BABI NA TALATIN

2.5K 206 14
                                    

Su Aunty na idar da sallah suka fara haramar tafiya gidan Baba Sule don acan zasu kwana sai gobe su wuce Kafin Madaki. Sallama suka yi mini akan cewa zasu dawo gobe suka tafi har da Manal zata zauna a wurin Hajiya sai an kwana biyu sannan ta dawo hannuna, Hajiyan ce kuma ta tsara hakan.

Humaira ma bata zauna ba duk da rokon da nayi tayi mata akan ta zauna ďin amma sam taki amincewa.


Bayan tafiyarsu ne na samu na karewa ďakina kallo. Sosai iyayena suka yi kokari, duk da kasancewarsu masu karamin karfi amma sunyi mini kaya masu kyau daidai aljihunsu.


Gado ne imitation ďin na waje kalar mustard haďe da dressing mirror da wardrobe babba mai kofofi shida sai chest of  drawers mai guda biyar da aka jera mini kwalaben turarukan wuta na da humra akai.


Labulayen ďakin kalar dark blue ne, akwai kananun dots kalar mustard a jiki. Sosai farin ciki ya lullubeni ganin yadda ďakina yayi kyau don banyi zaton zan samu kaya kwatankwacin waďannan ba ma.


Basu daďe da tafiya ba naji sallamar Habib a bakin kofar ďakina. Cikin hamzari na gyara lullubin kaina kafin na amsa sallamar a can ciki don banyi zaton ma ya jini ba.

Karasowa yayi cikin ďakin ya zauna a bakin gadon daf dani sosai don har jikinshi yana gogar nawa. Hannayena ya kamo ya rike a cikin nashi yana murzawa a hankali. "Kin ganni sai yanzu ko? Na biya ta gida ne mun gaisa dasu Hajiya, Ya gajiyar hanya?" yayi maganar tamkar mai raďa.

Cikin 'yar karamar murya na amsa mishi da "lafiya lau, yaya ka baro su Hajiya?" "Lafiyarsu lau, tace ma a gaisheki". Nace "ina amsawa". Cikin dabara nayi kokarin janye hannayena daga cikin nashi don wasan da yake yi dasu ya sanya mini jin kasala a dukkanin jikina sai dai kuma bai barni nayi hakan ba.


Hannu ya kai kan cikina yana shafawa a hankali. Cikin murya kasa-kasa yace "ga alama kina jin yunwa don naji cikinki a shafe shafal, hala ma duk yau baki ci abinci ba? Ďan bani mintuna biyu, ina zuwa".



Ya tashi ya fita ba tare da ya jira amsawata ba. Jim kaďan bayan fitarshi sai gashi ya dawo hannunshi ďauke da tray. Da sauri na tashi don na amshi tray ďin sai dai bai barni nayi hakan ba ajiyewa yayi akan ďan karamin rug ďin dake shimfiďe a gaban gadona.



Kamo hannuna yayi ya zaunar dani a kan rug ďin tare da buďe bowl ďin da akayi wrapping da foil paper ya juye naman dake ciki akan plate ya turo mini gabana. Kaza ce da akayi wa gashi ruwa-ruwa taji tumatur da albasa haďe da kayan kamshi sai tashin kamshi take yi.


A take yawu ne ya tsinke don sosai kazar ta bani sha'awa gashi kuma dama ina ta faman dakon yunwa ta kwana da kwanaki don tunda aka fara hidimar bikin bana samun zama naci abinci.


"Bismillah, ki fara ci mana kika wani kawar da fuska gefe. Ko kuwa dai ni kike so na baki?" Murmushi nayi sannan nace "a'a zan iya ci da kaina". "Oya saka hannu kici idan ba haka ba nayi miki ďura, kin san kuwa ba tausaya miki zan yi ba" yace tare da kashe idonshi guda ďaya.


A kunyace na saka hannu ina cin naman shi kuma yana jana da hira kaďan-kaďan. Yawanci dai tambaya yake mini akan karatuna ina bashi amsa.


Ga mamakina naci naman sosai don kiris ya rage ban cinye duka ba. Kunya ce ta kamani ganin yadda na saki ciki na kusa cinye naman, babu shiri na ďauke hannuna daga ciki.



