taura biyu 31

8.5K 687 54
                                    

*_MAMUH GEEE_*


_*TAURA BIYU....*_🍒
          _Mi amor-mi vida...._
 

_Viawattpad@mamuhgee_


                   *31*
 

Tunda tazo gidan kwananta biyu Bata Kuma sakashi a Ido Bata damu ba Dan dama bashine a gabanta ba hasalima iskancinta ta tsulawa a gidan son ranta sbd ganin take taken siyama data 'dauki tsana da kishi ta saka Mata,,
Abu 'daya ke damunta shine yanda tun ranar data dawo gidan ya 'dauke 'danta yamaida gurin mum sbd wai karyaga munanan 'dabi'unta,,,,

Khadija ce kawai abokiyar firarta wani lokacin musamman yanda suke cikin tsananin kewar kayan mayensu hardai ita ayshah Dan jitake kamar ta zare sbd rashinsu shiyasa kowa ya ta6ata a gidan Bata raga Masa sbd takaicin rashin kayan caza kwakwalwa,..

Tunda ayshah tadawo gidan siyama take cikin baqin ciki da takaici tayi mitar harta gaji Amma Yama qi sauraronta sbd idan har ayshah tabar gidan to gurin iyayenta zai maidata Amma ba yanxu ba saita dawo cikakkiyar nutsuwarta sbd yasan suka ganta ahaka zuciyarsu bazatayi dadiba,,,,

Kwance take cikin tsararen palonta ta qurawa tv Ido Amma ba kallon takeba tunani take ta yanda zata samu ganin shanty Dan tayi kewarta da Kuma kayan korawa.,

Gajeran wando ne black ajikinta da vest itama black da 'dan adon white ajiki.,

Qofar palon taji anbude anshigo da qarfi tareda jeho Mata Kaya akai.

'dagowa tayi taga siyama tsaye Rai a6ace kamar zata fashe tace,

Ga kayanki Nan idan bazaki iya wankewa da kankiba to saiki hkr Amma Mai Mana aiki bazata wanke wa'innan kayanba masu najasar giya da wama yasaniba ko harda najasar....

Wawan Mari ayshah tasakar Bata batareda tayi tsammaniba takuma tureta tareda fitowa daga palon ta qwala Kiran Mai aikin dakeda suna Fatima.

Da sauri fatimar ta iso jikinta na rawa ayshah ta kalleta fuska a 'daure tace,

Wuce maza ki kwaso kayan Nan ki aje duk aikin dakike Kona waye ki wankemin su now..

Fitowa siyama tayi cikin zafin Rai da zafin Marin datasha ta kalli fatima ta daka Mata tsawa tuni jikin yarinyar ya'dau rawa sbd ganin tana tsaka...

Kallon siyama ayshah tayi cikin takaici kafin ta juyo takalli Fatima Sai kawai takama hannun fatimar tajata zuwa part 'din Deen.

Da sauri siyama tabi bayansu tana Kiran sunan fatimar a fusace,

Zaune yake a palon Yana waya sanye yakeda qananan Kaya sai wani qyallin kyau fatarsa take Sai ganinta yayi gabansa ba zato,.

Kayan dake jikinta yafara kallo tunda sama har qasa ya dan tsuke fuska sbd fa'duwar da gabansa yayi,,,

Maida kallonsa kan siyama dake cika tana batsewa yayi hankali kwance yace,

Ya akayi ne?

Cikin 'dage gira ayshah tace,

Nizaka kalla Dan nice zanyi magana,

Kan tv ya maida fuskarsa Yana cewa,

Then speak.

Cikin takaici tace,

Wannan me aikin waye yake biyanta agidan Nan?

Kallonta yayi cikin mamaki da takaici yace,

Idan baniba kece kike biyanta?

Just answer the question bance ka fadamin maganaba.

Yana kuma maida kallonsa ga tv yace,

TAURA BIYU✅Where stories live. Discover now