi? Ko me yayi ai kanshi yayi wa".


"Kiyi hakuri Umma, ko me yayi mana dai ai ni na janyo, da ban biye mishi ba da duk haka bata faru ba. Yaudarata da yayi kuma kanshi yayi wa, duk da dai bazan yi mishi baki ba ko don kada ya faďa kan Manal amma da nace ai shima ya haifa".

"Akul" Umma tace "kada na kara jin irin wannan furucin ya fito daga bakin ki, shi ďa ai na kowa ne. Ko ba don Manal ba kada ki kuskura kiyi mishi baki, ki kyaleshi da duniya ma kaďai ta isa ta koya mishi hankali". Nace "to Umma, In Sha Allahu bazan kara ba".


A wannan daren nayi bacci irin wanda na daďe ban yi ba don kuwa gani ga Ummata mai sona da kaunata. Manal tana jikin Umma a haka suka yi bacci, na daďe ina kallonsu zuciyata fal farin ciki kafin na samu bacci ya ďaukeni.

UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now