taura biyu 15&16

8.1K 660 12
                                    

*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒
          _Mi amor-mi vida...._

_Viawattpad@mamuhgee_

              *15&16*

Kodasu mum suka iso gurin ya Dade da fita haytacinsa Dan dama Yana daurewane gaban ayshah sbd kar abin kunyar yayi Masa yawa anyi Masa duka gabanta Kuma ya ciwo yayi Masa rigis gabanta.

Hankali tashe mum tasa akai asibiti dashi bayan ankira police sun fara bincike agurin Dan ga alamar duka Nan ajikin 'dan nata.

Kodata Isa gida kasa tu6ewa tayi ta shige qarshen gado ta zauna tareda takurewa tana kuka ahankali sbd zazzafan baqon alamarin dataji yana shiga tareda Kama kowace kusurwar jijiyar dake aiki cikin zuciyarta.
Zazza6i ne Mai qarfi itama yakamata Nan take Wanda yasa hankalinsu husna tashi Amma ta hanasu fadawa iyayensu.

Kwananta 'daya da yini tana fama da zazza6i da rashin sukunin zuciya.

Gudun zargi da tambaya yasa tashirya tacigaba da zuwa makaranta.

Koda ya farfado kansa ciwo yake sosai Amma haka ya nunawa mum 'dinsa yaji sauqi dole aka sallamesu duk da mura yake sosai sbd dukan da  ruwa sukai Masa.

Lumshe ido yayi Yana tunano ko awane Hali ayshah take ita data fisa Shan dukan ruwan.

A daddafe yayi kwana biyu agidan mum na jinyarsa a kwana na ukun ya shirya yace yaji sauqi makaranta zashi.

Kallon mamaki mum tayi Masa tace,

Sweetheart you're not fully recovered... you're still weak.,,I can see it in your eyes.

Atishawa Mai qarfi yayi tareda saka farin lallausan handkerchief ya tare hancinsa kafin ya 'dago ya kalleta da lazy eyes dinsa yace,

Mum I'm fine.,,I promise.

Cikin kulawa da yar damuwa tace,

Ok my sweet boy,,but please take care..

Yes mum,,,,yace tareda 'daukar wayarsa da key 'din sabuwar motarsa ya sauko ya fice batareda ya tsaya bawa Davina amsar Murphy datake tambayarsa ba Dan shima nemansa yake Amma haryanzu wayarsa Bata zuwa.

Duk inda yake sakaran zai ganta ya Duba bai gantaba Nan take yaji jikinsa yafarayin sanyi..

Tunda yafara nemanta tagansa tayi saurin 6oyewa bayan wata mota tana kallonsa zuciyarta a sanyaye Amma hakanan taji dadin ganinsa yaji sauqi duk da dai tana iya ganin baida wani kuzari.

Tundaga ranar tafara 6oye Masa duk da baqaramin tirsasa zuciyarta takeba gurin aikata hakan.

Tun mum 'dinsa na 'daukar abin wasa saigata hankalinta yayi mugun tashi sbd wata irin damuwa da muguwar Rama data sako Nik 'din agaba sbd rashin ganin ayshar gashi yakasa samun ko wane information akanta.

Sam shida kansa baisan son da yake Mata yakai hakaba Sai yanzu..

Iya bincike da lallashi mum tayi Masa yafa'da Mata damuwarsa Amma yaqi.

Yau tun 6 na safe yatafi makarantar kosu mum basusan da fitarsaba..

Bakin bus stop ya Parker motarsa zuciyarsa sanyaya da damuwar dayake ciki game da ita Dan yau jiyake kozai kwana ya yini agurin saiya ganta zai iya samun sukunin masifar da zuciyarsa take ciki.

Ahankali bacci ya 'daukesa sbd rashin baccin dayake fama dashi na kwanakin.

A kunne yabar motar sbd Ac.

Sai 10 ta iso makarantar ana ajesu busstop ta fito ta nufi hanyarta cikin sanyin jiki sbd rashin kuzarin da itama take fama dashi.

Kamar daga sama ta hangosa kwance Yana bacci cikin motar yayi matuqar ramewa saitaji zuciyarta na neman karyewa tayi saurin juyawa tabar gurin.

Qarfe biyar na yamma ta gama lectures ta fito a galabaice sbd ranar azumi take..

Cak ta tsaya sakamakon ganin har lokacin Yana gurin saidai wannan time 'din yafito jingine yake jikin motarsa yayi wani irin fadawa sbd yunwa da wahala Amma yaqi tafiya.

Kamar ance ya juyo Sai kawai idonsa yashiga cikin nata yayi saurin miqewa tsaye daidai Yana kallonta amarairaice.

Dakewa tayi ta matso tareda ra6asa ta wuce tashige bus tareda sunkuyar da kanta Dan karma su hada ido.

Binta yayi da lazy eyes 'dinsa suna taruwa da ruwa sbd tunanin qila wani laifi yayi Mata.

Matsowa yayi da sauri zai shiga bus 'din cikin  tsautsayi yaron direban motar ya turesa sbd already motan yacika ya fa'di qasa cikin ruwan saman dake taruwa awurin Nan take kayansa da jikinsa ya lalace bai tsaya dubawaba ya miqe da sauri zaikuma matsowa aka tada motar sukabar gurin.

Motarsa yashiga da sauri yabi bayansu saigasu har anguwar su ayshah 'din.

Tana fitowa motar tagansa Yana qoqarin parking ya fito.

Saurin wucewa tayi batareda takuma kallon inda yakeba.

Biyota yayi da gudu batareda ya tsaya kashe motarsa ba..,,

Sauri ta qara gabanta na tsananta fa'duwa daf da zata shiga kwanar layinsu saiga ya Umar...

Wata mummunar fa'duwa gabanta yayi ta saci kallon bayanta taga Sai zubo sauri yake Dan ya iso wurinta ta rintse ido zuciyarta na tsinkewa da tausayinsa.

Kallonta ya Umar 'din yayi Yana son karanto firgicin daya gani tattare da ita.

Kamar ance ya Duba bayanta saiya hangosa Yana zubo sauri tareda tsalle Yana qoqarin fa'duwa sbd agwagi dasuka biyosa Sai tsalle yakeye Yana kallota karta 6ace Masa.

Kallonta Umar 'din yayi cikeda zargi kafin yayi Mata alamar ta wuce da ido.

Sum sum ta wuce Amma saita kasa shigewa konar ta juyo.

Manyan agwagin dasuka fi girma Umar ya 'dauka tareda jefa Masa cikin baqin ciki da takaicin ganinsa.

Baya yayi da sauri cikin tsoron agwagin cikin rashin sa'a Ashe yakai kwata sai gashi zaune cikinta.

Batareda 6ata lokaci ba ya yunquro yataso har lokacin idonsa nakan kwanar datake la6e tana kallonsa.

Qoqarin wucewa yake cikin takaici Umar ya fixgosa tareda wurgar dashi ya nunasa da yatsa cikin xafi yace,,

Zanbarka yau katafi Amma wlh duk nakuma ganin wannan kafirar fuskar taka cikin anguwar Nan saina yanka maka ita da kwalba..

Juyawa yayi zai wuce tayi saurin barin gurin tayi gida da sauri zuciyarta na wani irin nauyi.




Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comments_

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now