taura biyu 9&10

8.2K 729 10
                                    

*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
       _Mi amor-mi vida_....

_viawattpad@mamuhgee_

           *9&10*

Cikin rashin tsiwa ta matso gabansa tace,

Wat do you think you're doing Nik?

Kallon police 'din yayi da alamar kubar gurin da sauri suka bar gurin ya juyo ya kalleta yace,

Yes I mean she's not going anywhere and......

A hasale tace,

Wat?
are you crazy?
You must be out of your mind right?
I mean wat a are you thinkin......

Shut up Davina''''''' yafa'da cikin qosawa da zancenta sbd zuwa time 'din zazza6i da ciwon jiki yakeji sosai na 'yar wahalarda yayi akan spider 'din.

Juyawa yayi zai bar gurin Amma wani irin jiri da azabar ra'dadin da fatarsa ke Masa yasashi yanke jiki ya fa'di a sume.

A ki'dime sukayo kansa Davina tuni ta 'daga waya takira mum ta sanarda ita Aiko a gigice tabar office tayo asibiti.

Kinkimarsa sukayi sukabar gurin dashi Davina na jifanta da wani mugun qyamataccen kallo Dan tayi alqawarin na'da Mata mugun tarkon dabazata iya fitaba.

Zubewa gurin jiki a mace hawaye na tsiyayo Mata zuciyarta na wani irin nauyi,
Daqyar ta miqe tabar gurin jikinta a sake.

Kodata koma gida saita kasa samun sukuni ta zare hijab 'dinta zata ninke taji wani Abu Mai 'dan nauyi a hijab 'dinta.

'dagawa tayi taduba gabanta yayi mummunar sarawa sbd ganin agogo maqale a hijab 'din
Tabbas koba'a fa'da mataba tasan na Nik ne..

Zarosa tayi jikin hijabin takalla saiga hawaye sun gangaro Mata ta zauna bakin gado tareda rintse idanu tana Jin zafi cikin zuciyarta.

Asibiti kuwa sunga tashin hankali Dan kuwa qaramar haukace kawai mum batayiba ganin jikin Nik duk a yakushe abinka da farin mutum da fatarda Bata Saba da wahala ba tuni yayi jajir har wata fa'dawa yayi cikin qanqanin lokaci.

Cikin sati 'daya ya warke sbd kyakkyawar kulawa da tattalin dayake samu hakama dad 'dinsu tuni yazo sbd yanda suka zuzuta ciwon.

Sauri take ta qarasa gida sbd yamma datayi ga yunwa da gajiyar data kwaso a makaranta.,

Ya salam''  tafa'da ahankali tareda saurin Jada baya sakamakon wata ha'daddiyar jeeb tareda motar police datasha gabanta.

Yawu ta ha'diye da qyar idonta na kawo ruwa ganin Davina ce janye da jeeb din tareda 'yan sanda.

Glass ta sauke takalli officer mace cikin police 'din tace,

Arrest her she's the one.

Girgixa Kai tayi tareda ja baya Amma haka matar tajawota da qarfi ta tura motarsu sukai station da ita.

Suna Isa Kai tsaye aka bu'de file 'din qarar wai ta fasa motar Davina tayi Mata sata hakama tayi amfani da akaifa duk da yayyake jikin Nik.

Ba kunya ba tsoron Allah police suka filen case 'din ahaka
Banda kuka babu abinda takeyi hartana shaqewa.

Address 'din gidansu tabayar sukaje suka sanar dasu cikin qanqanin lokaci saigasu ya Umar da baba alhaji.

Tana ganinsu tasaki wani sabon kuka tana qara tausawa kanta da zuriarta sbd wannan shine zuwansu police station na farko atarihin rayuwar gidan Sai gashi akanta anfara.

Kai tsaye sukace basu yarda da wannan zancenba Dan kuwa sunsan halin ayshah babu yanda zaai su yarda da wannan qazafin.

Money and power Mss queen tayi amfani dasu ta Hana a tsaya a saurari su baba alhaji qarshema turata cell akayi aka rufe
Kuka Babu kalar Wanda batayiba
Gidansu ma gabaki 'daya suna cikin tashin hankali Dan iya zafi sun 'dauka matuqa akan wannan zalinci da toxarci da akai musu.

Kwananta 'daya a cell 'din ciwo ya rufeta ala dole aka saka Umar maimakonta itakuma akai asibiti da ita.

Kwananta biyu taji sauqi suka zo suka Kuma tafiya da ita.

Tunda suka iso police 'din take kuka wannan karon gaba 'daya su harda baba malam da abbanta da baba alhaji sukazo taredasu Yaya abbakar.

