BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI

2.9K 212 43
                                    

Tun daga tsakar gida Hajiya ta jiyo muryar kanwarta Halima tana faďa. Murmushi kawai tayi domin tasan za'a rina. Ďan yau ne ka haifeshi baka haifi halinshi ba idan banda haka ai da Farouq bai fara faďan rashin gaskiya ba.


Tun kafin Hajiya ta amsa sallamar da suka yi Aunty Halima ta bankaďe labulen kofar parlour suka shiga. Zama suka yi akan kujera suna maida numfashi kamar waďanda suka yi wasan tsere.


Ruwa Hajiya ta ďauko daga fridge ta haďa da kofuna ta ajiye musu sannan ta koma ta zauna. Har wannan lokacin babu wanda yayi magana a cikinsu.


Farouq ne ya fara ďaukar ruwan ya sha don Aunty Halima bacin rai bai barta ta kalli ruwan bama. Zuwa can ta sauke ajiyar zuciya kafin tace "amma dai wallahi mutanen nan basu da mutunci basu kuma gaje shi ba. Ai idan da girma da mutunci da ko a ranar auren yarinyar nan Farouq ya nuna yana da bukatar aurenta sun fasa da wancan su bashi bare a yanzu.


Har ce musu nayi ko don su taru su rufa asirin 'yarsu ai sun yarda da aurenta da Farouq amma mutanen nan suka yi mirsisi da idanunsu suka qi, shine nace musu to mu haďu a kotu don kuwa dole ne su bamu yarinya tunda har ubanta ya bukaci a bashi abarshi".


Hajiya ta girgiza kanta tace "u'uhm, marar kunya dai yaji daďin shi. Wato saboda su ba mutane bane ko kuma babu zuciya a cikin kirjinsu yasa zasu yi yadda kuke so ko? Da can ba sun bashi aurenta ba, me ya hanashi yin hakurin bari ya kaita gidanshi a matsayin matarshi kafin ya nemeta amma ya keta musu haddin 'ya, sai su yanzu don sun ce baza su bashi auren 'yarsu ba shine basu gaji mutunci ba? Shi mutuncin gareshi da ya rasa inda zai je yayi yaudara sai inda ake ganinmu da mutunci.


To ahir ďinku, kunji na faďa muku. Kada ku kuskura kuce zaku kai maganar nan kotu don ban amince muku ba, idan kuma har kaga kai ka isa ka zama ďan kanka sai ka karbi 'yarka ko ta halin kaka to ka sani cewa bada yawuna ba don bazan yadda ka kara zubar mana da mutuncin gida ba".


Tana gama faďin haka ta tashi ta shige uwar ďakinta ta barsu anan a parlour. Ko sallama Aunty Halima bata yi mata ba ta kaďa kai ta tafi gidanta don taji haushin yadda 'yar uwarta ta nuna kin amincewa akan kudurinsu na karbar 'yar ta Farouq ko ta halin kaka.


Shima Farouq ďin ya jima a zaune a wurin yana saka da warwara. Ya sani ya zama dole ya ga Khadija don shi ba wai ya damu da karbar yarinyar bane kawai dai yana ganin kamar idan ya takura da son karbarta ďin to dole ne ma Khadija ta amince da aurenshi.


Bai san cewa yana sonta ba sai bayan da yayi aure ya gane ashe tuntuni itan ce dai yake so ya ďauka sha'awarta ce kawai ke damunshi shi yasa yayi kokarin ganin ya kawar da ita kafin ya bar kasar duk da cewa yayi niyyar aurenta a wancan lokacin ko don ya kauda kwaďayinshi a kanta.


Shi yanzu idan bai samu aurenta ba ya zaiyi da rayuwarshi? Gaba ďaya ya kwallafa wa ranshi son auren Khadijan shine ma dalilin da yasa yana samun labarin zuwanta Kafin Madaki yayi wa garin tsinke ba tare da wani jinkiri ba.


Shi yanzu damuwarshi yadda zai samu ya ganta don yasan idan har ya samu ganawa da ita to an wuce wurin. A irin son da yasan Khadija tana yi mishi yasan ba zai sha wata wahala ba wajen kara kafa gwamnatin shi a birnin zuciyarta. Ai dama hausawa sun ce soyayya bata tsufa sai dai masoyan su tsufa su barta.


Tashi yayi ya shiga ďakin Hajiya yana rokonta akan ta daure suje gidansu Khadija ta basu hakuri, yasan a yadda suke ganin girmanta ba zai yiwu suki amsa mata ba.


A sakarce ta kalleshi tace "Allah ko? An faďa maka yadda kunya tayi kaura daga idanunka nima ta bar nawa idanun ne? To ka sani babu inda zani don ina kunyar haďa idanu dasu, abinda yasa ko murnar dawowar Khadija ban iya naje musu ba saboda ban san da wanne ido zan kalle su ba a irin wannan cin amanar da kayi musu. Idan ma zaka je kayi ta hakurin zama da matarka kaje kayi don ba wani ya zaba maka ita ba kai ka zabi abarka da kanka".


BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now