BABI NA GOMA

2.5K 177 3
                                    

Kiran sallar magriba ne ya tashe ni daga kwance. Tashi nayi na fita tsakar gida na ďauro alwala sannan na dawo ďaki na tada sallah. Duk abinnan da nake yi a cikin sanyin jiki nake yin shi saboda zazzabi da ya lullubeni.

Ina idar da sallah na bingire anan wurin na kwanta har akayi kiran sallar isha sannan na daure na mike nayi. Koda na idar kan gado na koma na kwanta. Ban jima da kwanciya ba Umma ta shigo ďakin.

Kallona tayi tace "lafiyarki kuwa Khadija, ina fa lura dake tunda kika dawo na ganki wani iri, duk akan tafiyar Faruqun ne kika wani sukurkuce kika fita hayyacinki, anya Khadija haka zamu yi dake gaba ďaya nema kike yi ki canja halayenki, soyayya na nema ta rufe miki idanu".

Da kyar na iya ďagowa nace "Umma fa kaina ke ciwo shi yasa kika ganni a kwance". Zama tayi a gefen gadon ta kai hannu ta taba goshina. Cikin kulawa tace "tun yaushe ne baki da lafiya baki faďa mini ba, kin sha magani da kika zo kika kwanta?"

Girgiza kaina nayi alamun a'a, "don shirme kuma sai ki kwanta ba tare da kin nemi magani ba, ai sai ki tashi ki ci abinci sai kisha maganin, bayan fitarki ma Adamu yazo yana tambayata ke nace mishi ba kya nan yace gobe idan Allah ya kaimu zaku je shagon Hamisu ki cike form ďin daga nan sai ya rakaki ki koma makaranta sai dai ina ganin dole a ďaga komawarki makarantar har sai kin samu sauki".

Ďaga kaina kawai nayi ba tare dana yi magana ba. Fita tayi ta kawo mini abinci, tuwon masara ne miyar ďanyar kubewa. "Sauko kici abincin idan kin gama sai ki sha maganin, kuma daurewa za kiyi ki ci abincin sosai don nasan halinki da kin cin abinci idan baki da lafiya Khadija". "To" kawai nace mata sannan na sauko na tasa kwanukan abincin a gaba ina turawa kamar mai cin maďaci.

Don kada Umma tayi mini faďan rashin cin abincin kawai na daure na tura abincin amma ba don ina jin daďinshi ba. A duk sanda na ďaga ido na kalli Umma sai tausayinta ya kamani, ni kaina na sani ban kyauta mata ba a abinda nayin, yadda na iya rufe ido nayi watsi da kyakkyawar tarbiyyar data ďora ni akai duk a dalilin soyayya.

Washegari na tashi babu zazzabin a tare dani sai dai kasala da nauyin zuciya da suke damuna. A haka na daure nayi wanka nayi shirin komawa makaranta don banga amfanin zamana a gida ba, nasan munyi maganar zuwana gida da Yaya Adam akan cike form ďin jamb to amma ba shine makasudin zuwana gida ba, nazo ne don Faruq ya bukaci hakan sai dai kuma da ace nasan manufarshi akan zuwan nawa gida da babu abinda zaisa ni baro makaranta nazo, to babu wanda ya tara sani da Allah. Fatana dai Allah yasa kada Faruq ya yaudareni yaki aurena, idan har hakan ta kasance da yaya zanyi ni Khadija?

Fitowa nayi tsakar gida don ďaukar abin karyawana. Umma na ganina da shigar makaranta tace mini "har kin samu saukin da zaki iya komawa makarantar a yau, ai da kin hakura ko zuwa ranar lahadi ne sai ki tafi".

Girgiza kaina nayi nace "a'a Umma gara dai na koma tunda dai na samu sauki, bana so ana ta wuce ni a karatu. In Sha Allahu daga intetnet cafe ďin zan wuce makaranta sai dai idan har bamu gama da wuri bane zan dawo gida amma idan har na samu na kammala da wuri to yau a cik8n school zan kwana".

Tace "hakane, to Allah ya bada sa'a ya bada abinda aje nema, abincinki na nan a cikin kitchen sai ki shiga ki ďauko". "To" nace "amma bari na shiga wajen Goggo tukunna". Ďakin Goggo na shiga na gaisheta sannan na fito na shiga kitchen na ďauko abincina.

Soyayyen dankalin hausa ne Umma ta ajiye mini a ďan karamin food flask sai ruwan lipton dana ďiba a cikin tukunyar da ake dafa shayin dake kare a kan murhu don kada ruwan ya huce na ďauka na nufi ďakin.

Ina shiga ďaki Umma ta miko mini sachet na madarar cowbell guda ďaya tace mini "gashi nan nasan ke ba kya son shan bakin shayi ďazu na bawa bilkisu kuďi ta karbo miki a shagon Mudi kafin su tafi makaranta".


Karbar madarar nayi nace "Umma nagode Allah ya kara buďi" haka nan naji hawaye na neman zubo mini, ta karfi na maida hawayen don bana son Umma ta gani don nasan tsirani za tayi don son jin dalilin kukana abinda ni kuma bazan iya faďa mata ba kenan.


Bamu wani daďe ba a internet cafe ďin Yaya Adam ya gama cike mini Jamb form ďin ya rakani makaranta. Lokacin da muka je ana dining hall don yin lunch don haka hostel kawai na wuce.


Tunda na koma school na rasa walwalata da kuzarina, komai zanyi cikin sanyin jiki nake yin shi. Ganin waďannan changes đin da Ramlatu tayi a tare dani sai ta danganta shi da tafiyar da Faruq yayi ni kuma sai na bita akan hakan ďin ne, abu guda ďaya na sani shine yawan tunanin da nake yi bai saka na watsar da karatuna ba don kuwa a yanzu shine kaďai abinda nake yi yake ďebe mini kewa.


Har lokacin hutu yayi muka koma gida bani da nutsuwa a tare dani bare dana lura cewa nayi missing period ďina, duk da haka ina kokarin ganin na kore zargin da yake ďarsuwa a cikin zuciyata wato tunanin ko ciki gareni. Duk da yawan kasala da son yin bacci a cikin kowane lokaci da nake fama da shi amma hakan bai sa na yardarwa kaina cewa ciki ne dani ba sai da naga na doshi wata na biyu ba tare da nayi period ba sannan na fara tsorata da al'amarin.


Damuwa ce tayi mini yawa don haka yau na shirya nace wa su Umma zani gidan Auntie Saratu don na gaisheta. Koda naje gidan nata ma ban iya tsinana mata komai ba sai faman kwanciya da nake yi har dai ta gaji ta tambayeni cewar me ke damuna don tana lura dani tunda nazo bana walwala sai yawan tunani da taga ina fama dashi. Babu komai kawai na iya ce mata.


Wurin azahar na tashi nayi mata sallama zan tafi gida. "Yanzu da ranar nan fatse-fatse zaki tafi Khadija sai kace wacce ake korarki, ba zaki bari ayi sallar la'asar ba sai ki tafi lokacin rana tayi sanyi?" tace mini. "A'a" nace mata "gara dai na koma gida don Baba ma bai san nazo nan ba kada ya koma gida ya tarar bana nan".


"Yanzu don kinzo gidana sai Baba yayi faďa, don Allah kiyi zamanki Khadija idan yaso sai na raka ki da yamman don dama na kwana biyu banje gidan ba ina so naje na gaishe su". Fafur naki yadda na zauna don haka ta kyale ni na tafi kawai amma ba don taso ba.

UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now