taura biyu 19&20

10.1K 669 14
                                    

*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒
          _Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_

              *19&20*

Zafin zuciya da bugawar zuciya ne suka mugun tasowa ya Umar ya rintse idanuwansa Dan Daman tuni ya fara zargin ayi hakan tun kallonda yaga Nik 'din yayi Mata a station lokacin....

Rufewa idanuwansa sukayi ya qarasa gurin zuciyarsa na tafasa bai tsaya komaiba ya 'daga qaqqarfan hannunsa ya shararawa Nik wani gigitaccen Mari saiga jini ya 6alle ta hancinsa...

Saukar wani mugun zafi  taji a zuciyarta tayi saurin rintse ido ta bu'de hawaye suka gangaro Mata ta 'dago a cikin karaya ta kallesa saitaga ko motsi yaqi yi ita ya qurawa lazy eyes 'dinsa dasukai ja sbd azabar Mari ko qyaftawa bayayi...

Fixgota taji anyi da qarfi ta 'dago jajayen you takalli ya Umar 'din ta bu'de baki zatayi magana  a zuciye ya mare bakin da qarfi...
Durqushewa tayi qasa cikin azaba Amma tabbas azabar da zuciyarta ke ciki taci wannan 'dan Marin..

'dagowa tayi idanuwan Nik suka sauka kan 'dan jinin daya fito gefen bakinta sbd Marin yayi saurin zubewa gabanta jikinsa na rawa hawaye na taruwa idonsa murya na rawa yace,

You're hurt ayeeshah....
Ya 'daga hannu ya nufi inda jinin yake.....

Cikin zafi ya Umar ya riqe hannun tareda mur'dewa su ya abbakar kuwa Nan suka rufesa da duka.

Rintse idanuwa tayi hawaye na tsiyaya akaro na farko dataji wata mummunar qiyayyar ya Umar tana shiga tareda Huda duk wasu jijiyoyin dake aiki acikin jinin ajikinta.

Miqewa tayi batareda tajuyoba takalli irin dukan dasuke Masa ta fara tafiya cikin damuwa tabar gurin.

'dakinsu ta nufa direct batareda ta leqa ko inaba ta gaida iyayensu kaman yanda tasaba.

Kodata shiga su husna basa 'dakin suna 6angaren mama sakina Dan can sukafi Zama a irin wannan time 'din..

Zubewa tayi bayan qofa tareda sakin wani irin  kuka ahankali tana dafe zuciyarta datakejin kaman xata tarwatse...

Hayaniyace ta kaure cikin gidan Nan take tani kowa na fitowa sbd hayaniyarsu ya Umar hardai shi da muryarsa tafi tashi cikin 6acin Rai...

Tanajin an ambaci kafiri ta lumshe idanuwa hawayenta na tsananta zuciyarta na da'da karyewa sbd batasan mummunan halinda suka sako Nik acikiba...

Da daddare bayan tayi sallah Bata tashi kan sallayarba anan ta qudundune sbd damuwa da zazza6in datakeji mai tsanani...

Nuratu ce tashigo 'dakin jiki a sanyaye ta zauna kusada ita takalleta murya asanyaye tace,

Anty ayshah su baba malam na Kira..

'dagowa tayi takalli nuratu da jajayen idanuwanta a sanyaye tace,

Sun kashesa ko nuratu?

Girgixa Kai nuratu tayi cikin tausayin 'yar uwarta tace,

Aa,,,,amma dai abun yayi Muni...

Kuka tasaki ahankali zuciyarta naci gabada tsananin zafi..

Anty ayshah da gaske soyayya kuke?

Batareda ta 'dagoba cikin kukan ta girgixa Kai...
Kafin ta miqe cikin sanyin jiki ta fito 'dakin ta nufi babban palon baba malam Dan tasan yanxu kowa nacan ya halarta..

Kanta a qasa tashiga tareda rakubewa ta zauna qasa..

So 'daya ta 'dago taga yanda kowa ke Mata kallon 6acin rai,qyama da tuhuma..tayi saurin qasa da kanta Tana danne hawayenta.

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now