taura biyu 35

10.2K 632 8
                                    

*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
          _Mi amor-mi vida...._
 

_Viawattpad@mamuhgee_

                    *35*

Nurse ce tashigo ta tsaya tareda kallon mum cikin yanayi na damuwa tace,

Ma'am doctor wants to see you in his office.

Fa'duwa gaban mum yayi takalli Deen da idanuwansa da fuskarsa tuni sukayi jajir sakancewarsa fari sbd kuka jijiyoyin kansama tuni suka firfito shika'dai yasan mummnan halinda zuciyarsa take ciki.

Danne damuwarsa yayi tareda miqewa tsaye riqeda hannun mum 'din suka nufi office and Dr ko kallon gefen siyama baiyiba Dan baimasan da wanxuwarta a 'dakinba.

Kallo 'daya Dr yayi musu yasan suna cikin tsananin damuwa Amma Dole ya sanar dasu halinda 'yarsu take ciki.

Shaikh ya jikin naka Kai?

'daga Masa Kai yayi Yana lumshe idanu sbd bayajin zai iya magana.

Well gskia a irin yanayin da Khadija ta farfado dashi yabamu tsoro da mamaki Amma bamu tabbatarda abinda muke zargiba Saida mukayi iya binciken mu....

Tsakanin buguwa ko duka days shiga sosai cikin kanta yayi sanadin ta6uwar qwaqwalwanta,,,,, ataqaice dai tasamu ta6in qwaqwalwa..

Kuka qarfi mum tasaki Deen yayi saurin rungumeta Yana Kiran innalillahi......

Duk wani kukan Dana sanin shuka mugun Abu yau mum tayishi sbd ganin mummunan halinda 'yayanta suka shiga,,
Finn ya mutu,
Deen baya cikin kwanciyar hankali,
Ga Khadija ta samu tabin Kai..

Kuka tayishi iyakar yinta harya daina fita saidai tunani.

Gida aka sallamosu suka dawo mum na riqeda khadijar daketa faman kalle kalle tana Sosa Kai tana ketar dariya.

Shikuwa ko magana baya iyayi suna dawowao ko Zama baiyiba ya kalli mum jiki amace yace,

Mum Zanje gurin ayshah.

Hawayen tausayinsa Dana kanta ne suka gangaro Mata ta miqe tareda shigewa bedroom ta hado kayanta Dana khadijar a akwati biyu tace,

Itama zata koma gomben sbd bazata iya Zama ananba tafison gidansu na can where it all started.

Bai hanataba ya fito kamar zai wuce saiya tsaya zuciyarsa na nauyi da qunci ya nufi part 'din siyama daidai lokacinda take waya da qawarta tana fa'da Mata abinda ta aikata..

Yaji abinda duk tafada saiya aje Mata kudi tareda ficewa batareda ta gansaba.

Airport driver yakaisu mintuna qalilan aka Kira jirginsu suka tashi Sai gombe.


**********

Tunda suka shigo garin gombe jikinta yayi mummunan sanyi tayi zuru rayuwarta tada na dawo Mata musamman dasuka kawo daidai makarantarsu Nan komai yadawo Mata tasaki kuka ahankali zuciyarta na qara karyewa.

Shiru muh'd yayi kukanta na ta6a zuciyarsa Dan shima ganin makarantar ya dawo Masa dakomai na lokacin suna cikin Jin da'di da duhu na kafirci.

Yana parking bakin kwanar layin gidansu zuciyarta ta tsinke akaro na farko rabonta da gida da tsananin tsoro yashigeta.

Kallonta yayi tareda 'daga Mata Kai murya a sarqe yace,

You can do this,, Allah na tareda ke.

Share hawaye tayi jikinta na rawa sbd tsoro cikin sanyi tace,

Thank you murph....

Katseta yayi da cewa,

Muh'd.

TAURA BIYU✅Donde viven las historias. Descúbrelo ahora