taura biyu 2

10.7K 893 13
                                    

*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
       _Mi amor-mi vida_....

_viawattpad@mamuhgee_

           *2*

Yauma a sanyaye ta iso makarantar sbd duk jinta take a takure badan tana tsananin son karatunba da batajin zata iya cigaba da zuwa sbd wannan new site 'din yafi qarfin abinda qwaqwalwarta zata iya 'dauka.

Lectures biyu tayi yau Dan haka da wuri tagama Tana fitowa hall ta fiddo niqaf 'dinta ta rufe kyakkyawar fuskarta sbd kallo dayayi mata yawa Wanda tasan bai wuce na suturartaba sbd har ja hijabinta keyi.

Sauri takeyi ta tafi gida duk da niqaf 'din data saka kanta a qasa yake bazaka ta6a cewa sauri takeyiba sbd cikin nutsuwa take tafiyar kaman yanda addini ya koyar.

Tsayawa tayi cak tareda juyowa ahankali sbd sunanta dataji ankira daga bayanta.

Ajiyar zuciya tasaki sbd ganin wata ayshar ce ake Kira ba itaba.

Juyawa tayi zata wuce batareda sanin isowa mutumba sukai wani irin karon dayasa wayar hannunsa da car keys 'dinsa zubewa qasa.

Ya salam'' tafada ahankali cikin sauri tareda ja da baya jikinta na matuqar rawa sbd jikinsu daya 'dan ha'du Wanda wannan shine karo na farko da jikinta ya ta6a ha'duwa da jikin wani 'da namiji.

Tsayawa kallonta yayi sbd ganin yanda jikinta ke tsananin rawa abin dayafi basa takaici ma kenan,

Samanta zawa qasanta ya kalla cikin qyanqyamin shigarta sannan shibaiji baqin cikin ha'duwar jikinsuba shida yakeda komai na rayuwa musamman kyawunsa dake fuzgar mata Sai itace da fuskarta ke rufe qilama nakasasshiyace shiyasa ta rufe fuskar.

Dafasa abokinsa Murphy yayi bayan ya 'dauko Masa kayansa dasuka zube Yana cewa,

Let's go Nik we're getting more late..

Wucewa yayi tareda qara juyowa ya kalleta yana 6ata fuska.

Hawayen datake dannewa ne suka gangaro mata ta 'dago Kai ahankali takalli inda sukabi dai dai yakuma juyowa manyan idanuwansu suka ha'du da juna.

Atare gabansu ya Fadi yayi saurin 'dauke Kai sbd tsoro da idanuwanta suka bashi danshi mutum ne Mai tsoron mutane sbd bai cikason ko kallon wasu mutanen ba.

Ita ma cikeda tsoro ta juya jikinta na tsananta rawa ta fice tabar makarantar.

Harta Isa gida nutsuwarta bata gama daidaita.

A qofar farko ta ha'du da ya Umar gabanta yakuma yankewa ya Fadi sbd ganin Yana qureta da kallo tai saurin tattaro nutsuwa tareda qaqalo murmushi cikin sanyin murya tace,

Ya Umar ina yini?

Cikin Jin da'di da tsananin qaunarta ya amsa tareda cewa,

Ayshah da gani kin 'debo gajiya ko?

Eh'''tace tana sauke Kai qasa.

Bata hanya yayi ta wuce batareda yakuma wat maganarba.

A 'dakin umminta ta yada zango ta cire hijab 'dinta tareda sakin ajiyar zuciya ahankali.

Washe gari jiki a sanyaye ta shirya ta nufi makarantar duk da yau ya Umar da kansa ya rakota har bus stop tashiga mota.

Tunda suka shiga first lecture 'dinsu taga tamuqar ba tattaro nutsuwa tayiba to bazata fahimci komaiba shiyasa ta 'dan nutsu ta karanto addua tareda maida hankali saigashi tana fahimtar komai.

Sai four suka fito a gajiye take sosai ga yunwa datakeji sbd Sam basa cin abinci a waje komai rintsi shiyasa ko ruwan makarantar Bata ta6a siya tashaba.

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now