Isowar mss queen tareda Finn da Davina yasa dukkaninsu miqewa suna kallonta cikin qyanqyami musamman ma iyayensu dasukafi Jin zafi ganinma Ashe kafiraine wainda suka yiwa ayshah wannan mugun wulaqancin.

Wani kallo tabisu baba Mal dashi kafin tashige office 'din officer incharge tabarsu tsaye kafin shima baba Mal yashiga daga baya.

Alamari dai baiyi kyauba sbd kaca kaca akayi a office 'din hardasu fa'da dansu Yaya abbakar taruwa sukayi sukaiwa Finn duka Suma Nan police suka hau dukansu kan kace me gurin ya ida hargitsewa Saida akaida gaske aka shiga tsakani.

Kwance yake a Palo Yana hutawa Dan har lokacin qarfinsa bai gama dawowaba duk da dai tunanine wannan karon yafi hanasa qarfafa jikinsa.

Three-quarter blue jeans ne a jikinsa da farar designer shirts qal,

Fatarsa tayi kyau hutu ya da'da bayyana ajikinsa sbd tun ranarda aka sallamosa ko gate 'din gidan bai ta6a fitaba Yana lafe kullum ana lilinsa.

Shigowa Murphy yayi cikin yanayi na damuwa ya kalli Nik yafara Koro masa bayanin halinda ake ciki.

Cikin wani irin yanayi zancen ke shiyarsa  ya aje cup 'din milkshake dake hannunsa ya miqe tareda kallon Murphy yace,

Take me to the station...

Gudu Murphy yayi cikin mintuna qalilian suka iso station 'din daidai lokacinda Davina ta 'daga handbag 'dinta Mai qarfe ajiki zata qwalawa ayshah cikin zafin nama ya janyeta ta fa'do jikinsa cikin rashin sa'a niqaf dinta ya zame ya fa'di qasa.

Wani wahallalen numfashi yasaki kunnuwansa da idanuwansa sukai 'dif numfashinta dake fita da sauri kawai yakeji.

Fixgosa ya Umar yayi da qarfi tareda sakar Masa wani wahallalen Marin dayasa hancinsa 6arewa da jini tayi saurin rintse idanuwanta wani nauyi na na sauka zuciyarta.

Ihu mum tasaki tareda shararawa Umar wani gigitaccen Marin itama.

Zaburowa su abbakar sukai aka damqesu tareda turasu cell shikuma mum da Murphy sukaja hannunsa zuwa mota Dan kaisa asibiti Dan hancinsa dake jini
Shikuwa duk baimasan sunayiba idanuwansa na kanta ko qiftawa bayayi

Itakuwa kanta na qasa takasa 'dagowa Dan jikinta yabata idonsa har lokacin na kanta.

A asibiti bayan anyi treating 'dinsa sun dawo gida kwantawa yayi kamar Mai bacci tareda dunqulewa cikin bargo bugun zuciyarsa na tsananta.

Daqyar da biyan ku'din suka samu aka sakosu abbakar suka dawo gida zuciyoyinsu duk a qone da tsananin 6acin Rai da baqin ciki ace wai su rasa abin arxikin dazasuyi fa'da dashi Sai kafirai.

Fa'da da nasiha Kam ayshah tashasu harta gaji.,

Sati 'daya kenan da faruwar alamarin kullum tana 'daki kwance lamo ko doguwar magana batason yi Dan ita tuni tacire Rai da batun komawa makaranta Dan tasan yanada wuya abarta takoma.

Zaune take da safe tana a 'dakinsu tana karanta wani hadisi su husnah nata Shirin tafiya makaranta.

Nuratu ce tashigo cikin uniform 'din makarantarsu takalleta tace,

Anty ayshah ya Umar nakira.

Lumshe idanu tayi tareda rufe hadisin ta miqe tsaye tasaka dogon hijabinta ta nufi 'dakin mama sakina Dan tasan yanacan.

Kallo 'daya yayi Mata ya 'dauke Kai sbd duk ya kalleta yanxu tunowa yakeda fixgowarda wannan shegen Christian  yayi Mata ta fa'da jikinsa saiyaji zuciyarsa na tafasa Dan duk ranar dayakuma ganin wannan gayen ko a hanyane saiya cire Masa hannun daya ta6a Masa aysharsa dashi.

Gaishesa tayi a ladafce taredayin qasa dakai tana sauraron abinda zai fa'da.

Cikin danne baqin cikinsa yace,

Ki shirya kici gabada zuwa makaranta munyi mgn dasu baba sbd bazakibar karatunki kan wasu kafiran banxaba.

Lumshe ido tayi sbd yanda hakanan zancensa ya daki zuciyarta ahankali tace,.  To tareda ficewa tabar 'dakin.


Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comments_

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now