taura biyu 23

10.2K 745 18
                                    

*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒
          _Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_

              *23*

Rawa jikinta yake sosai duk ta qara rikice Masa Nan hankalinsa ya tashi ya qara shigarda ita jikinsa cikin tsananin damuwa sbd baisan Mai zaiyi Mata ba duk da shima yanajin zazza6in sosai Amma ganinta cikin wannan yanayin yasashi daurewa tareda mamakin kansa yanda yanajin zazza6in nacin jikinsa Amma ya share shida a gida ko 'dan yatsansa ke ciwo kwantawa yake su mum suhau jinyarsa ana tarairaysrsa.

Sannu ahankali saiga zazza6in yafara sauka tafara tsatsafo zufa ahankali duk da tuni bacci yayi gaba da ita.

Kallon face 'dinta yayi yaga yanda ta ha'da zufa ya zura hannu ya'dau remote ya kunna aircon.

Sanyin Aircon 'din yaji na qara rura wutar nasa zazza6in ya gyara kwanciyarsa tareda shigewa cikin bangon gaba 'daya Nan shima bacci ya 'daukesa.

Kiran sallar asubar masallacin hotel 'din ne ya tayardasu Amma ita tafara tashi sbd sabon tashi datake dashi na sallar asuba.

Maqalqale yake da ita yashige cikin jikinta sosai Yana baccinsa cikin kwanciyar hankali...

Face 'dinsa ta kalla duk da ba haske hasken dim light ne kawai Amma tana iya ganin baiwar kyau da Allah yayi masa.,

Lumshe idanu tayi tareda addua cikin ranta,
Ya Allah ka sanyaya rayuwar iyayenmu ka kawo sauqi cikin wannan alamarin.

Qoqarin zame jikinta Take ta tashi saitaga ya bu'de lazy eyes 'dinsa cikin bacci ya kalleta.

Cikin kunnensa dake daf da bakinta murya qasa qasa tace,

It's time for salat.

Wata mummunan fa'duwa gabansa yayi sbd numfashinta da yanda muryarta suka shiga kunnensa sun sakar Masa da wani irin yanayi Kuma Nan take idanuwansa suka nuna ya 'dago yakuma kallonta  sai lokacin ya lurada yanda take tun jiya da dare..

Dogon gashinta daya sauko saman kafa'darta ya kalla kafin ya maida idonsa kan rigarta Mai qaramin hannu data bayyana kafa'dunta da dogayen hannunwanta har zuwa qirjinta daya zaunu ya tsaya daidai acikin rigar.. lumshe idanu yayi tareda 'dauke kansa ya tashi zaune a kasalance yakai hannunsa goshinta ya ta6a yaji ba wani zafi ko alaman zazza6i ya sauko gadon ya fa'da toilet yayo brush da alwala yazo yafice ya nufi masallacin.

Saukowa itama tayi tareda 'dauro alwala tazo tayi sallah.
Har gari ya fara haske bai dawoba tana gama azkar 'dinta zame ta kwanta agun Nan take bacci yakuma 'daukarta.

Qarfe bakwai saura yashigo yaga tana bacci ya shiga toilet ya 'dauko kayansu na jiya tareda 'dagata ahankali ya zame  hijab 'dinta ya miqawa laundry man na hotel 'din dake tsaye bakin qofa kafin ya rufe dakin.

Duqawa yayi ahankali ya dauketa ya 'dora saman gado ya kwantar shima jallabiyarsa ya cire ya haye gadon ya kwanta cikin jikinta.

Bacci sukayi sosai na tsawon lokaci kafin suka tashi..

Wannan karon shiya fara tashi ya qurawa fuskanta Ido musamman bakinta dayake jajir kaman tasa lipstick.

Shafa fuskanta yayi ahankali tareda Kai bakinsa saitin kunnenta cikin wata irin kasala yace,

my love..

Tsikar jikinta ce ta tashi gabaki 'daya lokacin da muryar dayayi amfani da ita tashige ta ta bu'de idanuwanta ahankali ta sauke su Akan face 'dinsa dake daf da Tata har dogayen hancinansu na gugan juna.

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now