taura biyu 1

26.1K 1.4K 37
                                    

*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
       _Mi amor-mi vida_....

_viawattpad@mamuhgee_

           *1*

_Bismillahir-rahmanirraheem_.

*B* abban gidane sosai daya qunshi 6angarora acikinsa sbd yawa da zuriar gidan sukeda shi,,

Gidane tsohon gini irin na masu arzikin lokacin baya daya gabata,

Mal Zubair shine mamallakin gidan da ahalin gidan gabaki 'daya,

Ya rasu shida Mai 'dakinsa Fatima sunbar 'yaya hudu duka maza,,

Baba malam hayatu shine babba agidan yanada tsananin zafi da fa'da,
Sam baya kar6ar uzuri ko kuskure duk da kasancewarsu malamai masana addini,

Baba malam shine Mai zartarda duk wani hukunci acikin gidan Kuma ya zartu Koda baiyiwa kowa dadiba.
yanada mata biyu inna hindatu da iya lami,

Inna hindatu bata ta6a haihuwaba iya lami ce keda 'yaya bakwai, _zayyanu, auwalu, dahiru,Musa,mustapha, abudullahi da sani_.

Baba shehu shine mabiyin baba malam Kuma shima kusan duk halinsu 'daya da baba malam illai shi Yana da'dewa baiyi fadan ba,
Matarsa 'daya shi,mama salamatu Sai 'yaya biyar duk mata,hafsat, Amina, hajaru, zainab da sumayya Kuma duk anyi musu aure.

Sai baba Yusuf Mai sanyin Hali da kawaici dakuma tsananin qaunar 'yanuwansa, shima matarsa 'daya fatima da 'yaya biyu _*AYSHA*_ da nuratu.

Alh Bello shine qaraminsu Kuma fitnannensu Dan masifa da son kansa a fili yake sbd ya 'dan taba yin arziki abaya Amma yanxu Babu shiyasa ko Abu ka'dan akai saiya maidasa babba akan fitina da fa'dansa.
Matansa biyu mama bilki da umma sakina.,
'yayansa bakwai _ahmad, isah, Umar, abbakar Sai saudat Salma da husna_

Dukkaninsu a gida 'daya suke Sai dai kowa da shiyarsa Amma yaransu maza kaf 6angarensu 'daya hakama matan.

Asalinsu buzayen qasar nijar ne malanci yakawo mahaifinsu garin gombe harya gina gida yazama mazauni.

Malamai ne kaf 'dinsu Kuma basuda wani aiki bayan malanta hakama ba wani arzikine  dasuba Sai rufin asiri.

A rayuwar gidan Sam basa auren na waje saidai atsakaninsu sbd yawa dakuma tsananin kyamar wani yare daba nasuba na buzaye.

Qabilanci ne tsantsa acikin jinin kowane 'dan Adam dake rayuwa acikin gidan,
Basa qaunar ha'dawa da ko bahaushe bare wani yare har gwara Fulani.

Wannan aladace dasuka gado tun gurin iyaye da kakanni shiyasa duk kwa'dayi da maita ta kyau da 'yayan gidan sukedashi ba'a tunkararsu da maganarso,

Qiyayyar dasuke fitowa suna nunawa ta rashin son ha'da zuria da wata qabila a qarara yake Dan abin har tsoro da mamaki suke bawa na taredasu.

Yaran gidan kaf dinsu maza da mata ustazai ne kamilallu kullum jikinsu a rufe yake ruf ko qafarsu baka gani fuskarsu ma wani sa'ilin suna rufewa idan zasu fita.,

Mazansu da matansu sun haddace alqur'ani akansu da sauran littafan addini.

Ka'dan ne daga cikinsu sukai karatun Boko sbd bai damesuba sunfi riqe addini shiyasa layin gidan kullum acike yakeda motoci da mashina harda kekuna gurin 'daukar karatu a gidan.

Ayshah,husnah,saudat da Salma kusan sa'anin juna ne 'yan kimanin shekaru goma Sha takwas zuwa Sha Tara.

A al'adar gidan mata basa wuce gaba da secondary aure suke musu Amma wannan karon anbarsu Aysha sun wuce sbd ba'ayi Shirin aurensuba Amma antsayarwa kowaccensu da miji.

A university suke karatu yanxu suna two hundred level.,
Aysha medicine take karatu sukuma sauran gabaki 'daya Islamic sukeyi.

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now