taura biyu 29

8.8K 628 44
                                    

*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU....*_🍒
          _Mi amor-mi vida...._
 

_Viawattpad@mamuhgee_

                   *29*
 

  Arikice shanty takamota tana girgixata da qarfi cikin tashin hankali Amma ba alamar ko numfashi atareda ita bare tasakaran zata motsa.,,

Kallon Nana dake risgar kuka cikin tashin hankali tayi tace,

Kamomin ita maza,
Mota suka sakata cikin mota aguje ta Isa specialist da ita kafin takira anty fannah tafa'da Mata abinda ke faruwa.

Sumane kawai anty fannah batayiba Jin mummunan zancen cikin qoqarin danne kukanta tace gatanan qarasowa asibitin,
Tana kashe wayar tasaki kuka ahankali jikinta na matuqar rawa Dan tasan rashin ganin Mahmud barazanace ga kwanciyar hankali da dadda'dar rayuwarsu musamman ayshah datasan zaucewama zatayi.

Kodata isa asibitin ayshahn ta farko Banda hauka Babu abinda take musu Sai ririqeta akeyi tana ganin anty fannah tasaki wani irin kuka Mai qarfi tareda fadawa jikinta tana cewa,

Anty fannah Mahmud 'dina,,,,I can't live without my son,,,,, Mahmud is my life,,,my Mahmud.....

Kukane yaci qarfinta ta rintse idanuwa tana rerosa da qarfi..

Anty fannah da shanty ma duk kukan suke Nana kuwa ita ko magana ba'ayi.

Police sukaje suka bada report tareda zube maqudan ku'di Nan da Nan suka 'dau bayanai suka fara nemansa cikin gaggawa.

Gida suka koma Amma ayshah ko Zama kasayi tayi ta zari mukullin mota ta Fice da sauri suka bita Nan suka fara yawo cikin gari lungu da saqo suna nemansa ganin dare yafarayi ba alamar ganinsa yasa ayshah qara rikicewa Banda kukan tashin hankali Babu abinda takeyi,,

Daqyar suka samu suka tirsasata suka dawo gida  cikin dare..

Washe gari ma hakance takuma faruwa tun safe suna yawo Amma ba alamar nasara suna dawowa gida wani mugun zazza6i ya rufeta sbd kuka da rashin cin abinci danko ruwa su anty sunyi sunyi Amma Sam ko kallon abinci tason yi Banda kuka ba abinda take iyayi.

Police sunyi iya yinsu har tsawon sati biyu ba wani bayani Sai kawai suka aje case 'din gefe,,,

Duk inda hankalin anty fannah da shanty yake ya matuqar tashi sbd halinda ayshah ke ciki Dan kuwa sosai ciwo ya kwantar da ita tayi wata irin muguwar Rama ta yamutse ta Fice hayyacinta sbd komaima sabo yadawo Mata ciwon rabuwa da iyayenta Dana 6atan 'danta da yanda rayuwarta ta ta6ar6are duk komai ya taru ya zautata.

Anty fannah ma tuni kwanciyar hankali yayi Mata qaura duk ta rame sbd ganin yanda ayshan takoma kamar Wadda tayi shekaru cikin ciwo,,

Sunyi yawon asibitota harsun gaji Amma Babu wani sauqi..

Wata biyu da 6atan mahmud ciwo ya kwantar da ayshah suka kwanta asibiti jinya..

Zaune take bakin gadon 'dakin datake cikin mummunan yanayi Dan ko gani sosai batayi yanzu sbd kuka dayafara cinye Mata lafiyar Ido.

Daqyar shanty dake zaune ta lalla6ata takamota suka fito wajen 'dakin kota 'dan sake maimakon ciki Banda ajiyar zuciyan kuka ba abinda take Dan yanxuma kukan bai zuwa saidai na zuci dayafi ciwo.

Wata kyakkyawar lady ce ta nufo aminity word 'din cikin shiga ta alfarma ta dogon hijab maroon har qasa daya matuqar qayata kalar fatarta hannuwanta sunci adon Jan lalle hakama qafafuwanta wasu matsiyatan heels ne duk da hijab ne ajikinta,

Murmushi fuskarta ke bayyanawa har haqoranta na 'dan bayyana ta qaraso gurin wasu Mata dake zaune kan qatuwar dadduma suna fira daganinsu kasan gidan masu tsananin arxiki suka fito.
 
Cikin farin ciki suka tarbeta tareda 'yan rakiyanta guda biyu dake bayanta,
Kujera aka 'dauko Mata da sauri aka aje Mata ta zauna cikin sakewar fuska takalli dattijuwar ciki tace,

TAURA BIYU✅Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon