BABI NA TALATIN DA HUĎU

2.5K 203 10
                                    

A kan table na tarar dasu tana zubawa Habib abinci. Tana ganina ta bata rai. Kujerar dake gefen hagunshi na janyo na zauna ina facing ďin Nabila. Tura plate ďin abincin tayi gabanshi sannan ta ďauki spoon ta soma ciyar dashi a baki.

Ďauke kaina nayi tamkar ban lura da abinda suke yi ba duk da naji babu daďi a cikin raina. Plate na ďauka na ďebi abincin daidai yadda zai isheni na soma ci don dama akwai yunwa a tare dani duk da naci cake da lemo a hanya.

Jefi-jefi Nabila ke jan shi da hira yana amsa mata. Ina gama cin abincin na tashi zan koma ďaki, hannuna ya riko yace mini "ina zaki?"


"Ďaki" na amsa mishi a gajarce ina kokarin kwatar hannuna daga nashi. "Koma ki zauna zan yi magana daku idan na gama cin abinci" uace tare da sakir mini hannu.


Komawa nayi na zauna sai dai a takure nake jina don banda harara babu abinda Nabila ke watsa mini. Tashi tayi ta  hau tattare kwanukan bayan ya gama. Tashi nayi zan tayata ta ďaga mini hannu wajen dakatar dani tace "please, ban saka ki ba, da ina bukatar taimakon ki da na ambata".


Zama nayi gwiwata a sage, ga alama baza mu shirya da Nabila ba don na tsani wulakanci ita kuma naga ta kware ta nan fannin.


Bayan ta kai kayan kitchen ta dawo ta zauna akan kujerar data tashi. Gyaran murya yayi sannan yace "Nabila ga nan Khadija na kawo miki don ta gaishe ki ku kuma saba da juna, duk da ba'a waje ďaya kuke zaune ba ina so ya kasance akwai kyakkyawar mu'amala a tsakaninku.


Zaman lafiyarku shine kwanciyar hankalina. Dukkanku na aure ku ne don ina son ku, babu wacce tafi wata a wajena don haka bazan ďauki cece kuce da kananun maganganu ba daga gareku.


Don Allah Nabila kija girman ki a matsayinki na babba, idan kinga Khadija tayi ba daidai ba ki tsawatar mata. Ke kuma Khadija ina so ki bata girmanta a matsayinta na wacce ta fiki a shekaru da kuma gidan aure.


Kada ki kuskura na kamaki da laifin raina mini mata don ba zan ďauki hakan ba. Game da yara kuma dama naki ne kina da iko dasu kamar yadda mahaifiyar su ke iko dasu sai kiyi mu'amala dasu cikin adalci a matsayinki na uwa a garesu.


Sannan sai maganar girki, zaku na yin kwana bibbiyu har zuwa lokacin da Khadija zata koma Kano".


A take Nabila da da bata wani bada hankalinta wajen maganar da yake yi ba ta hayyayyako tana cewa "ban gane mu raba girki ba? Nan ďin gidanta ne da za'a yi rabon girki da ita. To wallahi ba zan yarda ba yadda idan naje Kano bana sauka a gidanta bare a raba girki dani haka nan bazata zo gidana na ďauki aiki na bata ba. Gara ma tun wuri ka sake lale".


Shi ďin ma a hassale yace "bana son fitina Nabila, bazan ďauki raini ba daga wajenki. Ke har kin isa ki tsara mini yadda zan tafiyar da al'amuran gidana. Da zakice idan kinje Kano a gidanku kike sauka, da yardata kike yin hakan? Ko kuwa don kinga na zuba miki ido kina yin abinda kika ga dama. To na gama magana zaku raba girki kwana bibbiyu tsakaninki da Khadija ba kuma na son na kara jin kin tayar da magana.


Ina fatan kun fahimce ni za kuma kuyi aiki da abinda nace. Akwai mai magana cikin ku wacce bata danganci girki ba?" ya kare maganar da tambaya a garemu.


Shiru nayi a matsayina na karama ina jiran jin Nabila tayi magana sai dai bata yi hakan ba don har yanzu bata huce ba sai ajiyar numfashi da take yi tamkar wacce tayi tseren gudu don haka nace "ni kam bani da abin cewa sai fatan Allah ya bamu ikon aiki da abinda kace ya kuma bamu zaman lafiya mai ďorewa".


"Ameen Khadija" ya faďa fuskarshi ďauke da murmushi, ga alama dai yaji daďin maganar da nayi. Wani matsiyacin tsaki Nabila tayi ta ďauke kai daga duban mu. Tashi nayi nace "zan koma ďaki, Aunty Nabila sai anjima".


BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now