Girarshi ya ďaga mini cikin yanayi na tambaya. "Na koshi" nace ina mai sunkuyar da kaina. "Babu laifi, ai kinci da yawa" yace tare da miko mini tumbler ďin da ya cika da sassanyar yoghurt ďin nagari.


Karba nayi ina sha a hankali shi kuma yana cin sauran naman dana rage muna hira duk da dai na kasa sakewa da shi a yau. A haka har muka kammala ya ďauke tray ďin ya maida kitchen. Wai da nace ya kawo na kai sai ce mini yayi yau ranata ce don haka ko cokali ba yaso yaga na ďaga shi zai yi mini duk abinda nake so, nawa kawai na ambata.


Har ya dawo ďakin ban tashi daga wurin da ya barni ba. Yana shigowa ya shige toilet sai da ya fito ne naga ashe alwala ya ďauro. "Tashi kiyi alwala muyi sallah Allah yasa ma kin yi sallar isha?" ya karashe maganar da tambaya.


Sunkuyar da kaina nayi sannan cikin sanyin murya nace mishi "bani da tsarki" don sosai naji kunyarshi ta kamani.


"Ok" kawai yace ya shimfiďa sallaya ya tada sallah. Tashi nq buďe wardrobe na fito da kayan bacci na haďe da jakar kayan wanka na da duk wasu kaya da zan bukata na shiga toilet.


Wanka na fara yi a cikin ruwa mai zafi sosai sannan nayi brushing hakorana na kuskure bakina da mouthwash. Sai da na fara kimtsa jikina sannan na saka cotton doguwar rigar baccina mai zanen butterfly kalar pink.


Dogon hijabin da dama na shiga banďakin na ware na saka sannan na ninke kayan dana cire na fita. Ban tarar dashi a cikin ďakin ba don haka na buďe wardrobe na ajiye kayan hannuna na koma kan gado na zauna.


Ina zama sai gashi ya shigo a cikin fara kar ďin jallabiya, ga dukkanin alamu dai wanka yayi shima. "Wani wuri zakije ne naga kin kunshe a cikin hijabi?" shine abinda yace mini bayan shigowarshi ďakin.


Girgiza kaina nayi alamun a'a. Sai cewa yayi "to ki cire shi bana so, idan har ina tare dake bana son ganinki a kunshe cikin hijabi ko mayafi, sai dai idan baki akayi shine zaki rufe mini jikinki don ban yadda matata ta fita cikin waďanda ba muharramanta ba ba tare da ta suturta jikinta ba".


"To" nace na saka hannu na zare hijabin daga jikina. Karbar hijabin yayi ya ajiye a gefe tare da cewa "ko ke fa, da kin wani kunshe a cikin zumbulelen hijabi sai kace mai takaba".


Dariya nayi nace "au sai mai takaba kaďai ke saka hijabi" yace "eh, sai ko matar liman" ya faďa yana dariya.


"Wash Allah na gaji wallahi" ya kwanta a rigingine yana kallon ceiling kafafunshi kuma na kasa. Yana daga kwancen ya janyo ni jikina ya kwantar dani a samanshi. Kwantar da kaina nayi akan kirjinshi tare da lumshe idanuna.



Ina jinshi ya zare ribbon ďin dana ďaure gashina dashi yana shafawa a hankali har yana nutsar da hannunshi a cikin gashin sai yaja ta tsakankanin 'yan yatsunshi har sai ya kai karshe sannan ya kara maidawa.


Mun yi kusan mintuna goma a haka kafin ya kwantar dani sosai akan gadon. Tashi yayi ya kashe fitilar ďakin sannan ya dawo ya kwanta a jikina yana wasa da wasu daga cikin sassan jikina.


A haka har bacci ya ďaukeni, ko da na tashi farkawa har an shiga masallaci sallar asuba. Tashi nayi na shiga toilet na kara kimtsa jikina sannan na dawo na kwanta. Ina cikin bacci naji dawowar Habib daga masallaci, kwanciyar shima yayi a inda bamu farka ba sai karfe goma na safe.


UMMASGHAR.

BA'A KANTA FARAU BAWhere stories live. Discover now